Alakar “Katin shaidar zama dan kasa” da ci gaban kasa (3)

Kariya ga Bayanan Kasa Duk da cewa babu wata doka gamammiya ta kasa kan kariyar bayanai (Information Security Law), dokar da ta kafa Hukumar NIMC ta tsara, a takaice, yadda za a alkinta bayanan al’umma.  A sashi na 27, dokar ta tabbatar da cewa Hukumar NIMC za ta tsare bayanan al’umma, ba za ta baiwa […]

Alakar “Katin shaidar zama dan kasa” da ci gaban kasa (3)

Kariya ga Bayanan Kasa

Duk da cewa babu wata doka gamammiya ta kasa kan kariyar bayanai (Information Security Law), dokar da ta kafa Hukumar NIMC ta tsara, a takaice, yadda za a alkinta bayanan al’umma.  A sashi na 27, dokar ta tabbatar da cewa Hukumar NIMC za ta tsare bayanan al’umma, ba za ta baiwa kowa ba, sai tsananin bukata.  Kamar ga hukumar ‘yan sanda idan ana neman bayani kan wani kasurgumin barawo da ya bace, ko neman tambarin tafin hannun wani da ya arce, ko kuma don “Manufar tsaron kasa.”  Wadannan, a halin yanzu, su ne tsare-tsaren wannan hukuma don kokarin tabbatar da cin nasarar wannan tsari na samarwa da rabawa da kuma alkinta bayanan ‘yan kasa, ta hanyar amfani da Katin Shedar Zama dan kasa (e-ID Card).  To amma, bayan bayyanar samfurin katin, kamar yadda aka baiwa shugaban kasa, jama’a sun ga tambarin kamfanin Mastercard a bayansa.  Wannan hakan, kamar yadda masana harkar sadarwa da kariyar bayanai suka tabbatar, alama ce da ke nuna da su dumu-dumu a cikin harkar.  Wannan ya haifar da cece-ku-ce tsakanin ‘yan Najeriya, musamman ma wadanda suke da sanayya mai zurfi kan tasirin hakan ga kasar baki daya, a jumlace.

kalubale
Kamar kowane irin tsari na rayuwa a bangaren mu’amala, ayyukan dan adam ba sa rasa kalubale.  Bayan kaddamar da wannan shiri na gwamnati kan batun Katin Shedar Zama dan kasa, masana da dama sun ambaci matsaloli ko wasu kalubalen da ke jiran wannan shiri, kamar sauran tsare-tsaren gwamnati.  
kalubale na farko shi ne rashin wata doka mai fadi wacce za ta baiwa dukkan wasu bayanai da ake tarawa ko karba daga jama’a, kariya na musamman a bangaren hukunci.  Misali, idan wani ya kutsa cikin Rumbun Bayanan kasa (National Database) ya sace bayanan jama’a, har a karshe aka kama shi, babu wata doka da ta yi bayani dalla-dalla kan ga yadda za a yi da shi, ga irin hukuncin da za a yanke masa, ko tarar da za a yi masa.  Wannan na cikin manyan kaalubale da ke fuskantar wannan tsari.  Domin dokar da ta kafa hukumar NIMC ba ta yi dogon bayani ba.  Ta dai nuna cewa wajibi ne hukumar ta tsare wa ‘yan Najeriya bayanansu, sannan ba za ta baiwa kowa ba sai da dalili mai karfi, kamar abin da ya shafi tsaron kasa ko makamancin haka.
A sauran kasashen da suka ci gaba, irin Ingila misali akwai doka ta kasa ta musamman da ‘yan Majalisar kasar suka samar mai suna “Data Protection Act, 1998” wadda ke bayani filla-filla kan dukkan abubuwan da suka shafi kariyar bayanai, da hakkin jama’ar kasa wajen kare musu sirri da mutuncinsu ta hanyar hana wasu ko wani dan ta’addar Yanar Gizo sace musu bayanansu na sirri, da irin hukuncin da za a yanke masa idan har aka kama shi da wannan laifi.  Haka ma wasu kasashen, suna da irin wannan doka.  Amma a Najeriya har yanzu babu wata doka ta kasa gamammiya, ta musamman wacce ke bayar da kariya ga sirri da bayanan jama’ar kasar.  
Masu korafi kan rashin wannan doka sun nuna cewa babbar illar hakan kuwa shi ne, a karshe muna iya samun kasarmu kamar yadda kasar Amurka ta samu kanta.  Kasar Amurka tana da dokoki na kariyar bayanai, amma barkatai suke; babu tsari, sannan babu daidaito kan hukuncin da suka tanada ga wanda ya aikata laifi irin wannan.  Kuma tunda har an samu kamfanin Mastercard, wanda kamfani ne dan kasar Amurka, a cikin wannan tsari, dole jama’a su damu.  Domin hakan na nuna cewa wannan kamfani zai samu bayanan ‘yan Najeriya kenan a tafin hannunsa.  Abu na biyu kuma suka ce buga tambarin wannan kamfani a katin da za a baiwa kowane dan Najeriya a matsayin Katin Shedar Zama dan kasa, bai dace ba.  Domin hakan na nuna rashin alkinta wa ‘yan Najeriya mutuncinsu ne daga wani sabon tsarin mulkin mallaka, kamar dai irin tambarin da ake wa bayi lokacin mulkin mallaka, idan an debo su a jirgin ruwa za a kaisu kasar Amurka ko gonakin rake dake kasar Burazil.
Bayan damar da wannan kamfani zai iya samu na bayanan sirrin ‘yan Najeriya, kalubale na gaba shi ne, wasu ‘yan Dandatsa (Hackers) na kasar Amurka ko wasu kasashe na iya sace bayananmu ta hanyar wannan kamfani, tun da a Amurka yake.  Wannan mahanga ta samo asali ne sanadiyyar badakalar hankado bayanai da ake tayi a  Amurka, inda wasu ke iya kutsawa cikin rumbun adana bayanan hukumar tsaron Amurka ma gaba daya, su sace bayanai, su kuma bayyana wa duniya abubuwan da suka hankado.  Ba wannan kadai ba, ita kanta hukumar  Amurka ba amintacciya bace wajen abin da ya shafi leken asiri.  Wannan ya fito fili karara sanadiyyar badakalar Snowden da na Wikileaks, inda ya tabbata cewa lallai hukumar tsaron Amurka na tursasa wa kamfanin sadarwa (irin su Google da Yahoo da Facebook dsr) su ba ta bayanan mutanen da suke mu’amala da su a shafukansu, wanda wannan haramun ne a ka’idar yarjejeniya.  Wannan ya dada fitowa fili cikin wani bincike na musamman da kamfanin PEER 1 ya gudanar kan kamfanonin kasashen wajen da ke da rumbun bayanai a kasar Amurka.  Ya ce kashi 25 cikin 100 na ire-iren wadannan kamfanoni sun janye bayanansu na sirri daga kamfanonin da ke da rumbun adana bayanansu a Amurka, sannan kashi 81 cikin 100 na wadanda har yanzu ake adana musu bayanansu a Amurka, suna son sanin a ina ne hakikatan, ake ajiye musu bayanansu?  Wannan, a cewar masana, alama ce da ke nuna karancin aminci da kamfanonin kasashen waje ke da shi kan kamfanonin sadarwa na Amurka.  In kuwa haka ne, don me Najeriya za ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da ta shafi bugawa da tafiyar da tsarin biyan kudade ko aiwatar da ciniyyar kudi da kamfanin Mastercard?
A nata bangare, hukumar NIMC ta nuna cewa babu wata matsala kan haka.  Domin alakar da ke tsakanin Najeriya da kamfanin Mastercard bai kai iya haddin da ake kambama shi ba.  Na biyu, hukumar ta ce matsayin kamfanin Mastercard a wannan aiki shi ne baiwa masu dauke da wannan kati damar iya aiwatar da cinikayya na kudi.  A lokacin da aka zo baiwa kowane dan Najeriya, inji wannan hukuma, kana da dama kace a kulle maka wannan tsari daga katinka.  Idan kuma kana bukatar haka, sai a bude maka.  Wannnan, inji wannan hukuma, zabi ne ga kowane dan Najeriya.  Dalili na uku, hukumar ta nuna cewa a Najeriya ne za a adana wadannan bayanai, cikin kwamfutoci, kuma ‘yan Najeriya ne za su tafiyar da tsarin ba jami’an wannan kamfani ba.  Don haka babu wata matsala.
Kammalawa
A karshe, wannan tsari ne mai muhimmanci, amma kamar yadda bayanai suka gabata, Gwamnatin Najeriya na da sauran aiki a gaba wajen ganin ta tabbatar da tsare-tsaren da ta ayyana.  Domin wannan fargaba da jama’a ke samu ya samo asali ne sanadiyyar rashin amintuwa da suke yi don sakacin hukuma wajen aiwatar da ayyuka masu muhimmanci.  Bayan haka, dole ne ‘yan Majalisa su yi tunanin fitar da doka gamammiya wacce za ta dunkule ta kuma fayyace dukkan dokokin da suka shafi karba, da adanawa, da sarrafawa, da mikawa (in bukata ta tashi) da kuma ladabtar da dukkan wanda ya yi ta’addanci kan wadannan bayanai na sirri na ‘yan Najeriya.  Ba kafa dokar kadai ba, dole ne hukuma ta tabbatar an aiwatar da su a duk sadda bukata ta tashi.  Wannan ne kadai zai rage fargabar jama’a, ya kuma kara wa jama’a kwarin gwiwa kan cewa lallai da gaske take.