Al-Makura ya sallami kwamishinoninsa 8

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya sallami kwamishinoni takwas daga majalisar zartarwar jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Hajiya Zainab Abdulmumin ta rattaba wa hannu da aka raba wa manema labarai a Lafiya a karshen makon jiya.Sanarwar ta ce kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da Barista […]

Al-Makura ya sallami kwamishinoninsa 8
Al-Makura ya sallami kwamishinoninsa 8

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya sallami kwamishinoni takwas daga majalisar zartarwar jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Hajiya Zainab Abdulmumin ta rattaba wa hannu da aka raba wa manema labarai a Lafiya a karshen makon jiya.
Sanarwar ta ce kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da Barista Enocent Lagi da Mista Angama Waibe da alhaji Sani Yakubun Hauwa da danladi Madaki da Alhaji Adamu Mu’azu Adogi da Mista Godwin Embatse da Mista Samuel Meshi da kuma Mista Amos Bala Akawu. Har ila yau Gwamnan ya sauke wasu masu mukamai daban-daban daga kujerunsu da suka hada da Babban Sakataren Hukumar Bada Tallafin Karatu na Jihar Alhaji Suleiman Abdul Wahab da Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Alhaji Idris Abdullahi da Babban Daraktan Kamfanin Zuba-Jari da Kadarori na Jihar Mista Daniel Ajigena da mai taimaka wa Gwamnan a kan tallafa wa matasa, Murtala Adogi Muhammed da Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan Alhaji Iliyasu Ali Yakubu.
Sanarwar ta bukaci tsofaffin kwamishinonin su mika ragamar al’amuran ma’aikatu ko hukumominsu ga manyan sakatarorinsu daga yanzu zuwa mako mai zuwa, inda Gwamnan ya gode musu dangane da gudunmawar da suka bayar don ci gaban jihar, kuma ya yi musu fatar alheri a al’amuransu na gaba.