Al’amuran Rayuwa: Tunatarwa ga shugabannin al’umma (3)
Tare da sallama nake sake bude wannan fili, kuma nake ci gaba da wannan muhimmiyar tunasarwa da nake rubutawa ga manyana. Idan ba ku manta ba, makon da ya gabata, na tsaya ne daidai inda na kammala ba shugabanni ’yan siyasa shawarwari, inda kuma a yau zan ci gaba in Allah Ya yarda.Sarakunan gargajiya: Ya […]
Tare da sallama nake sake bude wannan fili, kuma nake ci gaba da wannan muhimmiyar tunasarwa da nake rubutawa ga manyana. Idan ba ku manta ba, makon da ya gabata, na tsaya ne daidai inda na kammala ba shugabanni ’yan siyasa shawarwari, inda kuma a yau zan ci gaba in Allah Ya yarda.
Sarakunan gargajiya: Ya sarakuna iyayen kasa, yau kuma ga ni durkushe a gabanku, musamman domin in kawo caffa, a lokacin da nake dauke da wasu ’yan shawarwari a matsayin tunasarwa gare ku da mu mabiyanku gaba daya. Domin kuwa na ga mutane sun fara mancewa da irin kimarku a cikin al’umma, kamar kuma yadda na ankara da yadda gwamnatocin siyasa ke neman mayar da ku tamkar gugar yasa, idan an gama sai a jefar da ku a gefe daya. Ni dai na yi imanin cewa kuna da tsananin muhimmanci ga al’umma, don haka ya dace a ce ana ba ku matsayinku na musamman da ya dace da ku cikin al’umma.
Kamar yadda na karanta a tarihi, fasihin malamin nan, marigayi Sa’adu Zurgur ya taba ba da shawarar cewa, kada mu sake mu watsar da kimar mulkin sarakuna, kada mu sake mu amshi jamhuriya alhali tsarin mulukiya shi ya fi muhimmanci da yanayinmu. To, amma abin takaicin shi ne, mun watsar da wannan muhimmiyar shawara, wanda haka ya sanya darajarku ta rage, kuma aka saukar muku da karfin mulki, wanda haka ya haddasa wai shugaban karamar hukuma ma kawai ya fi ku iko da izzar mulki, kawai don wai tsarin mulki ya nuna haka.
To, ni dai babbar shawarar da zan kara ba ku a saman ta marigayi Sa’adu Zungur ita ce, don Allah ku rike girmanku, wanda haka zai sanya ku samu bakin yi wa talakawanku aikin da ya dace na shugabanci. A baya, an nuna cewa kuna yin sakaci da mutuncinku, kuna kaskantar da darajar mulkinku, wanda haka ya sanya wanda bai kai ya kawo ba ma, sai ya rika yi muku wani gani-gani. Idan dai har kuna son ci gaba da tasiri, to lallai ya dace ku kama girmanku, ku amshi kambinku na iyayen kasa, ku rungumi kowa ba tare da bambanci ba. Wannan lallai zai taimaka wajen kawo muku muhibba da kima wacce ta dace da ku, a matsayinku na manyan kasa.
Shugabannin ma’aikatu da ’yan kasuwa: Ku ma fa shugabanni ne ga al’umma, kuma al’amuranku na shafar jama’a ta bangarorin rayuwa daban-daban. Yana da kyau ku kula da nauyin da ke kanku, musamman wanda ya danganci ma’aikatan da ke karkashinku. Kula da tafiyar da al’amuran aikin ma’aikatarku abu ne da ya zama wajibi, wanda da haka ne za ku iya kare hakkokin da suka rataya a kanku, a matsayinku na shugabanni. Akwai wata al’ada ta son kai da wasu shugabanni ke nunawa, wato su nuna son wani fiye da wani, alhali duk ma’aikata ne bai daya. Wannan hali babu abin da zai haifar sai rashin jituwa da rashin ci gaba a ma’aikatar da kai kanka ke shugabanci. Domin ta wannan hanya ce girmanka da mutuncinka za su zube a idanun wadanda ka nuna wa son kai din. Kuma daga nan ka kawo rashin jituwa ke nan tsakanin al’ummarka, domin kuwa shi wanda ka dauka dan lele, zai samu kalubale daga wadanda ka mayar ’yan bora. Idan haka ta faru, to lallai babu wani abu na kirki da zai rika wakana a tsakaninsu, wanda haka zai shafi ci gaban wannan ma’aikata ko kamfani.
A matsayinka na dan kasuwa, akwai abubuwa na rayuwa da ya kamata ka fuskanta. Ya dace ka sanya wa kanka natsuwa, musamman wajen gudanar da harkarka ta kasuwanci. Misali, kada hankoron neman tara abin duniya ya sanya ka wuce makadi da rawa. Duk iya dukiyar da za ka tara, ka sani cewa ba za a kai ka kabari da ko ranyo ba. Iyakar ka nan duniya. To me zai hana ka yi amfani da dukiyar taka wajen kawo wa marasa shi farin ciki? Idan ka yi kyauta da taimako da dukiyarka, haka shi zai fi alheri da ka yi mako. Ka kasance mai saukaka wa al’umma ta hanyar sana’a ko aikinka, babu shakka wannan zai kawo maka martaba da muhibba; kamar kuma yadda za ka samu ladar kyautatawar da ka yi wa al’umma.
Iyaye maza da mata: Iyayena, ku ma ga ni nan gare ku. Wannan wasika ba za ta shallake ku ba, sai ta fada kanku, saboda ku ne shugabannina na farko, ku ya kamata ku tarbiyantar da ’ya’yanku tun daga gida, ta yadda idan suka fita waje za su kawo maku kyakkyawan suna, kuma su kare mutuncinku. Wannan batu haka yake, dole sai kun zage damtse, kun yi jan ido. Wajen yin jan idon, dole sai kun yi nasiha. A wajen yin nasihar, sannan ’ya’yanku za su dauki turbar kwarai. Abin da aka sani shi ne, duk lokacin da aka ga yaro ya lalace, na farko da za a dora wa laifi ku ne iyaye. Haka kuma idan an ga yaro na kirki, mai halin kiriki, mai da’a da kishin kasa, ku iyaye ne na farko da za a fara yaba ma wa.
Ku ya kamata ku tsaya kai da fata, ku tabbatar kun ilimantar da ’ya’yanku, su fahimta da ilimin zamani da na addini, kuma su san ya kamata, musamman ma wajen iya mu’amala da al’umma. Wannan idan kun yi, kun taimaki kanku, kun taimaki yaran naku, kuma kun taimaki kasa baki daya.
Ya shugabnni gaba daya, wadannan ’yan shawarwari, lallai suna da bukatar a duba su kuma a saurare su. Bayan haka, ya dace a sanya su a aikace, domin dai a samu fa’idar rayuwa ta kirki. Ina da yakinin cewa, karin maganar nan ta Malam Bahaushe da ke cewa, da na gaba akan ga zurfin ruwa, lallai gaskiya ce. Don haka, ya zama dole ku rika gudanar da al’amuranku bisa dacewar mutunci da dabi’a. Da haka mabiya za su yi koyi da ku, su ma su zama nagargaru, wadanda za su jagoranci na bayansu su ma.
Amfanin wannan dai na da yawa, abin da aka fuskanta dai guda daya ne, wato muradin samun ingantattar rayuwa mai fa’ida; rayuwa wacce za ta zama mai amfanin kowa da kowa. Idan kuwa aka samu karkatattun shugabanni a cikin al’umma, to babu shakka babu abin da zai hana a samu karkatattun mabiya. Haka kuma idan an samu shugabnni da manya masu kirki, masu sanin ya kamata, masu kishin kasa, to tabbas al’umma za ta kasance mai fa’ida, mai da’a ke nan. Da haka ne za a samu ci gaba a kowane fanni na rayuwa. Idan haka ta samu kuwa, sai mu ce san barka! Allah Ya sanya mu kasance kyakkyawar al’umma, mai ji da da’a da kishin kasa, amin!