Al-Makura ya nada yaro Gwamnan yini daya
Wani karamin yaro kuma Shugaban Majalisar Yara ta Jihar Nasarawa Richard Aga ya rika mukamin Gwamnan Jihar na yini daya a shekaranjiya Laraba, bayan da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya nada shi ya jagoranci mulkin jihar na yini.Aga, wanda ya jagoranci Gwamna Al-Makura zuwa Unguwar Jaba da ke Lafiyya, don cin abinci da kutare da […]
Wani karamin yaro kuma Shugaban Majalisar Yara ta Jihar Nasarawa Richard Aga ya rika mukamin Gwamnan Jihar na yini daya a shekaranjiya Laraba, bayan da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya nada shi ya jagoranci mulkin jihar na yini.
Aga, wanda ya jagoranci Gwamna Al-Makura zuwa Unguwar Jaba da ke Lafiyya, don cin abinci da kutare da makafi da kurami da sauran nakasassu ya amshi ragamar Gwamnan Jihar ne da misalin karfe 10:30 na safe a dakin taro na Gidan Gwamnati, inda daukacin wakilan Majalisar Zartarwar Jihar ciki har da Mataimakin Gwamna Dameshi Barau Luka da Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Hajiya Zainab Abdulmumun da dukkan kwamishinoni da mashawarta suka hallara.
Al-Makura ya sanar da wakilan majalisarsa cewa ya gayyaci Aga zuwa Gidan Gwamnatin ya dana kujerar Gwamna ta yini domin ya taimaka wajen wa’azin zaman lafiya ga al’ummar jihar. Al-Makura ya ce ya yi haka ne don karfafa gwiwar jama’ar jihar su fahimci akwa alheri a gaba, amma hakan zai samu a yanayi na zaman lafiya da yarda da juna.
Yaro Aga yana hawa kujerar Gwamna ya yi godiya ga Gwamna kan wannan karramawa sannan ya gabatar da jawabi na musamman kai-tsaye ga al’ummar jihar ta rediyo da talabijin, jawabin mai taken: “Mu rungumi zama da juna lafiyya don kwanciya hankali da ci gaba,” ya nemi al’ummar jihar su yi watsi da duk abin da zai bata kyakkyawan zaman da ke tsakanin sama da kabilu 27 na jihar.