Al-Mustapha: Ta Allah ba tasu ba
A duniya komai ya yi farko zai yi karshe ban da ikon Allah. Shi ya sa gwanayen magana ke cewa kowane al’amari da lokacinsa. A makon jiya ne wa’adin zaman gidan jarun da Jalla Ya hukunta kan bawanSa, Hamza Al-Mustapha ya kawo karshe, bayan shekaru 14. Tun daga ranar aka kame shi a shekarar 1999, […]
A duniya komai ya yi farko zai yi karshe ban da ikon Allah. Shi ya sa gwanayen magana ke cewa kowane al’amari da lokacinsa. A makon jiya ne wa’adin zaman gidan jarun da Jalla Ya hukunta kan bawanSa, Hamza Al-Mustapha ya kawo karshe, bayan shekaru 14. Tun daga ranar aka kame shi a shekarar 1999, bisa zargin kisan uwargidan marigayi Moshood Abiola, ‘yanuwa da abokan arziki suka yi ta fafutikar ganin ya yi galaba a kotu bisa wadanda suka yi masa wannan zargi, amma abin tamkar mai ne suka kara bulbulawa kan wutar da ta gawurta. Rashin samun nasararsu ta tsawaita wahalhalunsa, kuma a sakamakon haka duniya gaba daya ta kosa da haka ganin cewa babu zaluncin da wuce jinkirta adalci, domin kuwa ana iya kwarar wanda bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.
Da yake Allah Mai karbar addu’ar bayinsa ne, musamman wadanda aka zalunta; sai ga shi nan ranar Juma’ar da ta gabata kotun daukaka kara ta warware hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata babbar kotu ta yanke masa, a watan Janairun bara, shekaru goma 13 bayan zarginsa da ake yi da kisan kai. Duk da cewa Al- Mustapha ya daukaka kara game da wannan hukuncin a wancan lokacin, jama’a da yawa sun tunzura, suka kuma dukufa yi masa addu’o’i don samun sa’ida da mafita daga abin da suka kira kutungwila da kinibibin makiyansa, wadanda suka dage lallai sai sun ga bayansa.
Sakin Al-Mustapha ya faranta ran miliyoyin masu sha’awar ganin ana kamanta gaskiya, ana kuma shimfida adalci a harkokin gudanar da mulkin kasar nan; nan take kuma suka shiga shagulgullan taya shi murna a dukkan manyan birane da kauyukan tarayyar Najeriya. Bayan kwanaki biyu da yin haka sai ya karasa birnin Kano don saduwa da iyalansa, inda dubun-dubatan masoyansa suka yi cincirindo, saffan-saffa, a filin jirgin saman Kano don yi masa marhababiya, irin wacce ake yi wa kowane shugaban al’umma mai tsananin farin jini da muhibban jama’a. Irin wannan karimcin ne ya dace da mutumin da ya sayar da ransa don kare mutuncin ubangidansa, Janar Sani Abacha, da kuma kwanzarta martabar kasarsa, wanda Yahudu da Nasara suka tozarta, suka kuma ci gaba da wulakantawa har bayan mutuwarsa. Wannan na daga cikin irin karimcin da aka san al’ummomin Arewacin kasar nan da shi, sun kuma kyauta ainun da suka yi haka, sun kuma nuna wa duniya cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne.
To amma a wajen wasu jinsin kasar nan, marasa kaunar zaman lafiya, karrama Al-Mustapha, kamar yadda aka yi a Kano da sauran wasu wurare, bai dace ba, domin kuwa har jaridun irin wadannan mutanen na ganin cewa an bi son zuciya ne wajen sakinsa, kuma wai hakan zai bakanta zukatan zuriyar Alhaja Kudirat Abiola. Wata daga cikin jaridun ma ta fito fili, firi-falo tana tsattsagar Gwamnan Jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso don haba-haban da yake yi da Al-Mustapha, mutumin da ya ce ya zame jan gwarzon da ya wajaba a mutunta. Yaushe ke nan murnar taya dan uwa tsira daga kutungwilar makiya ta zama aibi? A shekarar 1989 daukacin kasashen duniya sun taya jama’ar Afrika ta Kudu murnar fito da Nelson Mandela daga kurkuku, inda ya yi shekaru 27 a garkame, akwai wanda ya hana ko ya ci gaba da yi wa Mandela wani gani-gani saboda an zarge shi da aikata laifi bisa zalunci? Shin al’ummomin Najeriya ba su zuba ruwa a kasa sun sha ba, sa’ilin da gwamnatin Janar Gowon, a 1966, ta sako Cif Obafemi Awolowo daga kurkuku? To sai akan Al-Mustapha ne za a ga wallen masu taya shi murnar samun ‘yanci?
A’aha! Zargi dai ba gaskiya ba ne, sai an bincika, an tabbatar tukuna. Al-Mustapha ya yi shekaru 14 a tsare, an kuma yi binciken kazafin da aka yi masa, a zahiri da badini, an tsuguna gaban alkalai don bin bahasi, kotuna kuma sun yi la’akari da hujjojin da aka gabatar musu, sun saurari dukkan shaidun da suka hallara gabansu, sun yanke hukunci gwargwadon basirarsu, bisa ka’idar aikinsu da kuma tsarin dokar kasa. To ba shi ke nan sai magana ta kare ba? A’a, a Najeriya idan an zargi mutum, ko kotu ta wanke shi zai ci gaba da kasancewa mujrumi a idanun wadanda ba su kaunarsa, walau don kabilarsa ko addininsa ko kuma wata akidarsa can ta dabam.
Wai shin Alhaja Kudirat ce ta farko da aka taba yi wa kisan gilla a kudancin kasar nan? A’a, amma kuma akanta ce kadai aka zargi wasu da yin haka, aka kuma gurfanar da su gaban mahukunta, shari’a kuma ta wanke su da soso da sabulu. To su wane ne aka zarga game da da kisan gillar da aka yi wa wasu fitattun ‘yan kudancin kasar nan kamar su Pa Alfred Rewane, Cif Bola Ige da kuma Alhaja Suliat Adedeji? Ba wanda aka zarga game da haka! An taba tsayawa a binciki yadda mijin Alhaja Kudirat, Cif Moshood Abiola da kuma Janar Sani Abacha suka rasa rayukansu? Ba a yi ba. Akwai wanda zai saba laya cewa wanda ya kashe wadannan fitattun mutane don kokarin tayar da zaune tsaye ba shi ne kuma ya kashe Alhaja Kudirat ba, amma aka nemi batar da sawu, aka dora wa Al-Mustapha?
Kisan kai da ake ta yi a kudancin kasar nan ba kakkautawa, kuma ba a gano ko su wane ne ke aikatawa, ba wani abin mamaki ne ba idan aka yi la’akari da cewa ana yin haka ne don tayar da gagarumar husuma tsakankanin al’ummomin kasar nan ta hanyar haddasa bakar gaba tsakankaninsu don Yahudu da Nasara su ji dadin wanzar da yanayin siyasar da zai ba su daman ci gaba da bin munanan manufofinsu na dankwafar da kasar don kada ta kasance tauraruwar kasashen bakaken fata. Saboda haka nan ma a yanzu za su yi amfani da wannan damar ta samun ‘yancin Al-Mustapha don haddasa gagarumar husumar da za ta farraka kawunan al’ummomin Arewaci da na Yammaci, ta yadda za a daidaita yunkurinsu na kafa sabuwar jam’iyyar hadaka ta APC, don kada ta kawar da gwamnatin da Turawa suka daure wa gindi, wacce kuma suke amfani da shugabanninta wajen danne masu kan macijin don su yi ta wasa da wutsiyar. Bai dai kamata ba a mayar da batun Al-Mustapha na siyasa don gudun kada a ba makiya zaman lafiya damar tayar da husuma a sakamakon haka don cutar da Arewa da ‘ya’yanta. To, ta Allah ba tasu ba. Mutum na nasa ne, Allah kuma na nasa, abin da Allah Ya hukunta shi ne tabbas.