Alamu sun nuna Jam’iyyar APC za ta karbi gwamnatin Filato a shekarar 2015 – Nazifi
Tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Jihar Filato a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP Malam Muhammad Nazifi Ahmed ya ce bisa ga dukkan alamu Jam’iyyar APC za ta karbi gwamnatin jihar daga hannun Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015. Malam Nazifi Ahmed ya bayyana wa wakilinmu a Jos cewa jam’iyyarsu ta APC ta samu karbuwa a […]

Tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Jihar Filato a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP Malam Muhammad Nazifi Ahmed ya ce bisa ga dukkan alamu Jam’iyyar APC za ta karbi gwamnatin jihar daga hannun Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015.
Malam Nazifi Ahmed ya bayyana wa wakilinmu a Jos cewa jam’iyyarsu ta APC ta samu karbuwa a jihar, domin ba ya ga jam’iyyun ACN da ANPP da CPC akwai jam’iyyun LP da DPP da wasu magoya bayan PDP da suka shigo APC a jihar.
Ya ce matsalar da suka samu ita ce kawai wasu sun nemi su nada shugabancin riko daga sama. Ya ce amma daga baya shugabannin jam’iyyun da suka yi hadaka a jihar sun yi taro suka yanke shawarar ba ACN shugaban riko, ANPP sakatare, CPC ma’aji.
Malam Nazifi ya ce sun gaya wa masu kokarin nado musu shugaba daga sama cewa haka bai dace ba. “Domin mu ne ‘ya’yan jam’iyyun kuma mun san ’yancinmu, don haka wannan ba zai yiwu ba,” inji shi.
Ya ce duk wanda ya san tarihin siyasarsu a Jihar Filato ya san ba su taba canja jam’iyya ba, duk jam’iyyar da suka shiga da wuya da dadi suna nan a cikinta. Don haka ya yi kira ga uwar Jam’iyyar APC ta kasa kan ta yarda da abin da shugabannin suka yanke shawara a kai, domin a samu zaman lafiya a cikin jam’iyyar ta yadda za ta ci gaba bunkasa a jihar.