Al’amuran ’Yan Shi’a: Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari (2)

Dokta Abdussamad Umar Jibiya, shugaba ne a daya daga cikin tsangayoyin koyar da injiniyanci a Jami’ar Bayero Kano. Jim kadan da hawan Shugaba Muhammadu Buhari karagar mulki, ya rubuta masa budaddiyar wasika, inda yake rokonsa da ya yi hankali da take-taken ’yan Shi’a. Malamin ya bibiyi tarihi, inda ya warware amsar tambayar da ke cewa, […]

Al’amuran ’Yan Shi’a: Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari (2)
Al’amuran ’Yan Shi’a: Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari (2)

Dokta Abdussamad Umar Jibiya, shugaba ne a daya daga cikin tsangayoyin koyar da injiniyanci a Jami’ar Bayero Kano. Jim kadan da hawan Shugaba Muhammadu Buhari karagar mulki, ya rubuta masa budaddiyar wasika, inda yake rokonsa da ya yi hankali da take-taken ’yan Shi’a. Malamin ya bibiyi tarihi, inda ya warware amsar tambayar da ke cewa, shin ko akwai wani hadari da Shi’a za ta iya kawo wa al’ummar Najeriya?

 

Mafi yawan abin da suka kware a aikace-aikacensu sun hada da zanga-zanga a ranakun kudus da na Ashura. A yayin wadannan zanga-zanga, sukan toshe muhimman hanyoyin sufuri a biranen Arewa, inda suke jefa tsoro da barazana ga al’umma da jami’an tsaro, domin ba su ma neman izinin yin haka daga gare su. A bara ma, a yayin irin wannan zanga-zanga suka yi arangama da sojoji, inda ta haddasa mutuwar mutane da yawa ciki kuwa har da ’ya’yan Zakzaky guda uku. Haka kuma a duk shekara, sukan shirya abin da suke kira da ‘tattaki’ zuwa Zariya. Suka yi tattakin ne cikin kwambar mutane, inda suke tasowa daga mikatai daban-daban domin zuwa ganawa da shugabansu na Zariya. A yayin wannan tattakin, sukan rufe manyan hanyoyin safara, inda suke haddasa kunci da wahala, sannan su rika takalar matafiya, domin neman tada husuma; al’amarin da jami’an tsaro ke nuna ko-in-kula da shi.
Kamar dai ’yan Boko Haram, su ma ’yan Shi’a ba su daraja doka da oda komai kankantarsu. Misali, bayan bama-bamai da aka yi ta tayarwa a birnin Kano, mahukunta a jihar sun haramta yin goyo a babur ko amfani da shi bayan karfe shida na yamma. Al’umma sun kiyaye wannan doka, ayayin da aka rika hukunta masu kunnen kashi. kungiyar da ta fito karara ta abauce wa wannan doka, ita ce Shi’a. Har zuwa lokacin da dokar ke ganiyarta, za ka ga ’yan Shi’a suna goyo a babura, wani lokaci ma suna goya mutum sama da daya a babur amma abin mamaki, babu daya daga mambansu da aka taba kamawa.
Wani abokina ya taba tambayar wani dan sanda, cewa me ya sanya ba su kama ’yan Shi’a idan sun karya doka? Sai ya amsa masa da cewa: “Ai su ’yan kungiya ne.” Babu shakka ’yan sanda suna jin tsoron haddasa wani tashin hankali ne, amma duk da haka rashin daukar matakin doka a kansu na nuna cewa lallai wasu mutanen sun fi karfin doka.
’Yan Shi’a suna da uwa a gindin murhu, kasancewar shugabanninsu, har da Ibrahim Zakzaky sun yi karatun zamani mai zurfi na jami’a; domin haka abu ne mai sauki yadda suka samu mafaka a wurare masu maiko a kasar nan. Duk da cewa a fili suna nuna adawa da tsarin mulkin Najeriya kuma suna kaurace wa shiga al’amuran siyasa, amma biri ya yi kama da mutum cewa, suna da alaka da wasu ’yan siyasa da suke tallafa musu. Misali, akwai wani tsohon Gwamnan farar hula a Arewa da ya riga ba wani kamfanin gine-gine mallakar wani dan Shi’a kwangiloli. An yin zargin cewa daga ribar da kamfanin ya rika samu ne aka rika daukar dawainiyar wasu aikace-aikacen kungiyar, dadi kuma da abin da suke samu na tallafi daga kasar Iran da kuma wasu attajirai. A zahiri, yin haka ba laifi ba ne tunda su ma ai ’yan kasa ne, amma kasancewar wasunsu an kore su ne daga aiki saboda tayar da zaune-tsaye, ya kamata a ce wannan tsohon Gwamna bai tallafa musu ba.
Malam Ibrahim Zakzaky yana rayuwa ce irin ta hamshakan attajirai, a yayin da mafi yawan mabiyansa suke rayuwa cikin bakin talauci. Haka kuma, duk inda za ya je, za ka same shi da rakiyar masu gadi da sauransu. Za ka same su  suna wasa da makamai iri-iri, inda suke uzzura wa mazauna unguwa ko wadanda suka ziyarci unguwar. An sha kai koke ga ’yan sanda da masarautar Zazzau, amma babu wani matakin hana haka da hukuma take dauka, domin ceto al’umma daga wulakancin. Ko a kwanakin baya ma, an samu rahoton rigimar da ta barke tsakanin ’yan banga da ’yan Shi’a a Unguwar Gyallesu, al’amarin da ya haddasa mutuwar wasu mutane. Amma duk da haka babu wani mataki da gwamnati ta dauka.
Ya Mai girma Shugaban kasa, ga wasu ’yan shawarwari da zan ba ka: Matukar dai da gaske kana son magance barazanar da rashin tsaro ke haifarwa, lallai ya zama tilas ka kawo karshen rayuwar kungiyar Shi’a a kasar nan. Hanyar da za ka yi haka ita ce, ka tabbata babu wani mamba na kungiyar da ya samu matsayi mai muhimmanci a gwamnatinka. Abin ba zai yi dadi ba ko kadan, idan al’ummar kasa suka fahimci cewa akwai wani dan Shi’a da ke rike da wani muhimmin mukami a gwamnatinka, komai girman iliminsa kuwa. Mutane za su yi mamaki su ga cewa shin wane mataki za ka dauka idan aka samu rikici tsakanin jami’an tsaro da ’yan Shi’a, musamman idan aka yi la’akari da cewa akwai wani jami’in da ke kusa da kai kuma dan Shi’a ne. Kuma ya kamata ka san cewa, cikin miliyoyin da suka zabe ka, babu dan Shi’a ko daya, domin ba su yin zabe. Sai dai in ko don su yi takiyya (irin munafuncin nan da ’yan shi’a ke yi, a zahiri su nuna wani abu amma a zuciya ba haka suke nufi ba). Na biyu kada a sake a yarda wani mutum, kamar dan siyasa, sarki ko malami da ya kamata a bari ya yi amfani da jama’arsa ya ce zai tada hargitsi ko ya ci zarafin jama’a. Idan har Malam Zakzaky ko wani mutum yana bukatar masu tsaro a tare da shi, to kamata ya yi ya dauki hayar kwararru da doka ta amince, wadanda ba za su uzzura wa makwabta ko al’ummar gari ba. Daga karshe, ya kamata duk kungiyar da ta tayar da rikici, a hukunta ta bisa doka ba tare da sani ko sabo ba kuma ba tare da nuna bambanci ba.
Ina ma a ce zan iya ganawa da kai ido-da-ido, da na bayyana maka wadannan shawarwari ga-da-ga, ba tare da na yi kwakwazo a bainar jama’a haka ba. Duk da cewa na san wasu kalilan mutane da ke kusa da kai, amma ba ni da tabbacin cewa sakon zai iya isa wurinka cikin sauri idan na biyo ta hannunsu. Kuma na san cewa a yanzu da wasu ’yan Najeriya ke ta turo takardun neman mukamai, babu mamaki idan na turo sakon nan a yi zaton kila na neman mukami ne a kaikaice.
Allah Ya tsare ka, Ya yi maka jagora! Mun kammala