Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani
Gwamnatin Uba Sani ta sallami wasu mukarraban El-Rufai, wanda shi kansa take zargin sa da almundahanar biliyoyin kudade
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsohon uban gidansa kuma magabacinsa Malam Nasir El-Rufai.
Uba sani ya ce babu kamshin gaskiya a maganganun da ke yawa cewa shi da tsohon gwamnan El-Rufai suna zaman doya da manja.
Ya bayyana haka ne a yayin hirar da kafar tala bijin ta TVC ta yi da shi a ranar Litinin, inda ya ce “alakarmu tana nan yadda ta ke, babu wata matsala, kamar yadda ake rade-radi.”
Am fara tunanin cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Uba da El-Rufai ne bayan da gwamnati mai cin ya yi zargin Gwamnatin El-Rufai da barin masa bashin biliyoyin Naira da kuma karkatar da wasu kudade.
- Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji
- Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba
A kwanakin baya Gwamnatin Uba Sani ta sallami wasu mukarraban El-Rufai da ke cikinta, masu rike da mukaman kwamishinoni kan zargin badakala.
Masu sharhi da magoya bayan tsohon gwamnan dai na zargin Gwamnatin Uba Sani da yi wa Nasir El-Rufai da mukarrabansa bi ta-da-kullin siyasa, zargin da ta karyata.
Zargin El-Rufai da karkatar da kudade, ya kai ga Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken El-Rufai, wanda ta ce ta same shi da laifin da ake zargin sa, amma tuni ya musanta zargin.
Amma da aka yi wa gwamnan tambaya game da hakan, ya bayyana cewa bangaren majalisa na aiki ne a matsayin mai cin gashin kansa ba a karkashin gwamna ba, kuma suna da ’yancin gudanar da ayyukansu.