Al-Mustapha ya ziyarci Dokta Ahmad Gumi

Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai ziyara gidan marigayi Sheikh Abubakar Gumi da ke titin Modibbo Adama a Kaduna inda ya gana da halifan malamin Dokta Ahmad Abubakar Gumi.Al-Mustapha ya ce ya ziyarci gidan ne saboda gida ne na kakansa domin tun bai shiga aikin soja […]

Al-Mustapha ya ziyarci Dokta Ahmad Gumi
Al-Mustapha ya ziyarci Dokta Ahmad Gumi

Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai ziyara gidan marigayi Sheikh Abubakar Gumi da ke titin Modibbo Adama a Kaduna inda ya gana da halifan malamin Dokta Ahmad Abubakar Gumi.
Al-Mustapha ya ce ya ziyarci gidan ne saboda gida ne na kakansa domin tun bai shiga aikin soja ba yakan je gidan kuma a can ne ya koyi kyakkywaar tarbiyya ta fadin gaskiya da dagewa a kan gaskiya irin na marigayi Sheikh Abubakar Gumi.
“Ban taba zaton rana irin ta yau z ata zo min da rai ba, amma Allah cikin yardarSa da isarSa da hikimarSa da ikonSa Ya kawo wannan rana. Burin da na saka a cikin zuciyata shi ne zan zo wannan gida da zarar an sake ni. Domin wannan gida gidan kakana ne domin shi Sheikh Gumi kakanmu ne kuma babanmu da muka samu tarbiyya kan halaye masu girma daga wurinsa. Wasu abubuwa da na kiyaye daga gare shi, shi ne rike amana da fadin gaskiya da tsayawa a kanta. Kuma hakan ne suka jawo min matsalolin da na samu kaina a ciki. Amma na san wannan gwaji ne daga Ubangiji kuma bi’iznillahi ba ma rikon kowa a zukatanmu, mun yafe wa kowa,” inji shi.
Mano Al-Mustapha ya ce a lokacin da yake a kulle an sha zuwa ana yi masa barazanar za a kashe shi.
“An sha yi min barazanar mutuwa, an ba ni guba amma da ikon Allah an kai ni asibiti an duba babu ita a jikina. Hikima ce ta Allah ban san yadda ta faru ba, hikimomin Ubangiji a kanmu suna da yawa, shi ya sa muka kasance masu godiya da yafe wa duk wadanda suka zalunce mu. “Addu’armu Allah Ya sa su daina, kuma Allah Ya ba Najeriya zaman lafiya,” inji Al-Mustapha
Da yake jawabi Dokta Ahmad Gumi ya nuna farin ciki da ziyarar ta Manjo Al-Mustapha, inda ya ce Allah Ya halicci dan Adam ne domin ya jarraba shi.
“Idan Allah Ya kare wannan fitina sai ya zo maka da wata, haka rayuwa take a duniya. Idan irin wannan ya samu mutum ya kuma fito lafiya sai ya gode wa Allah. Amma abu mahimmi shi ne kada mutum ya dauki ramuwar gayya. Duk abin da ya auku ka dauka Allah Ya rubuta shi. Kuma duk wanda yake da hannu cikin wannan abu ka yafe masa. Sai a bude wani sabon faifai na rayuwa. Kada a kullaci wani a zuciya, saboda idan Allah bai ba su ikon yin haka ba, ba za su iya yi ba,” inji shi.