Al-Makura ya mikawa sabon Gwamna makullan gidan gwamnati

Gwamnan jihar Nasarawa mai barin gado, Umaru Tanko Al-Makura ya mikawa zababben Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule, makullan gidan gwamnati jihar bayan wani biki da ma’aikatan gwamnatin jihar suka shirya. Gwamna Al-Makura, ya ce ya tattauna da sabon Gwamnan jihar mai jiran gado Injiniya Abdullahi game da ayyukan da gwamnati mai barin gado ta kaddamar […]

Al-Makura ya mikawa sabon Gwamna makullan gidan gwamnati

Gwamnan jihar Nasarawa mai barin gado, Umaru Tanko Al-Makura ya mikawa zababben Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule, makullan gidan gwamnati jihar bayan wani biki da ma’aikatan gwamnatin jihar suka shirya.

Gwamna Al-Makura, ya ce ya tattauna da sabon Gwamnan jihar mai jiran gado Injiniya Abdullahi game da ayyukan da gwamnati mai barin gado ta kaddamar a jihar na awanni duk a yau.