Al-Mustapha ya kai wa Shugaban Izala ziyara a Abuja

A shekaranjiya Laraba ne tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai ziyara ga Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau a ofishinsa da ke Abuja.Manjo Al-Mustaphan ya isa ofishin ne da misalin karfe 2:30 na rana inda da shugaban kungiyar ya tarye shi a daga bisani […]

Al-Mustapha ya kai wa Shugaban Izala ziyara a Abuja
Al-Mustapha ya kai wa Shugaban Izala ziyara a Abuja

A shekaranjiya Laraba ne tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai ziyara ga Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau a ofishinsa da ke Abuja.
Manjo Al-Mustaphan ya isa ofishin ne da misalin karfe 2:30 na rana inda da shugaban kungiyar ya tarye shi a daga bisani suka shiga daga ofishin.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna farin ciki bisa ga ziyarar da Manjo Al-Mustapha ya kawo musu, kuma ya yi masa nasiha game da muhimmancin hakuri da kara jin tsoron Allah a duk inda ya kasance a matsinya na Musulmi.
Ya kara da cewa, Manjon ya dauka wannan tsarewa da aka yi masa jarrabawa ce da Ubangiji Yake yi ga bayinSa. “Ka sani Allah Yana jarraba bayinSa da masifu daban-daban da suka hada da tsoro, yunwa, nakasar dukiya da kuma ta rayuka, amma Allah Ya ce da ManzonSa ya yi bushara ga masu hakuri. Kamar yadda Ya fada cikin Alkur’ani Mai girma.
“Allah ba Ya bambancewa kan wadanda za a yi wa jarrabawar, domin AnnabawanSa da dama Ya jarrabe su, don haka kamar yadda ka yi hakuri, to ka yafe wa wadanda suka zalunce ka, sai Allah Ya kara maka, amma idan ka yi yunkurin ramuwa, to sai Allah Ya bar ka da su.”
Ya gargade shi ya nisanci miyagun malamai da za su iya nuna masa cewa kokarinsu ne ya kai ga kubutarsa. “Babu wanda ya fitar da kai face Allah ,” inji shugaban.
Tun farko a jawabinsa, Manjo Al-Mustapha ya ce ya dauki wannan mataki ne na kawo ziyarar ce musamman saboda irin bayanai da ka yi masa game irin gudunmawar da kungiyar Izala ta bayar wajen yi masa addu’a a tsawon lokacin da yake tsare.
Ya dauki lokaci mai tsawo yana bayanin ukubar da aka yi ta gana masa a lokacin zaman jarun, amma ya ce ya yafe wa wadanda suka kitsa masa wannan makirci, daga bisani ya bukaci kungiyar ta ci gaba da daukarsa a matsayin da, sannan ta rika nuna masa abin da ya dace ko kuma idan ya yi kuskure.