Al-Makura ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Suswan
Gwamnonin jihohin Nasarawa da Binuwai sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tsoma don kawo karshen rigingimu da suka ki ci suka ki cinyewa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma Tibi a iyakokin jihohin biyu. Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ne ya yi wannan kira a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Gabriel Suswan da […]
Gwamnonin jihohin Nasarawa da Binuwai sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tsoma don kawo karshen rigingimu da suka ki ci suka ki cinyewa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma Tibi a iyakokin jihohin biyu.
Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ne ya yi wannan kira a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Gabriel Suswan da al’ummar Jihar Binuwai a gidan gwamnati da ke Makurdi a karshen makon jiya dangane da hari da wasu ’yan bindiga suka kai ga Gwamna Suswan a wani kauye da ake kira Ste.akenye da ke iyakar jihohin biyu, lokacin da ya kai ziyara ga ’yan gudun hijira.
Gwamna Al-Makura ya roki Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa jihohin biyu wajen warware matsalar da ke ci gaba da ci musu tuwo a kwarya inda ya ce lamarin ya dauki sabon salo saboda hare-haren sun shafi yawancin jihohin Arewa a yanzu.
Gwamnan ya ce ya yi matukar girgiza da ya samu labarin an kai wa ayarin Gwamna Suswan hari inda ya ce al’ummar Jihar Nasarawa sun yi tofin Allah tsine ga aukuwar lamarin.
Ya yaba wa kokarin Gwamna Suswan wajen samar da dauwamammen zaman lafiya a iyakokin jihohin biyu, inda ya bukace shi da al’ummar Binuwai su kara hakuri saboda Jihar Nasarawa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba da tata gudunmawa don inganta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin jihohin biyu.
Gwamna Suswan ya gode wa Gwamna Al-Makura da tawagarsa dangane da ziyarar jajen da suka kai masa, ya bayyana rigirgimun da suke aukuwa a tsakanin al’ummar Tibi da Fulani makiyaya da harin da aka kai masa a matsayin babban kalubale da jihohin biyu ke fuskanta a halin yanzu, kuma ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen rigirgimun.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu ’yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai wa Gwamna Suswan hari a hanyarsa ta zuwa kauyen Ste.akenye da ke iyakar Binuwai da Nasarawa don ziyartar ’yan gudun hijira.