Alan Hattel: Mutumin da ya mallaki kabarinsa kafin ya rasu

Wani mutumin yankin Scotland da ke Birtaniya mai suna Alan Hattel ya razana jama’a da dama bayan ya zabi kabarinsa a makabartar da aka binne matarsa, duk da yana raye cikin koshin lafiya. Alan Hattel, ya yanke wannan hukunci ne sakamakon cewa babu wanda ya kira shi a wayar salula da nufin nemansa har na […]

Alan Hattel: Mutumin da ya mallaki kabarinsa kafin ya rasu

Wani mutumin yankin Scotland da ke Birtaniya mai suna Alan Hattel ya razana jama’a da dama bayan ya zabi kabarinsa a makabartar da aka binne matarsa, duk da yana raye cikin koshin lafiya.

Alan Hattel, ya yanke wannan hukunci ne sakamakon cewa babu wanda ya kira shi a wayar salula da nufin nemansa har na tsawon wata uku zuwa hudu sannan bai san dalilin yin haka ba.

A cewarsa jama’a na zaton ya rasu ne, sannan suna son sanin gaskiyar abin da ke faruwa. Amma ya zargi matarsa da ta rasu saboda rubuta sunansa a jikin wani dutse da aka gindaya a kabarinta.

Alan, mai shekara 75 wanda ya yi ritaya daga aikin walda a Karamar Hukumar Forfar, a yankin Tayside da ke Scotland a Birtaniya ya ce: “Wayar salulata ba ta nuna alamar kira ba daga wata uku zuwa hudu. Na shiga cikin wani yanayi, na san dalilin da ya sa ba wanda ke nemana. Ba na bukatar a binne ni – don haka na shirya kamar an binne ni a cikin kabari.”

Alan, ya tabbatar da cewa yana raye, bayan ya tsaya a kusa da dutsen da ake gindawa a kan kabari. Ya ce, an watsa rahoton mutuwarsa kamar wani abu na zahiri.

Mista Hattel, ya fahimci rahoton mutuwar Alan ba da gaske ba ce, saboda kawai rashin kasancewarsa a cikin kafafen sadarwa na zamani sama da wata uku zuwa hudu.

Wannan dutse shi ne irin wanda ake gindayawa a makabartar Newmonthill a garin Forfar, ya ce wannan abin da Alan ya aikata ya yi ne ba a cikin hayyacinsa ba, abu ne da wanda ba su cikin hankalinsu za su iya aikatawa.

Mista Hattel, ya tattauna da jami’an yankin Angus da kuma shirinsa na rubuta sunansa a jikin dutsen da ake gindaya wa gawar da aka binne ta. Alan, mai kimanin shekara 75 ya yi shekara 37 yana aikin walda kafin daga bisani ya yi ritaya, ya yi zargin cewa tsohuwar matarsa ce ta sayi fili ta rubuta sunan mijinta a jikin duten da nufin idan sun mutu a binne su a wuri guda, sunayensu sun fito karara a jikin dutsen kabarin.

“Ban taba cewa, ina son a binne ni tare da  matata ba,’ in ji Alan.

Sun haifi ’ya’ya biyu tare da matar. Sannan sun rabu kimanin shekara 26 da suka wuce. Sannan rubuta sunan mutum kafin ya mutu a jikin dutsen da ake sawa a gawa, abu ne da har yau ake yi.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato