Al’adun kasar Sin sun yi tasiri a kan kanen Shugaba Obama
kanen Shugaba Barack Obama na Amurka, Mark Obama Ndesandjo ya saje da Sinawa, bayan da ya shafe shekara 14 a kasar Sin, har ya auri ’yar kasa. Wannan dan uwa na shugaban Amurka ya wallafa ittattafai da ma, har ma wasu ya juya su cikin harshen mutane kasar da cukurkudadden rubutun su. Sannan ya bayyana […]
kanen Shugaba Barack Obama na Amurka, Mark Obama Ndesandjo ya saje da Sinawa, bayan da ya shafe shekara 14 a kasar Sin, har ya auri ’yar kasa. Wannan dan uwa na shugaban Amurka ya wallafa ittattafai da ma, har ma wasu ya juya su cikin harshen mutane kasar da cukurkudadden rubutun su. Sannan ya bayyana matsalar zamantakewa da rikicin iyali, har ma ya soki lamirin mahaifinsa.
“Mutane ba za su damu da ni ba ko la’akari da matsalolin da na bijiro da su, idan da ni ban fito daga zuri’ar Obama ba, don haka ina farihinci da irin wannan tasiri,” a cewar Mark Obama Ndesandjo, kanen Shugaba Obama na Amurka, a lokacin da ya kaddamar da littafinsa da ala wallafa cikin harshen Sinawa, wato mandarin, a Asabar din makon da ya wuce a birnin Beijing.
Littafin san a Ingilishi kuwa, an yi masa lakabin, ‘Takun Obama: Kai kawona wajen fahimtar al’adu uku,” Kam Williams ya sanya shi a mataki na biyu, cikin jerin litattafan da bakaken fata suka wallafa da suka samu shahara a shekara ta 2014. Wallafar littafin a cikin harshen mutanren Sin Kamfanin dab’i ne na masu adabi, al’amarin da aka ce ya yi karin haske game da zuri’ar Obama da Shugaban kasa da mafarkin mawallafin a matsayin san a haifafffen kasar Kenya da ya yi hankoron zama dan Amurka, inda ya kare a kasar Sin.
A littafin Ndesandjo na biyu kuwa ya yi takaitaccen tarihin rayuwarsa, a siffar kirkirarren labari da ya yi wa taken, “daga Nairpobi zuwa Shenzhen: Littafin Soyayya a yankin Gabas,” wanda aka wallafa cikin harsuna biyu, wato Ingilishi da Mandarin (harshen mutanen Sin).
daukacin littattafan biyu sun yi nuni da rikicin zamantakewar iyalan Barack Obama, mahaifin Shugaban kasr Amurka da matarsa Ndesandjo. Matar mai suna Ruth Baker, wadda ta dauki lakabin Ndesandjo, asalinta Bayahudiyar Amurka ce da ta haifi mawallafin, inda ta kasance mata ta uku ga baban Obama. Daga bisani ya saketa, inda ta auri wani mutum mai suna Ndesandjo.
“dole ne in bayar da wannan labarin domin muhimmancinsa in an yi la’akari da rikicin zamantakewar iyali. Kimanin kashi 30 cikin 100 na iyalan da ke fadin duniyar nan suna fama da rikicin,” inji Ndesandjo. “Ina son yi wa dunjiya nuni da cewa hattta zuri’ar shugaban kasa sun yi fama da wannan matsalar, amma mun samu damart shawo kanta..”
“Na samu kwarin gwiwa daga Mark don in bayyana al’amuran rayuwarsa da suka faru a baya,” a cewar Wang Ruikin, Editan littafin da aka wallafa a harshen mutanen Sin.
Littafin na dauke da hotunan iyalai, inda marubucin ya bayar da labrin yadda kakansa, Hussein Onyango Obama ya fice daga wani kauye a kasar Kenya har ya halarci yake-yaken duniya na daya da na biyu da kuma yadda mahaifinsa Barrack Obama ya zama daya daga cikin mutanen Kenya na farko da suka je karatu kasar Amurka; sannan yadda dan uwansa ya zama shugaban kasa, a matsayinsa na bakin Afirka haifaffen Amurka.
“Bayanan Ndesandjo sun fayyace yadda zuri’arsu, har mataki uku suka yi fafutika tare da kwarin gwiwa,” inji Wang. “Wannan shi ne dalilin da ya sa muka yanke matsaya wajen sauya taken littafi na harshen Mandarin, ind aya koma “Fafutika mutum da iyalai.”
Ndesandjo ya bayyana cukurkudaddiya dangantakarsa da dan uwansa (Shugaba Obama), har ma da yaddda suka gana a lokacin da Shugaban Amurka ya ziyarci birnin Beijing, cikin shekarar 2009.
Ndesandjo ya zauna a Shenzhen da ke kudancin kasar Sin tsawon shekara 14, shi ya sa ma yake tunkaho wajen kiran kansa mazaunin duniya.
Bayan harin 11 ga Satumba eda aka kai Amurka, Ndesandjo ya fahimci cewa, rayuwa ta sauya a Amurka, don haka ya yi tunanin zuwa Gabas. Ya sayar da gidansa da motarsa, ya koma Shenzhen, wani birni da ake hada-hada a kan iyakar kasar Sin da Hong Kong.
kwararren makadin Piano, ya kirkiro da wani tsarin amfani da abin kidan da ake yi wa lakabi da “Piano + 1,” wadda dabarar aike wad a kidan Piano da malaman kade-kade zuwa ga makarantun sassan kasar Sin da ake fama da talauci.
“Kida na taimaka musu wajen samun kwarin gwiwa,” inji shi. An kai piano shida zuwa Lardin Sichuan a watan da ya gabata.
Ndesandjo ya damfaru da kaunar al’adun mutanen kasar Sin. Don haka da ya kware a harshen, sai ya rika amfani da sarkakiyar wake-wake da karin magana a littafinsa na baya-bayan nan.
Ya kuma yi kokarin sarrafa cukurkude-cukurden kawata rubutun Sin. A yakin neman zaben shekarar 2008, ya bai wa dan uwansa kyautar zababbben rubutun kawa na mutanen Sin: “Tian Ya Zhi chi,” (ma’ana ka kusa kai ga gaci; yanzu kana daf da isa).
“’Yanci manufa ce ta Amurka, amma na fi jin cewa, ina da ’yanci a kasar Sin,” inji shi. “Na fi zama Ba-Amurke a kasar Sin.”