Al’amuran ’Yan Shi’a: Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari
Ranka ya dade, ina taya ka murna bisa nasarar da Allah Ya ba ka, wacce tun da dadewa ka cancance ta. Allah ne ke bayarwa kuma Shi ne ke amshewa, har ma da mulki. To ga shi dai Ya ba ka mulki, don haka muna addu’ar Ya yi maka jagora a wannan gagarumin aiki na […]
Ranka ya dade, ina taya ka murna bisa nasarar da Allah Ya ba ka, wacce tun da dadewa ka cancance ta. Allah ne ke bayarwa kuma Shi ne ke amshewa, har ma da mulki. To ga shi dai Ya ba ka mulki, don haka muna addu’ar Ya yi maka jagora a wannan gagarumin aiki na dawo da martabar Najeriya da ka sanya a gaba.
A daidai lokacin da kake amsar ragamar mulki, lokacin ne kura ke neman lafawa, domin kuwa ’yan Boko Haram sun fara tserewa. Tsawon shekara shida ke nan mutanen nan suna yankan kauna da ta’addanci a kasar nan, musamman a Arewacin Najeriya. An kashe dubban mutane cikin ruwan sanyi, an daidaita dubbai, aka raba su da muhallansu. Haka kuma an sace dubban mata da matasa da yara maza da mata ana garkuwa da su. Talakawan Najeriya ba su iya gane kullin da ke cikin Boko Haram, ba su iya tantance wadanda ke daukar nauyin ta’addancinsu ba, musamman saboda yanayin mutanen da tu’annatinsu yake shafa, wadanda suka fito daga sassa daban-daban na al’ummomin Najeriya. An yi ta kawo hasashe daban-daban bisa wannan, amma dai wasu idan ma ka ji, abin dariya ne kawai. Akwai wadanda suka yi amanna cewa wasu dattawa ne ’yan Arewa suka kirkiri Boko Haram, domin su haddasa wa Jonathan ‘cikas a mulki.’ Wasu kuwa suna ganin cewa wai kabilar Ibo ce ke kokarin daukar fansa kan abin da ’yan Arewa suka yi musu a yayin Yakin Basasa. Wasu ma sun ce kai Buhari ne Boko Haram, wasu kuma suka ce Jonathan ne. Ba wadannan ne kadai hasashen da ake faman yi ba, akwai ma wasu da dama.
Abin lura a nan shi ne, wadannan hasashe, kodai gaskiya ne ko akasin haka, abu ne sananne cewa mambobin kungiyar Boko Haram ko Jama’atu Ahlis Sunnah Lidda’awati wal Jihad, kamar yadda suke kiran kansu, mabiya ne ga Muhammad Yusuf. Ya rayu ne a Maiduguri kuma a nan ya rika gudanar da wa’azinsa, har zuwa lokacin da ya gamu da ajalinsa a hannun ’yan sandan Najeriya a shekarar 2009. Babban abin da ya haddasa takun-saka a tsakanin mabiyansa da jami’an tsaro shi ne, kiyawarsu ga bin dokar hanya mai sauki, kamar sanya hular kwano a lokacin tuka babur.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, musabbabin rubuto maka wannan wasika ba don Boko Haram ba ne, wani abu ne da na hango wanda ya fi Boko Haram muni da hadari. Wannan wata kungiya ce da ta kafa rassanta a kowane lungu na al’ummar Musulmin Najeriya. Za ka samu mambobin wannan kungiya a ma’aikatun gwamnati, akwai su a harkokin kasuwanci. Haka kuma sun yi hikimar kutsa kansu, har suka samu kusanci ga manyan ’yan siyasar da ba su ankare da akidunsu ba. Wannan kungiya, ita ce ta ’yan Shi’a.
Dukkan Musulmi dai sun san ko mene ne Shi’a, ba su bukatar wani ya sake fadakar da su amma ga wadanda ke da karancin sani, suna son su san ko mene ne Shi’a, zan yi musu takaitaccen bayani. Shi’a dai wata tsohuwar akida ce da ta dade a Musulunci. Bayan wafatin Annabi Muhammadu (SAW), wanda shi ne Manzon Allah kuma shugaban al’umma, Musulunci ya ci gaba da gudana tare da fadada a karkashin jagorancin Khalifofi shiryayyu. A lokacin mulkinsu ne manyan dauloli kamar Siriya da Iran da Irak da Masar da Faladinu suka fada hannun Musulmi.
Sai dai kuma Annabi (SAW) ya kori Yahudawa daga birnin Madina saboda makircinsu, kuma sun ankara da yadda Musulunci ke kara samun daukaka, bayan wafatin Manzon Allah (SAW). Dalili ke nan suka shirya wata makida, inda suka rika daukar nauyin wasu daga cikinsu, suna shiga Musulunci da nufin kawosabani da rikici a tsakanin al’ummar Musulmi. Irin wadannan masu karyar tuba a karkashin jagorancin Abdullahi Ibn Saba’i suka samu nasarar shirya tawaye ga Khalifa Usman bin Affan (RA). Tun daga farko sun fara gano rauninsa ta wasu bangarori, suka ci gaba da zuzuta su ga al’umma. Daga bisani sai suka nemi ya yi murabus daga mulki. Da Khalifa ya ki yin murabus, sai suka kashe shi. Daga nan ne al’ummar Musulmi suka zabi Khalifa Ali (RA), wanda dan uwa ne ga Manzon Allah (SAW), domin ya jagorance su. Daga bisani kuwa sai dai su wadannan ’yan Shi’ati Ali, suka sukurkuta kokarinsa na binciko makasan Khalifa Usman. Daga nan ne suka sanya akidar Shi’a ta zama wani tambari na nuna kauna ga Ali (RA) da wasu danginsa, sannan suka rika nuna kiyayya da gaba ga sauran Khalifofi da sauran sahabban Manzon Allah (SAW), wadanda suka rika kira da cewa munafukai ne.
Farisawan Iran sai suka rungumi wannan akida ta Shi’a, domin sun fahimci cewa hanya ce da za ta ba su damar gurbata addinin da ya wargaza musu daula da al’ada. Bayan nasarar da juyin-juya-halin da malaman Shi’a suka jagoranta a Iran, sai gwamnatin ta kirkiro tsare-tsaren yada akidar zuwa ga sauran kasashen duniyar Musulmi.
A Najeriya, sai suka nada Ibrahim Yakub Zakzaky domin ya tafiyar da shugabancin yada akidar. Ya kuwa fito da hanyoyi masu yawa domin cimma burinsa. A kan haka sai ya rika amfani da matasan Musulmi wadanda ba su san ciwon kansu ba, ya rika yaudararsu da “Jihadi” da batun “Kafa Daular Musulunci” da kuma batun “Canji” da sauransu. Daga farko sai suka rika kiran kansu da ’Yan uwa Musulmi, suna shirya laccoci da zanga-zanga a kai-a kai.
A wani lokacin can baya a shekarun 1980, Zakzaky ya bayyana wa kowa cewa shi ba dan Shi’a ba ne, kungiyarsa ba ta fito ne domin bunkasa akidar Shi’a ba, abin da suke kira gare shi, shi ne tsantsar Musulunci. Sauran hanyoyin da ya rika bi sun kasance irin wadanda ’yan Shi’a suka dade suna bi a tarihi, wadanda suka hada da auren mut’a. ’Yan Shi’a sun halalta wannan aure, inda mutum zai iya auren mace na kayyadajjen lokaci. Mutane da dama ba su fahimci dalilin da ya sanya matasa maza da matan da suka kamata a ce suna makaranta, amma suke tattaki daga birane daban-daban kamar Kano, Gusau da Katsina zuwa Zariya ba. Wannan shi ne sirrin, wato auren mut’a. Kuma har yau babu wani dan Shi’a da yake musanta wannan aure. Abin da kawai suke musantawa shi ne ‘aron farji’ da ake zargin suna yi, wato musayar mata tsakanin abokai.
Akwai abubuwan takaici da yawa a tattare da ’yan Shi’a da akidojinsu amma abin da nake ganin ya kamata gwamnatinka ta kula da shi, shi ne tsagerancinsu da tsaurin ido da suke nuna wa gwamnati da kuma sauran al’umma. A can baya, a shekarar 1990, ’yan Shi’a sun taba zama alakakai ga al’ummar Jihar Kaduna. A wasu lokuta da zarar wani malamin addini ya nuna kuskuren Ibrahim Zakzaky ko na Ayatullahi Khomeini a wa’azinsa, za ka ga an far masa da duka a gidansa, a gaban matarsa da ’ya’yansa. Saboda takaicin wannan akida, ya sanya gwamnatin Kanar Hameed Ali ta fatattaki ’yan Shi’a. A lokacin nan aka kama mafi yawa daga shugabanninsu kuma aka yi musu shari’a. Wannan dalili ne ya sanya suka canja salo na dan lokaci.
Za mu kammala makon gobe