Al-Makura ya kaddamar da sababbin motocin kashe gobara
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya nanata kudirin gwamnatinsa na kare rayukan al’ummar jihar ta hanyar gudanar da ayyuka da za su ciyar da jihar gaba. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da wasu sababbin motocin kashe gobara biyar da na kwasar shara biyu da wasu kayayyakin aikinsu a harabar […]

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya nanata kudirin gwamnatinsa na kare rayukan al’ummar jihar ta hanyar gudanar da ayyuka da za su ciyar da jihar gaba. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da wasu sababbin motocin kashe gobara biyar da na kwasar shara biyu da wasu kayayyakin aikinsu a harabar Ma’aikatar Ayyuka da ke Lafiya a ranar Litinin da ta gabata.
Gwamnan ya ce sayon motocin na daga cikin kokarin gwamnatinsa na biyan bukatun al’umma da kuma kyakkyawar fatar da suke mata.
Ya kara da cewa “Gwamnatina ta sayo wadannan motoci ne tda wasu kayayyakin aiki domin taimakawa musamman a lokaci da ake bukatar su cikin gaggawa. Kuma za a aje mutocin da kayayyakin ne a muhimman wurare inda za a yi amfani da su domin samar da ayyuka yadda ya kamata.”
Sai ya bukaci jami’an hukumar su tabbatar sun yi amfani da motocin kashe gobarar da sauran kayayyakin aikin yadda ya kamata.
Gwamnan ya kuma bayyaana shirin gwamnatinsa na samar da kananan asibitoci a duk kananan hukumomi da yankunan raya kasa na jihar.
Dangane da motocin kwasan shara kuwa, Gwamnan ya ce an yi haka ne domin cimma kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsabtace muhalli a jihar baki daya.
Tun farko da yake jawabi, Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Mista Philips Audu ya jinjina wa Gwamnan ne kan wannan karamci inda ya ce babu shakka samar da motocin kashe gobarar zai rage asarar da al’ummar jihar ke yi. Ya yi kira ga jami’an hukumar su yi amfani da motocin da sauran kayayyakin aikin yadda ya kamata don a dade ana cin moriyarsu.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta cika alkawarin da ta yi na biya wa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar kudin alawus dinsu don karfafa su wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Alhaji dalhatu Dogara ya nuna farin cikinsa dangane da karamcin inda ya bukaci jami’an hukumar su yi amfani da motocin yadda ya dace don tallafawa wa kokarin gwamnati na inganta harkokin hukumar.