Alafanun Gwamatin Masari ko akasinta

Katsinawa za su iya tantance dimbin alfanu ko akasin hakan da aka samu cikin watanni takwas da Gwamna Aminu Bello Masari ya yi yana mulki. Siyasa rigar yanci. Siyasa ita ke bai wa mutane dama su zabi wadanda suke so su jagoran ce a gwamnati. Haka takan ba da dama ga masu sha’awar tsayawa takara […]

Alafanun Gwamatin Masari ko akasinta
Alafanun Gwamatin Masari ko akasinta

Katsinawa za su iya tantance dimbin alfanu ko akasin hakan da aka samu cikin watanni takwas da Gwamna Aminu Bello Masari ya yi yana mulki. Siyasa rigar yanci. Siyasa ita ke bai wa mutane dama su zabi wadanda suke so su jagoran ce a gwamnati. Haka takan ba da dama ga masu sha’awar tsayawa takara damar yin takarar duk irin kujerar da suke bukata.Wannan damar ce tasa Aminu Bello Masari (Dallatun Katsina) ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Malumfashi da Kafur a shekarar 1999, karkashin  tutar jam’iyyar PDP. Kuma ya samu nasarar lashe zaben.Ya sake mai-maita wannan kujera a shekarar 2013 inda aloka cinne ya zama Shugaban Majalisar Wakilai.Ya kuma taka rawar gani a wannan kujera inda ya haramta wa Shugaba Obasanjo yin tazarce karo na ukku alokacin.
Haka ya sa kafa ya hambarar da kudurin nan na Turawan Yamna a kan auren jinsi daya, namiji ya auri na miniji, mace ta auri mace. Aminu Bello Masarin a shekarar 2007, ya tsaya takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyar PDP, inda aka yi zaben fitar da gwani tsakanin shi da Ibrahim Shehu Shema da Ambasada Magaji Muhammad da kuma Malam Murtala Ibrahim Safana, inda Ibrahim Shehu Shema ya samu nasara akan su. A cikin shekarar ta 2007 ne Shugaban kasa a lokacin Goodluck Ebele Jonathan ya sa sunan sa a cikin mutanen da za a bai wa mukamin Minista sai dai mukamin ya zama ta leko ta koma ne gare shi ! Domin bai tabbata ba !
Daga nan sai ya canza sheka zuwa jam’iyar adawa ta CPC. A nan ma ya tsaya takarar kujerar gwamna, inda ya fafata wajen zaben fitar da gwani shi da Sanata Yakubu Lado danmarke sai dai ba da kalar da ta barke a zaben ya sa an yi turmi biyu, wajen fitar da gwanin  inda aka ce Yakubu Lado ne ya samu nasara ya yinda shi kuma Dallatun na Katsina ya gar zaya kotu inda ya kalubalanci zaben kuma kotu ta tabbatar masa da cewa, shi ne, dantakara, inda CPC ta gwafza da PDP mai mulki, wadda Gwamna Shehu Shema mai mulki ke mata takara, inda kuma Sheman aka ayyana shi da lashe zaben.Yana cikin CPC aka yi maja (hadaka) da wasu jam’iyyu, inda aka samar da APC a nan ne ya samu zama mukaddashin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa. A shekarar 2015 lokacin da guguwar Janar Muhammadu Buhari ta taso Dallatun. Shi ma ba a barshi a baya ba wajen shiga rigar Buharin, inda har ya samu sa’a ya tsaya takarar gwamna a cikin APC a nan ma wajen zaben fitar da gwanin ya daura zare, tare da dimbin mabukata kujerar kamar Injiniya Mamud Kanti Bello/Sada Ilu/ Abubakar Sadik Yar’aduwa/Abdul’aziz Yar’aduwa(Audu Soja) /Abubakar Isma’il Funtuwa/Abdullahi Aminci/Usman Bugaje da kuma Malam A K Daura.
Duk wannan taron maneman kujerar Aminu Bello Masarin ya yi masu dauka daya ne, inda ya samu galaba akansu. Sai ya gwafza da abokan hamayyar sa na sauran Jam’iyyu irin su, Yakubu Lado na Jam’iyyar PDM da Umar Abdu Tsauri (Tata) na APGA da kuma Injiniya Musa Nashuni daga PDP. A nan kuma guguwar Buhari ta sa Aminu Bello Masarin ya samu galaba akan su, inda hukumar zabe ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan. Sai dai wani hanzari ba gudu ba dimbi al’ummar Jihar Katsina sun zuba ido na ganin Aminu Bello Masari ya gaggauta kai su tudun mun tsira,  ya kuma cire musu kitse a wuta domin ganin yana cikin rigar Buharin da talakkawa ke yi masa kyakkyawar fata. Al’umma da dama sun sa ran cikin ’yan kwanaki rayuwar su za ta inganta.
Sai dai yanzu hawa Dallatun wata na takwas ke nan. Kadan daga nasarorin da ake cewa Gwamnatin Aminu Masarin ta kawo su ne.
1. An samu saukin satar shanu, inda har an kwato dimbin dabbobin da barayi suka sace.
2. An yi tsaftar muhalli na wata daya a kowace gundumar sanata. Daura/Katsina da Funtuwa.
3. Ana ci gaba da kwashe shara a cikin birnin Katsina.
4.Ya samar da injunan samar da hasken wutar lantarki (taransifoma) a wasu unguwannin birnin Katsina.
5.Ya nada kwamishinoni da masu ba da shawara.
6. An sayar da takin zamani ta hanyoyin rumfunan zabe domin takin ya isa ga talaka.
7.Ya dauki kudurin tallafa wa mutane dari da kudin jarin yin sana’a a kowace rumfar zabe maza 40 mata 60, inda aka ba da fom mabukatan suka cike sai dai har yanzu mabukatan sun ce ba su ga wannan tallafin ba’!
 8.Ya yi kasafin kudi na wannan shekara ta 2016.Na Naira Bilyan 111, wanda tarihin Katsina ba a taba yin irin sa ba.  To ! Sai dai abin tambaya ga Katsinawan Dikko, shin sun gamsu da wannan ci gaba da Gwamnatin Masarin take tunkaho ta samar cikin watanni takwas da ta yi ? Shin wannan ne ci gaban da suke bukatar Gwamna Masarin tasa mar masu? Shin gwamnatin ta cancan ci yabo a wadannan watan ni takwas duba da wadannan ci gaba ta take bugun kirjin ta kawo? Amsa ta rage ga Katsinawan na Dikko.
Haruna Muhammad Katsina, shi ne, Shugaban kungiyar Muryar Jama’.Reshen Jihar Katsina. 07039205659 ko [email protected] 07057491050.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno