Al’adar tashe na fuskantar barazana a Legas
Ga alamu kimar da tashe yake da ita a idon Hausawan da ke sassa da dama na Jihar Legas ta fara raguwa, inda ake ganin yara kanana suna yi a maimakon matasa majiya karfi kamar yadda aka saba yi a shekarun baya. Binciken Aminiya ya gano cewa Hausawan da ke zaune a Agege da Mil […]
Ga alamu kimar da tashe yake da ita a idon Hausawan da ke sassa da dama na Jihar Legas ta fara raguwa, inda ake ganin yara kanana suna yi a maimakon matasa majiya karfi kamar yadda aka saba yi a shekarun baya.
Binciken Aminiya ya gano cewa Hausawan da ke zaune a Agege da Mil 12 da Idi Araba da Alaba Rago da Okokomaiko da cikin birnin Ikko da Ajah da Lekki da Ilefo duk sun bar tashe ga yara kanana. Haka kuma Hausawan da ke zaune a wurare kamar cikin birnin Ikko da Lekki da Ajah da Apapa da Ifelodun da Ikosi Isheri ba sa yin tashen.
Shugaban Hausawa mazauna Legas, Alhaji Gali Sulaiman ya ce wasu akidun zamani ne suka sa aka yi watsi da tashe a Legas.
“Yanzu a Legas idan ka ce za ka yi tashe sai a rika ganinka kamar bakauye ko kuma kai kidahumi ne, ba dan zamani ba. Kuma su sun manta da cewa tashe al’adar Hausawa ce mai kyau wacce bai kamata a yi watsi da ita ba. Saboda haka nake kira da irin wadannan mutane su daina daukar wasu al’adu suna bata al’adunmu.” Inji shi.
Shi ma Malam Isyaku da ke zaune a Ajah, ya bayyana takaicinsa da irin yadda al’ummar Hausawa da ke zaune a yankin suka yi watsi da al’adar tashe.
Ya ce: “Babu shakka wannan abin bakin ciki ne kuma abin alhini ne a ce Hausawa da ke wannan yankin namu na Ajah sun yi watsi da al’adar tashe. Ba wanda za ka ga yana yi ko yara kanana ma ba za ka ga suna yi ba.”
Malam Isa Muhammadu wanda ke zaune a unguwar Igando cewa ya yi Hausawan yankin ba sa yin tashe. Ya ce: “Hausawan da ke zaune a wannan yanki ba sa yin tashe. Sai azumi ya zo ya wuce amma ba za ka ga Bahaushe ko daya ba yana tashe. Da ka yi magana sai su ce maka ai al’adar da ce kuma kauyanci ne.”
Ya yi kira ga shugabannin al’ummar Hausawa su tashi tsaye wajen ganin al’adar ba ta bace ba.