Al’adun da ake yi yayin haihuwar ’ya mace
Al’adu da suka kebanci Hausawa dangane da haihuwar ’ya
A duk inda aka yi haihuwa, akan yi wasu abubuwa na al’ada, kuma kowace al’umma da irin nata al’adun a wannan bangaren.
Kamar sauran al’ummomi, Hausawa na da al’adu da suka kebanta da su dangane da abin da aka haifa, mace ko namji. A cikinsu wanne kuka sani?
- Ranar Yara Mata: Aminiya Ta Shirya Rahotanni Na Musamman
- Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (2)
Albarkacin ranar Yara Mata ta Duniya ta 2022, mai taken Yanzu Lokacinmu Ne: ’Yancinmu, Makomarmu, Aminiya ta ziyarci wani gida da aka haifi ’ya mace, inda ta yi magana da mai jego da unguzoma game da haihuwar ’ya da kuma bambancin da ke tsakaninsu a wajen haihuwa da raino da suaransu.
Ta kuma zanta da wata tsohuwa game da dalilin da ya sa ake yin irin wadannan ayyuka da kuma yadda suka samo asali.
Al’adun haihuwar mace
Al’adun da ake gudanarwa a lokacin da aka haifi ’ya mace sun hada da cire beli na makogoro da kuma angurya daga gabanta a wasu wuraren, duk da cewa yanzu akwai masu ganin kuskure ne cire angurya da ake yi wa ’ya’ya mata.
Haka kuma ana yi mata gyaran fuska a maimakon aske mata gashi gaba daya, da hujin kunne don sanya dan kunne.
A wasu wuraren kuma, daga lokacin da aka haifi ’ya mace, akan yi mata lalle domin kwalliya.
Malama Maryam Ali wata uwa ce da a kwanan nan ta haifi ’ya mace, bayan a baya ta haifi ’ya’ya maza uku.
Ta bayyana cewa ta hadu da sauye-sauye wajen gudanar da kula da jaririyarta mai suna Fatima, sabanin yadda ta saba a kan ’ya’yanta maza – Musaddik da Abulkhair da Ahmad.
-
Wanka
A cewar Malama Maryam, wanka ma kadai akwai bambanci tsakanin ’ya’ya maza da mata.
“A lokacin da na yi goyon wadancan yaran, abin da na sani shi ne idan na tashi yi musu wanka ina yi musu ne kai tsaye ba tare da wani bata lokaci wajen wanke wasu bangarori na jikinsu ba.
“Amma da na haifi wannan yarinyar sai aka sanar da ni yadda zan yi mata wanka.
“Don haka idan na zo yi mata wanka ina tsayawa na kula sosai wajen wanke mata matucinta da kyau don gudun shigar wasu kwayoyin cuta da sauransu.”
-
Kwalliya
Ta ci gaba da cewa ba a bangaren wanka kadai ake samun bambanci tsakanin kula da ’ya mace da namiji ba, ta fuskar yin kwalliya ma haka abin yake.
“Kin ga ita ’ya mace idan kika yi mata wanka sai kin zauna kin yi mata kwalliya.
“Bayan na shafa mata mai zan kawo hoda na shafa mata a fuska.
“Sai kin sa mata kwalli har da jambaki da dai duk abin da ya samu na kwalliyar fuskar mata.
“Sabanin namiji da shi kawai man shafawa za a shafa masa.”
-
Shayawarwa
Haka kuma a cewar Malama Maryam, ko a wajen shan nono akwai bambanci tsakanin ’ya’ya maza da mata.
“A yanzu da nake goyon mace na fuskanci cewa ’ya mace ba ta da shan nono kamar namji.
“A lokacin da na yi goyon wadancan yaran, kafin na haife ta na fuskanci sun fi ta shan nono sosai.
“Ita idan ta sha sau daya tana daukar lokaci kafin ta sake nema, ba kamar yadda sauran ’yan uwanta mazan suka yi ba.
“A gaskiya dukkaninsu suna shan nono sosai duk da cewa wani ya fi wani damuwa da nonon.”
Ungozoma
Ita ma wata ungozoma mai suna Yanbiyu Auwalu ta bayyana cewa akwai bambance-bambance wajen kula da jariri namiji da mace.
“Zan iya cewa wajen karbar haihuwa babu bambanci tsakanin ’ya mace da namiji; domin a wannan lokaci duk abubuwan da ake yi wa namji shi ake yi wa mace.
“Sai dai waje daya ne nake tunanin akwai bambanci, wato na yin hujin kunne wanda kuma a matsayina na unguwazoma dole ne na kula da kunnen har sai ya warke.
“Nakan yi hakan ne ta hanyar amfani da garwashin wuta maras yawa na zuba a dan kasko sannan na sami hankici na rika gasa kunnen da shi.”
Hajiya Magajiya Adamu wata dattijuwa ce da ta ga jiya, ta ga yau, ta bayyana cewa ana gudanar da yawanicn al’adun haihuwa ne domin amfanin jariri, don haka a takaice abubuwa ne da ke taimaka wa jikin jariri ya sami cikkakiyar lafiya.
“Kin san shi jikin jariri ba shi da kwari kasancewarsa sabuwar haihuwa. To yana bukatar a yi masa duk abin da zai taimaka masa waje samun cikkakiyar lafiya.”
“Idan kika dauki batun yi wa jaririya lalle za ki ga cewa baya ga kara armashin kwalliya da zai yi a jikin jaririyar, a gefe guda kuma lallen shi magani ne ga fatarta.
“Haka kuma yana zama maganin bakin baki na mutane, kasancewar idan an ga jaririya, musamman wacce take da kyau, za a iya tankawa, to wannan yawan maganar ce ba a so domin zai iya cutar da jaririyar.
“Haka kuma ana yin gashin cibi da kunne ne don cibi da kunnen jaririyar ya samu ya yi kwari tare da warkewa cikin sauri a maimakon a bar shi hakan ya warke don kansa.
Al’adun da ke cutarwa ga ’ya’ya mata
Wasu daga cikin al’adu da yaya mata ke fuskanta tun daga lokacin da aka haife su har zuwa girmansu sun hada da yi musu kaciya wacce aka fi sani da yakan gishiri.
Haka kuma fifita ’ya’ya maza a kansu na daga cikin al’adun da ke cutar da su.
Baya ga wannan’ya’ya mata na fuskantar kalubalen yi musu auren dole, ba tare da son ransu ba.
Yankan gishiri
Game da yi wa mata kaciya, wasu iyayen kan yi wa ’yarsu yankan gishiri ne da nufe tsare ta daga bin maza a lokacin da ta balaga.
A yanzu haka dai hukumomin lafiya suna ta yin Allah wadai da wannan al’ada tare da daukar matakai wajen ganin an daina wannan al’ada.
Binciken masana lafiya ya gano cewa yankan gishiri na cutar da ’ya’ya mata ta fuskar lafiyarsu musamman ma a lokacin da girma ya riske su.
Irin wadanan mata sukan hadu da matsalolin rashin sha’awar aure da kuma matsala a wajen samun ciki da haihuwa.
Fifita maza a kan ’ya’ya mata
Wata matsalar da ’ya’ya mata ke fuskanta ita ce yadda wasu iyayen ke fifita son maza a kansu.
A duk lokacin da ’ya mace ta sami kanta a cikin irin wannan iyali takan fuskanci kunci da karancin kulawar da ta kamata.
Auren dole
Har ila yau ’ya’ya mata na fuskantar al’adar auren dole, kasancewar wasu iyayen sun yi imani da cewa za a iya aurar da ’ya mace ba tare da yardarta ba.
Hakan ya janyo ba su bai wa ’ya’yansu mata zabin fitar da mijin da suke so su aura.
A wasu lokutan ma koda ta nuna wanda take so iyayen, kan yi watsi da zabinta, tare da tilasta mata auren wanda suke so ta aura.
A mafi yawancin lokuta, irin yan matan da suka sami kansu a auren dole sukan karar da rayuwarsu ta aure cikin kunci da takaici domin rashin kaunar wanda suke zama da shi a matsayin abokin zama
A wasu lokutan kuma matan sukan ki amincewa da zabin na iyayensu, inda sukan dauki matakai daban-daban wajen ganin ba su zauna da mazajen da aka aura musu dole ba.
Irin wannan tana kai matan da daukar matakin kisan kansu ko kuma kisan mazajen bayan an yi auren.