Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraqi

Masu goyon bayan dokar sun ce za ta taimaka wajen bunƙasa biyayya ga tanadin addini a ƙasar.

Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraqi

Majalisar Dokokin Iraqi ta zartar da dokar da ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya, inda ta yi tanadin hukuncin shekara 10 zuwa 15 a gidan yari ga duk wanda aka kama da karya dokar.

Gyaran da aka yi wa dokar hana karuwaci na shekarar 1988 wanda ’yan majalisu 170 cikin 329 suka halarta, za a yanke wa masu canza jinsi hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari.

Sannan a ƙarƙashin dokar, ’yan daudu za su fuskanci ɗaurin shekara ɗaya zuwa uku.

Masu goyon bayan dokar sun ce za ta taimaka wajen bunƙasa biyayya ga tanadin addini a ƙasar.

Sai dai ƙungiyoyin sa kai sun ce dokar za ta ƙara goga wa Iraqi kashin kaji, a tsakanin masu ra’ayin neman jinsi ɗaya.

Masu goyon bayan luwadi da maɗigo da kuma karuwanci, da likitocin da ke yin tiyatar sauya jinsi ga masu buƙata, da kuma  an daudu, duk za su fuskanci hukunci a sabuwar dokar.

A baya dai, daftarin dokar da aka zartar a 1980 ta yi tanadin hukuncin kisa ne ga masu neman jinsi.

Sai dai daga baya an yi gyaran fuska ga dokar, bayan fuskantar turjiya daga Amurka da sauran ƙasashen yamma.

Ɗan majalisa, Amir al-Maamouri ya shaida wa kafar Shafaq News, a ranar Lahadi, cewa sabuwar dokar za ta taimaka wajen yaƙi da sabuwar ɗabi’ar neman jinsi da ta bayyana a cikin al’umma, wadda kuma ta saɓa wa addinin musulunci da kuma al’adar jama’ar Iraqi.

Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudirin, Raed al-Maliki, ya ce an jinkirta aiwatar da ƙudirin dokar a farkon watan nan ne saboda ziyarar Firaiminista Mohamed Shia al-Sudani Amurka

Ya ce: “Mun yi ƙoƙarin kaucewa ɗaukar matakin da zai shafi ziyarar ne saboda sun ɗauki dokar a matsayin abin da ya shafi ƴan cikin gida kuma basu son a samu shisshigi daga waje.”

Masu alaƙar jinsi da ake yi wa laƙabi da LGBT a taƙaice sun daɗe suna fuskantar fushin hukumomi a Iraqi, inda a baya ake afani da dokokin tabbatar da ɗa’a da al’ada wajen hukunta su.

Human Rights Watch da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce sun tattara bayanan garkuwa da mutane da azabtarwa da fyaɗe da kuma kisan kai da dama.

A shekarun baya bayan nan an ga yadda manyan jam’iyyun siyasar ƙasar suke sukar masu neman jinsin, ake kuma ƙona tuttocin su, a wajen zanga-zanga da dama.

A cewar ofishin harkokin wajen Amurka dai, aiwatar da wannan doka barazana ne ga ’yancin ɗan Adam da kuma walwala.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce Iraqi ta rushe damar da take da ita, ta bunƙasa tattalin arzikin ta, a fannin janyo hankalin masu zuba jari.

Shi ma sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron, ya bayyana dokar a matsayin wani abu mai haɗari kuma na damuwa ga jama’a.