Aladu sun cinye mai su a gidan gonarsa

Aladu sun cinye wani mutum mai shekara 71 a duniya mai suna Mista Krzysztof (Christopher) da ya je debo ruwa a wata rijiya da take a cikin gonarsa a kauyen Osiek, a Kudancin kasar Poland, bayan da ya fadi a kasa sakamakon ciwon bugun zuciya . Jaridar Daily Mail ta Ingila ta ce dattijo ya […]

Aladu sun cinye mai su a gidan gonarsa

Aladu sun cinye wani mutum mai shekara 71 a duniya mai suna Mista Krzysztof (Christopher) da ya je debo ruwa a wata rijiya da take a cikin gonarsa a kauyen Osiek, a Kudancin kasar Poland, bayan da ya fadi a kasa sakamakon ciwon bugun zuciya . Jaridar Daily Mail ta Ingila ta ce dattijo ya samu bugun zuciya ne ya fadi kasa inda aladunsa 12 da ake kira da aladun Mangalica suka hau kansa suka cinye.

Makwabtansa ne suka gano wasu sassan jikinsa bayan da suka bazama nemansa ganin ba su ganshi ba tun ran jajibirin sabuwar shekara. A lokacin da suka isa wajen rijiyar sun samu sauran kasusuwa a kasa ciki har da kokon kai.

Kakakin masu gudanar da binciken Magdalena Serafin ta fada wa manema labarai cewa: “Makwabtan mutumin ne suka gano wasu kasusuwan jikinsa, inda daga baya kuma suka sanar da hukuma.

An yi wa marigayin ganin karshe ne a ranar 31 ga Disamban bara lokacin da ya tafi rijiyar don ya debo ruwa, kuma a wajen rijiyar ce aka samu sauran kasusuwansa.”

Ta ci gaba da cewa: “Alamu sun nuna aladu ne suka cinye shi.”

Kamar yadda makwabtansa suka fada, Mista Krzysztof  rikakken dan giya ne, za ta iya yiwuwa kuma barci ne ya kwashe shi a lokacin da ya je debo ruwa a rijiyar.

Masu bincike sun ce zai kuma iya yiwuwa ya samu bugun zuciya ne ya fadi lokacin da ya je bakin rijiyar yana kokarin jawo ruwa.

Daya daga cikin makwabtansa ya ce “Ta yiwu ya manta y aba wa aladun abinci ne, kuma barci ya share shi.  Wadannan aladu suna da girma da karfi sosai, suna iya bata komai, cinye shi ba zai yi masu wahala ba. Mu ma muna jin tsoronsu sosai, don haka ba iya matsawa kusa da su.”

Wadannan irin aladu da ake  kira da aladun Mangalica na kasar Hungary ne, wadanda ake yin barbararsu don kiwo a gida. Ana hasashen an samar da zuriyarsu ne tun karni na 19 lokacin da aka hada barbarar a tsakanin aladun gida da aladun daji.

A halin yanzu dai ana tattaunawa kan makomar aladun, wato ko dai a ci gaba da kiwonsu ko kuma a hallaka su

Wadansu mazauna kauyen suna nuna shakkun cewa idan ma an kashe su, akwai yiwuwar za a sayar wa masu hada abinci namansu a birane.

Mai gabatar da binciken ta ce “Barin aladun da ransu ba laifi ba ne.” sannan “Halaka su ba zai shafi binciken da suke gabatarwa ba.”

A gefe daya kuma, Katarzyna Trotzek wacce take aiki da ‘Chrumkowo’ masu kula da aladu ta ce: ‘Ni ban yarda cewa aladun ne suka cinye mutumin ba.

“A koyaushe muna tare da aladu, ana kawo su daga wurare da dama, a wasu lokuta ma za ka ga an bar su da yunwa a kulle cikin keji tare da wasunsu ma da suka mutu. Kuma wadanda suke a raye a cikin kejin ba sa cin gawar ’yan uwansu. Don haka zai yi wuya in yarda cewa su ne suka yi wannan aiki,” inji ta.