Al-Makura ya shawarci ’yan takarar Shugaban kasa a APC su fahimci juna
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci ’yan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC su tabbatar sun fahimci juna don samun nasarar jam’iyyar a zaben badi. Gwamna Al-Makura ya yi wannan kira ne a lokacin da yake karbar tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya kai ziyara jihar a gidan gwamnati […]
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci ’yan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC su tabbatar sun fahimci juna don samun nasarar jam’iyyar a zaben badi.
Gwamna Al-Makura ya yi wannan kira ne a lokacin da yake karbar tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya kai ziyara jihar a gidan gwamnati da ke Lafiya.
Ya yi kira ga dukkan masu neman takarar kujerar Shugaban kasar nan a karkashin Jam’iyyar APC kan su kasance masu tuttubar juna domin fitar da dan takara daya da zai tsaya takara.
Gwamnan Al-Makura ya yaba da tsayin-daka da jajircewa da Atiku Abubakar yake yi tare da gudanar da al’amuran siyasa yadda ya kamata ba tare da nuna bambanci ba.
Kuma ya gode wa tsohon Mataimakin Shugaban kasar kan ziyarar da ya kai jihar inda ya ce babu shakka Atiku Abubakar abin alfahari ne a Jam’iyyar APC.
Tun farko a jawabin Atiku Abubakar ya ce ya ziyarci jihar ne musamman Gwamna Umaru Al-Makura don ya yaba masa dangane da nasarar da yake samu wajen shawo kan matsalolin da jihar ke fuskanta musamman na rikicin kabilanci. Ya ce a cikin shekara uku da rabi da Gwamnan ya yi a matsayin Gwamnan Jihar ya shawo kan matsalolin jihar da dama.
Ya ce ya je jihar ne don ya gana da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC musamman a kan yadda jam’iyyar za ta samu nasara a zabubbuka masu zuwa.
Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar jihar dangnane da kyakkyawar tarba da suka yi masa, inda ya yaba kyawawan halaye da gudanar da shugabanci mai inganci da Gwamnan ke yi a jihar, ya ce irin wadannan kyawawan halaye ne suka jawo hankalinsa ya shiga jam’iyyar.
Atiku ya ce “Idan aka yi la’akari da dimbin nasarorin da Jam’iyyar APC ta samu a kasar nan musamman a Jihar Nasarawa dole ne mutane irinmu su shigo jam’iyyar.”