Al-Mustapha: Ciki da gaskiya wuka ba ta huda da shi (2)
A yau muna cikin farin ciki da jin dadi da godiya ga Ubangijinmu da ya nuna mana Manjo Hamza Al-Mustapha ya fito daga gidan yari sama da shekara 14 da wata tara da kwana 13 dayayi a tsare ba tare da an yanke masa hukuncin gaskiya ba. A baya an tuhume shi da laifukkan da […]
A yau muna cikin farin ciki da jin dadi da godiya ga Ubangijinmu da ya nuna mana Manjo Hamza Al-Mustapha ya fito daga gidan yari sama da shekara 14 da wata tara da kwana 13 dayayi a tsare ba tare da an yanke masa hukuncin gaskiya ba. A baya an tuhume shi da laifukkan da ke da nasaba da shirya juyin mulki har sau biyar, da tuhumarsa da shigowa da bama-bamai daga kasashen waje da kisan Kudrata Abiola, wanda shi ne sanadiyar yankemasa hukuncin kissa, da ire-iren sauran sharrin da aka yi masa.
Sai dai cikin ikon rabbul-arshi sai ga shi Allah ya fitar da shi ba tare da laifi ko daya ba. Sanadiyar addu’o’in jama’a na tabbatar da gaskiya, akan al’amurra. Kamar yadda mai shari’a Rita Pemu ta fada a lokacin da take yanke hukuncin. inda ta dauki tsawon mintuna 88 tana karanta hujjoji na dalilin da yasa kotun daukaka kara ta sake shi, tare da Lateef Shofolahan, inda ta yi nuni da cewa karamar kotu ta nuna halin ko’in-kula na rashin bayyanar shaidu agabanta. “Hukuncin kisa ba wasa ba ne, dole ne alkali ko kotu ta tattara hujjoji masu nasaba da laifin wanda ake zargi da aikatawa, sabanin abin da karamar kotu ta yi,” injita.
Mai shari’a Pemu ta bayyana cewa bisa hujjojin da ke gabanta hukuncin da karamar kotu ta bayar ba shi da tasiri, ba shi da kkarfi balle madogara, don haka wannan kotu ba kowa take yi wa aiki ba, illa .yan Najeriya kuma idan gaskiya ta fito karya dole ta kauce.
Wannan abin godiya ne ga Ubangijinmu idan muka duba za mu ga sama da shekaru goma sha 14 wannan bawan Allah yana tsare, domin cin zarafi da zalunci aka kirkiri laifukkan karya aka aza masa duk wasu hujjoji da ya kawo tare da lauyansa. An yi banza da su, amma cikin ikon Allah sai ga shi lokacin fitowarsa ya yi da an ki da anso tun da Allah ya ce sai ya fito ranar ba wanda zai hana. Kamar yadda gidajen radio da ’yan jarida suka yi hira dashi major Hamza Almustapha yayi godiya ga Allah ubangiji da yanunamasa wannan ranar da kotun daukaka kara ta bayyanawa jama’a gaskiyar lamarin inda yace an shirya muna mugunta amma munyi tawakkali ga Allah.
Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa irin darasin da ya koya ya wuce karfin tunani. Domin ya fahimci shari’ar Najeriya, ya fahimci ’yancin dan Adam, sannanya fahimci irin yadda wasu ke amfani da doka domin tursasa wa talaka, da hukurin talakan Najeriya, da addini ba wasa ba.
Tabbas Allah ya saka maka da mafificin alherinsa, ya sa aljanna ce makomarka da mu buki daya. Jama’a ya kamata mu dauki darasi. Sharri (alhaki kwikuyo ne) kare ne mai shi yake biya.
A Ranar lahadi 14/07/13 Manjo Hamza Al-Mustapha ya baro filin jirgin saman Janar Murtala Ramat Muhammad da ke Legas zuwa Birnin Kano, inda ya sauka a filin ajirgin saman Aminu Kano da ke Kano, inda milliyoyin magoya bayansa da masoyan arziki da musu yi masa fatan alheri suka tarbe shi.
Lallai Hausawa sun yi gaskiya inda suke cewa ‘Ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi.”
Allah yasaka ma kowa da alherinsa amin. Alhamdulillah. dukkan godiya ta tabbata ga Allah mMadaukakin sarki mai kowa da komi me kashewa da rayawa.
M.A. Faruk Sakkwato
07014414414