Alakar wayar salula da mahallinmu (2)

Wayar Salula a Banki Wannan abu ne sananne, idan ka samu kanka a banki, kashe wayar salula dole ne. Tabbas za ka ga wasu na aiwatar da kira a cikin banki, amma wannan ya saba wa doka. Mu lura fa, don wasu sun saba doka ko an saba kin bin doka a al’ummar da kake […]

Alakar wayar salula da mahallinmu (2)

Wayar Salula a Banki

Wannan abu ne sananne, idan ka samu kanka a banki, kashe wayar salula dole ne. Tabbas za ka ga wasu na aiwatar da kira a cikin banki, amma wannan ya saba wa doka. Mu lura fa, don wasu sun saba doka ko an saba kin bin doka a al’ummar da kake rayuwa a ciki, ba lasisi ba ne a wajenka kaima ka zama haka. Duk sadda aka karkace, kai ka gyaru. Don haka a banki ba a amsa waya ko aiwatar da kira. Dalilin a fili yake. Banki waje ne na hada-hadar dukiyar jama’a, kuma miyagu na iya amfani da wayar salula wajen hada baki da miyagu ‘yan uwansu, su shigo su aiwatar da ta’addanci yadda suka so. Ba wayar salula kadai ba, hatta mota idan ka je da ita harabar banki, dole ka fita daga cikin motar, ko ku fita kai da wanda ko wadanda kuka je tare, su zauna su jira ka a cikin bankin. Amma ba a jiran abokin tafiya a cikin mota a harabar banki. Sai a kiyaye.

Wayar Salula a Gidan Biki
Babbar Magana. Wannan ba sai an yi dogon bayani ba. A wajen mata wannan sanannen lamari ne, cewa babu abin da aka fi farauta, ido bude, irin wayar salula. Wannan ya faru ne ganin cewa su mata ba aljihu ba ne da su, sai dai jaka. Kuma tun da gidan biki wuri ne na ci da sha da dabdala, wannan ke haifar da shagala ga duk abin da aka tafi da shi can din. Shi ya sa sace-sace suka yawaita a gidan biki. Tun fitowar wayar salula har zuwa yau, a duk sadda Maman Sadik za ta fita gidan biki daga cikin nasihar da nake yawaita nanata mata akwai lura da wayar salula. Domin su mata akwai su da son nuna birgewa (ku yi hakuri ba zargi ba ne, a dabi’ance nake nufi). Duk inda suka je a tsakanin junansu sukan so nuna abin da Allah Ya yi musu na falala da ni’ima. Wata ‘yar uwa ke sanar da ni kwanakin baya cewa idan mata suka hadu a gidan biki, da zarar mace ta shigo da kwalliya, abu na farko da ake fara dubawa shi ne kasan zanin da ta daura, don tantance shin, hadadde ne ko gijari-gijari ne.

Wayar Salula a Yayin Tuki
A sauran kasashen da suka ci gaba a tattalin arzikin kasa, daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yawan hadarurrukan mota a titunan kasashensu akwai yawan amfani da wayar salula a yayin tuki. Kwanakin baya wani bawan Allah, matashi, ya haye kan wasu ‘yan mata biyu da ke gefen titi suna tafiya a titin kafa (Pabement). Bayan ya murkushe su sai kawai ya wuce abinsa. Daga baya da aka kama shi, sai ya rantse da Allah cewa shi bai san cewa dan adam ya buge ba. Ya ce shi ya dauka robar gorar ruwa ce ya bi ta kanta kawai. Mece ce matsalar? A sadda ya kade wadannan ‘yan mata biyu, wayar salula ce a kunnensa. daya daga cikin wadannan ‘yan mata biyu sai bayan kwanaki shida ta farfado daga dogon suman da ta yi. Da aka bincika sai aka tarar kwakwalwarta ta samu dameji (Brain Damage) sanadiyyar buguwar da ta yi a yayin hadarin. Wannan kadan ne daga cikin matsalolin yin waya a yayin tukin mota ko kowane irin abin hawa ne. Idan kana tukk, ka hakura da wayar salula, wajen amsa kira ne ko aiwatar da kira. Idan kana da tsananin bukata, ka sauka gefen titi inda babu matsala ga motoci masu wucewa, ka yi abin da kake son yi, bayan ka gama sai ka ci gaba da tafiya.

Wayar Salula a Jirgin Sama
Idan ka zo kashe wayarka, musamman idan ta zamani ce, za ka ga wani tsari mai suna: “Flight Mode.” Wannan tsari idan ka latsa shi, zai dauke yanayin sadarwar wayar ne gaba daya; babu wanda zai iya isa gare ka, kuma kaima ba za ka iya aiwatar da kira ko aika sakon tes ba. Duk wani abu mai alaka da yanayin sadarwa (Network) ba za ka iya aiwatar da shi ba. Wannan tsari an sa shi ne musamman don masu hawa jirgin sama. Aiwatar da waya ko duk wani abu mai alaka da yanayin sadarwar tarho a yayin da jirgi ke kokarin tashi sama ko sauka a filin saukarsa, hadari ne mai girman gaske. Yana iya zama shamaki ga sadarwar da direban jirgin ke yi da masu ba shi umarni a inda yake son isa ko sauka. Hakan kuma, kamar yadda muka sani, na iya zama sanadiyyar hadari da salwantar rayuwar duk wadanda ke jirgin da wadanda ke wurin da hadarin zai auku. Don haka, idan ka shiga jirgi, ka kashe wayarka kawai. In so samu ne ma ka bari sai ka sauka ka kunna. Minti nawa ne?

Wayar Salula da Kananan Yara
Muna rayuwa ne kwanmu da kwarkwatanmu. kananan yara suna cikin marhalar rayuwa na farko ne. Da jinsu, da ganinsu, da tsarin fahimtarsu duk ba su habaka ba. Don haka duk wani sauti da ya wuce kima, ko wani haske mai kaifi daga wayar salula, dole ne a kare kananan yara daga gare su. Ba birgewa ba ne (wai tafiya ba wando), a sake wa kananan yara wayar salula don kawai ana son su. Girgizan wayar (bibration) na iya firgita su. Sautin waya mai kara na iya firgita su. Hoton bidiyo mai hasken gaske cikin duhu na iya yi wa idanunsu illa, idan hakan ya zama al’ada. Don haka sai mu kiyaye. Da muguwar rawa, inji Hausawa, gwamma kin tashi.

Kammalawa
Wannan shi ne karshen doguwar kasidar da muka daddatsa ta tun shekarar 2010 kan wayar salula. Kamar yadda mai karatu ya sani, muna cikin wani zamani da tsarin kere-kere musamman na kayayyaki da ka’idojin sadarwa ke canzawa kusan dukkan mako ko wata. Shi ya sa bibiyar ka’ida ita ce kadai hanya mafi sauki wajen nakaltar wannan ilimi mai mahimmanci. Idan Allah Ya yarda, kamar yadda na sanar a farko, za a buga wannan kasida a matsayin littafi mai zaman kansa. Idan haka ta kasance, zan sanar da masu bukata. Allah Ya yi mana jagora baki daya, amin.