Al’amuran Rayuwa: Tunatarwa ga shugabannin al’umma
Masu karatu, ina yi muku gaisuwa kamar kullum, Assalamu alaikum. Bayan haka, a yau za mu karkata akala ne zuwa ga wani rukunin al’umma mai muhimmanci a rayuwa, watau manya ko kuma mu kira su da shugabanni ko jagororin al’umma. Za mu duba yadda za mu tunasar da su kan wasu al’amura da suka shafi […]
Masu karatu, ina yi muku gaisuwa kamar kullum, Assalamu alaikum. Bayan haka, a yau za mu karkata akala ne zuwa ga wani rukunin al’umma mai muhimmanci a rayuwa, watau manya ko kuma mu kira su da shugabanni ko jagororin al’umma. Za mu duba yadda za mu tunasar da su kan wasu al’amura da suka shafi rayuwa.
Idan ana maganar manya ko shugabanni, ke nan ba za mu ce mu koya musu rayuwa ba, sai dai tunasarwa, domin kuwa sun dade da sanin abin da ke cikin rayuwar. Abin da za mu yi a nan shi ne, za mu ba su ’yan shawarwari ne, domin akwai bara-gurbi da yawa daga cikinsu. Shi ya sanya za mu yi wannan tunasarwa domin su koma daidai bisa hanya, don su zama abin koyi na gari ga matasa masu tasowa, domin an ce barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe, kuma da na gaba akan ga zurfin ruwa.
To, yanzu za mu fara da wasu kadan daga cikin irin wannan tunasarwa, kuma in Allah Ya yarda, za mu tabo kowane loko da manya suke zama. Babbar fa’idar dai ita ce, mu fahimtu da rayuwa, domin a gudu tare kuma a tsira tare. Mun dai gane tun da wuri, cewa, rayuwa al’amari ce mai dadi kuma mai wuya. Allah Ya yi mana muwafaka da samun dadinta, idan wuyar ta zo kuma, Allah Ya saukaka mana ita, domin ta zama zakka ga rayukanmu.
Kamar yadda na fada a baya, yau kuma tunasarwa ce nake dauke da ita, ba ga kowa ba sai ga manyanmu kuma shugabanninmu, wadanda suke shugabancinmu a kowane sakade na rayuwa. Da farko dai ina son sanar da iyayena cewa, su fahimce ni da basira, domin duk abin da zan fada nan dama sun riga ni saninsa, kasancewar daga gare su ne ma muka samu tubarrakin sanin haka.
Wannan tunasarwa tawa ga manya, ba tana nufin raini ne ba, ba tana nufin cewa zan koyar da manyana ba ne, illa iyaka irin abin nan ne da Hausawa ke cewa, motsi ya fi labewa. Na aiko muku da wannan tunasarwa ce kawai domin kara yin tuni gare ku, da nufin jaddada muhimmin nauyin da ke kanku, domin ku tuna ku sake kaimi wajen tallafar wannan nauyi da girma ya dora muku. Kuma ina ganin lallai za ku fahimce ni, domin kun dade da sanin karin maganar nan da ke cewa, gyara kayanka, ba zai zama sauke mu raba ba.
Ya manyana, da ku nake wannan batu, kuma idan na ce manyana, ina nufin kakannina, iyayena, masu unguwannina, shugabannina sarakunana, shugabannina ’yan siyasa, malamaina shugabannin makarantu, shugabannina manyan ’yan kasuwa da duk wani babban da ya san cewa shi babba ne, wanda ya samu kansa bisa shugabancin wani abu, ko wata kungiya, ko wani kamfani. Duk wadannan, maza da mata, kun cancanci ku zama shugabanni kuma manyana, domin kuwa girma ne ya ba ku wannan mukami ba ni na ba ku ba. Sai ku kara ba ni uzuri, domin sauraren wannan ’yar tunasarwa tawa da ta shafi rayuwa, amma ku kara hakuri da irin wautata da zan nuna, idan har hakan ta faru.
Tun farko dai ina jan hankalinku ya manayana, ku gane cewa ku ne shugabanni ta kowane fanni. Daga gare ku ne ake gane zurfin ruwa, kuma daga gare ku ne duk wani salon rayuwa ke darsuwa ga al’umma. Idan babu ku a cikin al’umma, ana nufin al’amari ya lalace ke nan, domin kowa zai zama a wargaje ke nan. Ai kun nuna mana cewa ma da tsohuwar zuma ake magani. Ashe ku ne zumar ke nan, kuma ku ne likitocin auna ta. Don haka ya dace ku rika yin aikin manya a kowane lokaci, ku nuna wa yara cewa ga yadda rawar kidan ya kamata ta kasance.
A lokacin da babba ya aikata wani aiki komai kankantarsa, ya sani cewa darasi ne ya aika, ko ya koya wa na bayansa. Idan na bayan nan ya gani ko ya ji batu daga babba, babu abin da zai zo masa a tunani ko a kwakwalwa sai batun cewa wannan abu daidai ne, don haka shi ma bai da wani zabi da ya rage masa, illa ya kwaikwaya, kuma ya aiwatar da shi a gaba. Bisa ga wannan dalili ya kai babba, duk abin da za ka aikata, ka tsaya tukunna ka yi nazari, ka aikata abin kirki, wanda zai zama abin kwatance nakwarai. Idan za ka furta kowane kalamai, ka yi tunanin furta alheri, domin kuwa abin koyi ne ga na bayanka.
Zan dan tsaya nan a wannan makon, in Allah Ya kai mu makon gobe, zan dora daga nan. Allah Ya sada mu da alheri, amin!