Albashin N14m ba ya isa ta —Sanata Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce albashin Naira miliyan 14 da ake biyan shi ya yi kaɗan

Albashin N14m ba ya isa ta —Sanata Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce albashin Naira miliyan 14 da ake biyan shi a matsayin sanata a halin yanzu ya yi kaɗan.

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce Naira miliyan 14 ba sa isan gudanar da ofishinsa da sauran buƙatu a wata guda.

Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels ranar Alhamis da dare.

Orji Kalu wanda ya ce yawancin sanatoci suna yi wa jama’ar mazabunsu abin a yaba, ya ce ba zai ba wa al’ummarsa kunya ba.

Ya ce, “Naira Miliyan 14 ake biya na a wata a matsayin albashi da sauran alawus da kundin hadimaina.

“Kasan cewa da wannan kuɗin nake sa mai a motoci in je mazaɓata? Ai ya yi kaɗan.”

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu