Al-Makura ya sa hannu kan kasafin Jihar Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya sanya hannu a kan kasafin kudin jiha na bana wanda ya kai sama da Naira biliyan 114. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Musa Ahmed Muhammed ne ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar a Lafiya. Ya ce bayan kammala zamansu na makon jiya ne mai taimaka wa Gwamnan […]

Al-Makura ya sa hannu kan kasafin Jihar Nasarawa
Al-Makura ya sa hannu kan kasafin Jihar Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya sanya hannu a kan kasafin kudin jiha na bana wanda ya kai sama da Naira biliyan 114.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Musa Ahmed Muhammed ne ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar a Lafiya. Ya ce bayan kammala zamansu na makon jiya ne mai taimaka wa Gwamnan a kan al’amuran majalisa Musa Omaki ya sanar da shi cewa Gwamnan ya rattaba hannu a kan kasafin kudin tun a ranar 28 ga watan jiya. Shugaban majalisar ya kara da cewa kudirin dokar hadin gwiwa na gwamnati da bangarori masu zaman kansu da ke gaban Gwamnan ne ya rattaba wa hannu. Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnan ya yi duk mai yuwa don ganin ya rattaba wa sauran kudirori da majalisar ta shigar kwanakin baya in ba haka ba a cewarsa majalisar za ta yi amfani da tanade-tanaden doka da suka wajaba don ganin cewa dokokin sun fara aiki a jihar. A nasu jawaban dan majalisa daga mazabar Keana Francis Orogo da takwaransa na Akwanga ta Kudu, Gyunka Philips sun yaba wa Gwamnan ne dangane da rattaba hannu a kan kasafin na bana, inda suka yi kira a bi dokar kasafin yadda ya dace. Sun kuma yi kira ga takwarorinsu su sanya ido sosai wajen tabbatar an aiwatar da kasafin ta hanyar kara kaimi wajen kai ziyarar gani da ido. Daga cikin kasafin an ware Naira biliyan 55 da miliyan 193 da dubu 556 da 74 don gudanar da manyan ayyuka, inda ayukan yau da kullum za su lakume Naira biliyan 57 da miliyan 882 da dubu 835 da 894.