Alakar “Katin shaidar zama dan kasa” da ci gaban kasa (1)

Matashiya Ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta ne shugabanr Najeriya ya kaddamar da sabon katin shedar zama dan kasa irin na zamani mai dauke da kariya, wato: National Electronic Identity Card (e-ID), wanda a cewarsa, nan gaba shi ne zai zama katin shedar zama dan Najeriya ga kowane dan kasar nan, bayan wasu fa’idoji da […]

Alakar “Katin shaidar zama dan kasa” da ci gaban kasa (1)

Matashiya

Ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta ne shugabanr Najeriya ya kaddamar da sabon katin shedar zama dan kasa irin na zamani mai dauke da kariya, wato: National Electronic Identity Card (e-ID), wanda a cewarsa, nan gaba shi ne zai zama katin shedar zama dan Najeriya ga kowane dan kasar nan, bayan wasu fa’idoji da ya zayyana, kamar yadda Hukumar Lura da Shedar Zama dan kasa (National Identity Management Commission – NIMC) ta sha sanarwa, kafin wannan rana da aka taru don kaddamar da katin.
Bayan zama shedar kasancewarka dan Najeriya, wannan kati zai ba ka damar aiwatar da abubuwa da dama, a zamanance.  Daga ciki akwai iya aiwatar da saye-da-sayarwa ta hanyar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani a jimlace, wato “Electronic Payments/Transactions” kenan.  Sannan, a cewar wannan hukuma, kana iya amfani da katin wajen cire kudadenka daga na’urar ATM (Automated Teller Machine) da ke kafe a kofofin bankunan Najeriya, ko iya biyan kudin hajar da ka saya ta amfani da na’urar cinikayya da ke kafe a galibin shagunan sayar da kayayyakin masarufi a biranen kasar nan, wato: “Point of Sales” (POS), da dai sauran hanyoyi ko na’urori masu iya fahimtar sakonnin da ke like a jikin kati ta hanyar siginar bayanai na zamani.  Wannan, a cewar shugaban wannan hukuma ta NIMC, ba karamar ci gaba ba ce.  Domin ‘yan Najeriya za su samu damar shiga sahun kasashen da suka ci gaba a wannan fage, ba tare da bata lokaci ba.
A wannan mako za mu dubi wannan tsari ne na bayar da katin shedar zama dan kasa, da siffofinsa, da fa’idojinsa ga daidaikun ‘yan Najeriya, da kuma gamammiyar fa’idar ci gaba da ake hasashen wannan tsari zai iya samarwa, don kawo ci gaba.  A karshe kuma za mu dubi kalubale da wasu ke ganin wannan tsari zai iya cin karo da shi – musamman ganin tambarin kamfanin “Mastercard” na Amurka a jikin katin da aka fara bugawa a yanzu –  da shirin da hukumar tace ta yi wajen ganin ba a samu matsala ba.  Galibin tattaunawarmu zai ta’allaka ne ga mahangar tsarin sadarwa na zamani.
Tarihi da Asali
Sabanin yadda wasunmu za su yi tunani, wannan tunani na samar da Katin shedan zama dan kasa ba sabon abu ba ne.  Ba tsari ba ne da tsohon Shugaba Obasanjo ko Babangida ko kuma Jonathan suka fara tunanin kawowa ba.  A’a.  Tunanin samar da katin shedar zama dan kasa ya samo asali ne tun shekarar 1976; tsakanin lokacin mulkin Marigayi Murtala Muhammad da Obasanjo. To amma saboda wasu dalilai na siyasa ko dabi’ar shugabanci, hakan bai samu ba.  Bayan gushewar wannan gwamnati har wa yau an samu wani yunkuri na kokarin samarwa ko tabbatar da wannan tsari na katin shedar zama dan kasa a lokacin mulkin Shugaban kasa Shehu Shagari.  Mataimakinsa, wato Aled Ekweme ya tabbatar da cewa lallai ya yi kokari wajen ganin gwamnati ta samar da wannan tsari a sadda suke mulki, amma nan ma, saboda wasu dalilai na dabi’ar shugabanci, abu bai samu ba.  Bayan wannan kokari, dawowar tsohon Shugaba Obasanjo ma an dawo da wannan tsari, wanda ya sha kasa; ba a samu wata natija mai fa’ida ba, kamar yadda na san mai karatu ya san wannan tarihi gajere.  Sai kuma yunkurin da wannan gwamnati mai ci ke yi wajen tabbatar da wannan tsari.  Duk wata fa’ida da za a zayyana ko yi hasashen samunta karkashin wannan tsari, ta ta’allaka ne kacokam ga karfin zuciyar gwamnati wajen ganin tsarin ya cinma nasara.
Manufa
Manufar samar da wannan tsari dai ita ce don tabbatar da tsari a kasa.  Wannan a fili yake ga duk wanda ya san abin da ke gudana a kasashen da suka ci gaba da masu tasowa.  Kusan dukkan wata kasa da za ka zayyana ta a duniya yanzu za ka samu tana da wannan tsari.  Wannan tsari na samar da wani Rumbun Bayanai ne na kasa, wato “National Database” wanda ke dauke da bayanan ‘yan kasa gaba dayansu; da shekarunsu, da launin fatansu, da launin idanunsu, da matakin iliminsu, da matsayinsu a rayuwa, da tsawon jikinsu, da sana’a ko aikinsu, da kwarewarsu a fanni ko sana’a ko aikin da suke yi, da abubuwan da suke sha’awa a rayuwa, da addinansu, da al’adunsu, da bangaren da suka fito a Najeriya, da inda aka haife su, da inda suke zaune a sadda aka ba su katin, da makarantun da suka yi karatu, da tambarin yantsun hannayensu guda goma, da hotunan fuskokinsu, da sauran bayanan da suka shafe su da nan gaba za a iya lodawa a shafukansu.  
Wadannan bayanai, idan ka hada su gaba daya, na yawan ‘yan Najeriya da suka cika shekaru 16 zuwa sama, za ka samu wani kundin bayanai ne mai tsada, wanda a duk duniya babu irinsa.  Muddin komai ya tafi daidai, wannan zai taimaka wa hukuma ne wajen aiwatar da abubuwa da yawa da za su samar da ingancin rayuwa da ci gaban kasa baki daya.  Wannan ta sa hukumomi a wasu kasashe tuni suka yi nisa wajen wannan tsari.  A galibin kasashe ta hanyar wannan Rumbun Bayanai na kasa hukuma ke yin alaka tsakaninta da talakawan kasarta.  Don haka, babbar manufar samar da wannan tsari shi ne don tsara bayanan da suka shafi ‘yan Najeriya wuri daya, da yin amfani da wadannan bayanai wajen ci gaban kasa.
Me Ke dauke Cikinsa?
Abin da ke dauke cikin wannan kati da za a baiwa kowane dan Najeriya da ya cika shekaru 16 kuwa su ne nau’ukan bayanan da suka gabata.  kari a kan haka, wannan kati zai kunshi bayanan da suka shafi taskar ajiyarka ta banki (in kana son haka), don taimaka maka wajen aiwatar da hada-hadar kudi tsakaninka da bankinka ko kantin sayar da abubuwan masarufi.  Sai bayanan da suka shafi tuki, wato “Driber’s License Information.”  Har wa yau, nan gaba da bayanan da ke cikin wannan kati Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (wato INEC) za ta rika amfani wajen tantance ‘yan kasa a duk sadda zabe ya tashi.  Har wa yau, wannan katin sheda na dauke ne da tambarin yatsun hannunka guda goma (na hagu da dama).  Wannan tambarin yatsu shi ake kira “Biometric Information,” wato bayanan da suka kebance ka, wadanda ta hanyarsu kadai ake iya gane ko waye kai, a duk inda aka sa.  Bayan haka, akwai lambbobi na musamman da kowane kati ke dauke da su.  Wadannan lambobi su ake kira: “National Identity Number.”  A duk sadda aka tashi neman bayananka, wadannan lambobi kawai za a shigar cikin kwamfuta, sai nan take shafin da ke dauke da bayananka da ke taskance a Rumbun Bayanai na kasa (National Database) su bayyana.
Wannan kati an kera shi ne da nau’in roba gasasshe (Plastic Rubbe) mai inganci.  Sannan akwai ma’adana ta musamman (Memory) a jikinsa, wadda a cikinta ne za a taskance dukkan wadancan bayanai da suka shafe ka, kai tsaye.  A jikin wannan kati, abin da ke dauke da wannan ma’adana kuwa shi ne sinadarin tagulla da ake kira “Microchip” irin wanda ke cikin kwamfuta, wanda ke iya rike bayanan da aka shigar masa ta hanyar siginar hasken lantarki irin na zamani (Digital Information).  Idan kana da katin ATM ka dubi bayan katin, za ka ci karo da wani tambari mai launin zinare dan karami; shi ne ma’adanar da ke dauke da bayananka.  To, wannan kati na shedar zama dan kasa ma na dauke da irinsu.  Hukumar NIMC ta tabbatar da cewa nan gaba idan na dan Najeriya ya tashi tafiya zuwa daya daga cikin kasashen da ke Yammacin Afirka (West Africa) ba ya bukatar biza; wannan kati kadai zai goga a na’urar da ke bakin bodar kowace kasa (idan sun sa  wannan na’ura nan gaba kenan).  Wannan ke nuna nan gaba za a shigar da wasu kare-karen bayanai da za su bayar da damar yin hakan kenan.
Ganin cewa akwai hukumomin gwamnati da dama da ke karban bayanan mutane a duk sadda bukata ta tashi – kamar hukumar shirya zabe, da hukumar lura da ababen hawa (bIO), da hukumar ‘yan sanda, da asibitoci, da bankuna, da kamfanonin sadarwar wayar tarho – Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar Samar da Bayanai na kasa (National Bureau of Statistics) da ta samar da wani tsari da zai bayar da damar hade wadannan hukumomi wuri daya, don tabbatar da cewa wannan tsari na shedar katin kasa ya zama makoma gare su wajen neman bayanai, ba wai kowace hukuma ta rika karbar bayanai a nata bangare ba.  Domin a halin yanzu, idan ka je bude taskar ajiya a banki, sai ka bayar da bayanan da suka shafe ka a rubuce.  Idan ka je neman Lasisin Tuki (Driber’s License) sai ka bayar da bayananka.  Idan aka tashi zabe, sai ka je hukumar zabe ta karbi bayananka.  Idan wata matsala ta faru wanda ya hada da jami’an tsaro, sai ka bayar da bayanan da suka shafe ka.  Haka idan lalurar rashin lafiya ta kama ka je asibiti don ganin likita a karo na farko, sai ka sake bayar da bayananka.  Wannan maimaici ne mara tsari, mai dan karen wahala.  Kuma hakan ke nuna babu tsari cikin harkokin gwamnati.  Amma da zarar an samar da wannan tsari na katin sheda, duk zai fa’idantar da dukkan wadannan hukumomi kan dukkan bayanan da suke bukata daga gare ka.

(za mu ci gaba)