Al-Qaeda ta dauki alhakin kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Mali

Al-Qaeda ta kuma yi ikirarin yin garkuwa da mutane biyu.

Al-Qaeda ta dauki alhakin kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Mali

Kungiyar ’yan ta’adda mai alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin harin ta’addancin nan da ya yi sanadin mutuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Mulkin Sojin Mali a wannan makon.

Kungiyar da ke sa ido tare da tattara bayanan sirri a kan yakin da ke gudana a kasar, SITE ce ta bayyana haka a ranar Juma’a.

Oumar Traore, Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Mali, Kanar Assimi Goita, yana daya daga cikin dimbin mutanen da suka mutu a wani harin kwanton bauna da aka kai kusa da iyakar kasar da Mauritania.

A ranar Juma’a kungiyar Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin (JNIM) ta dauki alhakin harin, tana mai cewa ta kashe Traore, ta kuma kama wasu sojoji biyu, a cewar wata sanarwa da SITE ta gani a shafin intanet dinsu.

Traore na cikin tawagar da ke rakiyar injiniyoyin da za su duba yankunan da za a gudanar da aikin tona rijiyar burtsatse a Arewacin babban birnin kasar, Bamako.

Sanarwar da kungiyar SITE, wadda ke sa ido a kan shafin intanet na kungiyoyi masu ikirarin jihadi ta ce kungiyar da ke da alaka da Al-Qaeda ta kuma yi ikirarin yin garkuwa da mutane biyu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Tags