Al-Qaeda ta dora alhakin mutuwar wadanda ta yi garkuwa da su a kan Obama
Qungiyar Al-Qaeda ta dora alhakin mutuwar mutane biyu da ta yi garkuwa da su a kan Shugaban qasar Amurka Barack Obama.Mutane biyu da qungiyar ta yi garkuwa da su sun hada da dan jarida mai daukar hoto dan qasar Amurka mai suna Luke Somers da kuma wani malami dan qasar Afirka ta Kudu mai suna […]
Qungiyar Al-Qaeda ta dora alhakin mutuwar mutane biyu da ta yi garkuwa da su a kan Shugaban qasar Amurka Barack Obama.
Mutane biyu da qungiyar ta yi garkuwa da su sun hada da dan jarida mai daukar hoto dan qasar Amurka mai suna Luke Somers da kuma wani malami dan qasar Afirka ta Kudu mai suna Pierre Korkie.
Qungiyar ta ce mutane biyun sun mutu ne sakamakon yunqurin da Amurka da kuma sojoji Yemen suka yi don qwato su daga sansanin al-Qaeda da ke Kudu maso Yammacin Yemen a ranar Asabar da ta gabata.
“Obama ne ya yanke mummunan hukunci, inda ya sanya hannu a takardar mutuwar dan qasarsa Amurka (Somers).” Inji wani jami’in qungiyar al-Qaeda mai suna Nasser bin Ali al-Ansi cikin wani faifan bidiyo da qungiyar ta fitar a jiya.
Sojojin Amurka da na Yemen sun yi yunqurin ceto mutanen ne ana saura kwana daya a sake Korkie, sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da wadanda suka yi garkuwa da shi.
Sakataren tsaron Amurka US Chuck Hagel ya ce an yanke hukunci ceto Somers ne saboda wadansu dalilai da suka sanya suka gamsu rayuwarsa tana cikin hadari.
Jaridar The New York Times ta ce wadanda suka yi garkuwa da Somers ne suka harbe shi bayan sojojin Amurka da na Yemen sun hada gwiwa don ceto shi.
Jaridar ta ce sojojin Amurka da na Yemen sun same shi dauke da munanan raunuka a jikinsa. Ya mutu a lokacin da aka dauko shi a jirgin sama don kawo shi Amurka.
Idan ba a manta ba dai an yi garkuwa da Somers ne a babban birnin Yemen a Satumba, 2013 a lokacin da yake dauka wa kafar yada labarai ta Yemeni Times hotuna, shi kuma Korkie da matarsa an yi garkuwa da su a watan Mayu, 2013, amma an sake matarsa a watan Janairu, 2014. Kafin mutuwar Somers yana taimaka wa Al Jazeera da hotuna.