Albarkar Kirsimeti (3)

Ya ce wa macen, zan yawaita bakin-cikinki kwarai da juna biyunki; da bakin ciki za ki haifi ’ya’ya; nufinki kuma zai komo wurin mijinki, za shi kuwa shugabance ki. Kuma ya ce wa Adamu, don ka lura da muryar matarka, har ka ci kuma daga cikin itacen, wanda na dokace ka, cewa, ba za ka […]

Albarkar Kirsimeti (3)
Albarkar Kirsimeti (3)

Ya ce wa macen, zan yawaita bakin-cikinki kwarai da juna biyunki; da bakin ciki za ki haifi ’ya’ya; nufinki kuma zai komo wurin mijinki, za shi kuwa shugabance ki. Kuma ya ce wa Adamu, don ka lura da muryar matarka, har ka ci kuma daga cikin itacen, wanda na dokace ka, cewa, ba za ka ci ba; saboda kai an la’anta kasa; da wahala za ka ci daga cikinta duk muddar ranka; kayayuwa da sarkakiya za su haifa maka; ganyen saura kuma za ka ci; sai da jibi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma kasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turbaya ce kai, ga turbaya kuma za ka koma. Mutumin kuma ya kira sunan matatasa Hawa’u; domin ita uwar masu rai duka ce. Ubangiji Allah kuma Ya yi wa Adamu da matatasa taggogi na fata, ya suturta su. Kuma Ubangiji Allah Ya ce, ga shi mutumin ya zama kamar daya daga cikinmu, mai sanin nagarta da mugunta; yanzu fa, kada ya mika hannunsa ya dauka kuma daga itace na rai, ya ci, ya yi rai har abada; Ubangiji Allah fa Ya fishe shi daga gonar Adnin, shi nomi kasa inda aka dauke shi. Ya fa kore mutumin; a gabashin gonar Adnin kuma Ya sanya Cerubim da takobi mai harshen wuta mai juyawa a kowace fuska, domin a tsare hanyar itace na rai.”
Idan muka lura sosai, za mu ga cewa mutum ya rasa wurin da Allah Ya shirya masa domin rashin biyayyarsa, Allah Ya rigaya Ya gaya masa cewa a ranar da ya ci daga cikin ’ya’yan itacen nan; to babu shakka zai mutu, mutuwar nan ba lallai wai gangan jinkinsa zai fadi a wurin matacce ba ne, a’a, amma duk lokacin da Allah Ya bar mutum karan-kansa, to gaskiyar ita ce mutumin ba ya da rai. Mu tuna fa cewa tushen ranmu Allah ne, to idan Allah Ya bar mutum, me zai faru? Mutuwa. Ainihin dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya ke nan, ya ceci mutum daga bautar zunubi kuma ya kawo shi a wurinsa inda dama ya kamata ya kasance. Yesu Kiristi ya shigo cikin wannan duniya da niyya guda daya ce kawai – CETON dAN ADAM DAGA ZUNUBI.
Mun ga yadda zunubi ya shigo duniya wanda ya sa mutum ya rasa matsayinsa a gaban Allah, mutum ya rasa matsayinsa na shugabanci bisa dukan halittar Allah. Amma mun gane kuma wannan ba shi ba ne shirin Allah domin mutum, shi ya sa Allah Ya yi shiri domin ya ceci mutum. Abu daya wanda ya bambamta Kirista da duk sauran addinai shi ne – yayin da duk sauran addinai, mutum ne yake kokarin neman hanyar da zai nemi ya samu Allah, Kirista kuwa Allah ne Ya zo neman mutum. Mutum ba zai iya ceton kansa ba daga bautar zunubi; shi ya sa Allah Ya yi shirin zuwa domin Ya ceci mutum. A cikin Littafin Matta:1:18 – 25 za mu sake ganin tarihin haihuwar Yesu Kiristi a cikin wannan duniya kamar haka:- “Haihuwar Yesu Kiristi haka take: sa’anda aka yi tashi tsakanin uwatasa Maryamu da Yusufu, tun ba su gamu ba, aka iske tana da juna biyu daga wurin Ruhu Mai tsarki. Yusufu mijinta kuwa, domin shi mai adalci ne, ba ya so ya nuna ta a sarari, ya yi nufi ya sake ta daga boye. Amma tun yana cikin tunanin wadannan al’amura, sai ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin mafarki, ya ce, Yusufu dan Dawuda, kada ka ji tsoro ka auro Maryamu matarka, gama abin da ke juna biyu a cikinta daga wurin Ruhu Mai tsarki ne. Za ta haifi da; kuma za ka kira sunansa Yesu; gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu. Dukan wannan fa ya zama domin a cika abin da Ubangiji Ya fadi ta bakin Annabi, cewa, Duba, budurwa za ta yi juna biyu, za ta haifi da, za a kira sunansa Immanuel; wato, Allah tare da mu. Yusufu ya tashi daga barcinsa, ya yi kamar yadda mala’ikan Ubangiji ya umurce shi, ya dauko matatasa; amma ba ya san ta ba har ta haifi da; ya kuwa kira sunansa Yesu.”
Daga cikin wannan dan gajeren tarihin; za mu iya tsintar abubuwa kadan da za su taimaki ganewarmu game da niyyar zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya. Tun daga ma’anar sunansa, za mu ga cewa yana tattare da dalilin da zai shigo duniya: sunan nan – YESU ne; sai a ci gaba da ba da bayani cewa gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu. Gaskaiyar ita ce babu wani irin labari da ya fi wannan dadi cikin dukan duniya; cewa Allah da kanSa Ya yi shiri domin Ya ciro mutum daga cikin bautar Shaidan da kuma zunubi, cewa ta wurin Yesu Kiristi, dukan wanda yake bukatar ceto daga zunubi, Allah Ya rigaya Ya bude kofar samun rai na har abada. Ubangiji bai nufi mutum ya mutu har abada ba, Shi da kansa ya yi shirin dawo da mutum bisa matsayinsa na shugabanci da kuma mulki bisa dukan halitar Allah a cikin wannan duniya.