Alaafin na Oyo: Yana shekara 31 ya zama sarki
An haife shi ranar 15 ga Oktoba, 1938 a gidan sarauta na Alowolodu kuma mamba a majalisar Oranmiyan.
A ranar Juma’a 22 ga Afrilu, 2022, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya riga mu gidan gaskiya bayan shekara 52 kan karagar mulki.
Oba Adeyemi mai shekara 83, wanda kuma shi ne sarki mafi dadewa yana jagorantar masarautar ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Babalola da ke Ado-Ekiti, Jihar Ekiti.
Yayin da al’ummar ke zaman makokinsa, ga wasu muhimman abubuwan tarihi da ya kamata a sani kansa:
- An haife shi ranar 15 ga Oktoba, 1938 a gidan sarauta na Alowolodu kuma mamba ne a majalisar Oranmiyan.
- Ya dare kan karagar mulki a 1970 yana da shekara 31, kwanaki kadan bayan kawo karshen yakin basasa, a zaman gwamnan soja na Jihar Oyo, Kanal Robert Adeyinka Adebayo.
- Wanin abin sha’awa da margayin ke kauna shi ne damben boksin, kuma ya kasance shago har zuwa lolacin da ya zama sarki.
- Ya sauke farali a 1975 sannan a 1990 shugaban kasa na mulkin soja a wancan lokaci, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nada shi Amirul Hajji saboda hidimarsa ga Musulnci.
- Ya kasance Uban Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (UDUS) daga 1980 zuwa 1992.
- Alafin shi ne zaunannen Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Oyo, har zuwa ranar 3 ga Mayu, 2011 lokacin marigyai Gwamna Adebayo Alao-Akala ya yi dokar karba-karbar shugabancin kujerar tsakanin Alaafin da Olubadan na Kasar Ibadan da kuma Soun na Ogbomoso.
- Matansa 13, sai dai an fi ganin shi a taruka tare da uwar gidansa, Ayaba Abibat Adeyemi.
- Ya rasu ya bar ’ya’ya 20 da jikoki da dama, yana da shekara 83, bayan shekara 52 a kan karagar mulki.