Albarkar Kirsimeti (4)

Daga cikin wannan dan gajeren tarihin; za mu iya tsintar abubuwa kadan da za su taimaki ganewarmu game da niyyar zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya. Tun daga ma’anar sunansa, za mu ga cewa yana tattare da dalilin da zai shigo duniya: sunan nan – YESU ne; sai a ci gaba da ba da bayani […]

Albarkar Kirsimeti (4)
Albarkar Kirsimeti (4)

Daga cikin wannan dan gajeren tarihin; za mu iya tsintar abubuwa kadan da za su taimaki ganewarmu game da niyyar zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya. Tun daga ma’anar sunansa, za mu ga cewa yana tattare da dalilin da zai shigo duniya: sunan nan – YESU ne; sai a ci gaba da ba da bayani cewa gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu. Gaskaiyar ita ce babu wani irin labari da ya fi wannan dadi cikin dukan duniya; cewa Allah da kanSa Ya yi shiri domin Ya ciro mutum daga cikin bautar Shaidan da kuma zunubi, cewa ta wurin Yesu Kiristi, dukan wanda yake bukatar ceto daga zunubi, Allah Ya rigaya Ya bude kofar samun rai na har abada. Ubangiji bai nufi mutum ya mutu har abada ba, Shi da kansa ya yi shirin dawo da mutum bisa matsayinsa na shugabanci da kuma mulki bisa dukan halitar Allah a cikin wannan duniya.
Yesu Kiristi kalmar Allah ne; a cikin littafin Yohanna sura daya daga aya daya zuwa aya biyar; maganar Allah na cewa “A cikin farko akwai Kalma; Kalmar kuwa tare da Allah ne, Kalmar kuwa Allah ne. Wannan a cikin farko tare da Allah yake, ta wurinsa aka yi dukan abu; ba a yi komi cikin abin da an yi, sai ta wurinsa. A cikinsa akwai rai, rai kuwa hasken mutane ne, Kuma hasken yana haskakawa a cikin duhu; duhu kuwa ba ya rinjaye shi ba.” Yesu Kiristi Kalmar Allah ne. Mutane da yawa sukan yi tambayoyi daban-daban musamman ma idan sun ji an ce Yesu Kiristi dan Allah ne, ina so mu sake duba binciken da muka rigaya muka yi mako biyu da suka gabata, za mu ga cewa Allah ne da kanSa Ya aiko mala’ika Jibraila da sakon zuwa ga Maryamu. Wannan sakon daga wurin Allah ne da kanSa, mu dauka misali Maryamu ta ki karbar wannan sakon, me muke ganin mala’ikan zai yi? Mala’ikan nan ba zai yarda da wannan sakon dan ba, zai koma ne ga shi wanda ya aiko shi; ya ce masa wadda ka aike ni zuwa wurinta fa, ta ki ta karbi wannan sakon. Yawancin mutane sun san cewa Yesu Kalmar Allah ne kuma Ruhun Allah ne; amma idan ya zo ga gane yadda ya zama dan Allah sai ya zama musu da damuwa; wani lokaci sukan yi tambaya yaya za a ce Allah Madaukakin Sarki Yana da da? Abin da yake kawo wa mutane irin wannan rudanin shi ne; mutum yana gani kamar zai iya kimanta ikon da Allah Yake da shi a cikin tunaninsa na mutuntaka. Ikon Allah ya fi gaban misalin mutum. Ikon Allah ya fi gaban hikimar dan Adam. Ba wani mutum da zai iya kwatanta irin ikonSa. Shi ne Mai iko duka. Komi wadda ya ga damar yi; zai yi ne ba zai karbi izni daga wurin kowa ba. Idan ya ga dama zai iya sa kalmarsa ta zama duk abin da Yake so; kuma haka din ne ya yi sa’anda Ya aiko mala’ika Jibraila zuwa ga Maryamu da wancan sakon. Damuwar ita ce; a cikin tunaninmu na mutane, babu yadda mace za ta yi juna biyu ba tare da sanin namiji ba, to amma abin lura a nan shi ne Allah ba mutum ba ne; shi Allah ne Mai komi Mai kowa, zai zama babban kuskure ne ga kowa ya yi tsammani Allah ba Ya da iko Ya sa kalmarSa a cikin budurwa; wannan Kalma kuma ya girma haka kawai ba tare da wani ya yi jima’i da ita ba, wannan a wurin Allah ba abu mai wuya ba ne ko kadan. Kada ka shiga kuskuren ‘yi wa Allah tunani.’
Kirsimeti, hasken Allah ne ya shigo duniya, kuma hasken yana haskakawa a cikin duhu; duhu kuwa ba ya rinjaye shi ba. Wannan shi ne RAI wanda Yesu Kiristi ya kawo. Idan mun tuna; a cikin bincikenmu da ya gabata, mun ga yadda mutum ya rasa gadon da Allah Ya ba shi a cikin gonar Adnin domin rashin biyayyarsa; kuma ta sanadiyar rashin bin umarnin Allah da suka yi, Allah sai Ya bar su, wannan ita ce mutuwa wadda ta fi muni, wato rabuwa da Allah: mutuwa cikin ruhu ke nan. Ubangiji Allah bai ji dadin abin da Adamu da Hawwa’u suka yi ba, amma duk da haka bai bar su, su halaka ba, Shi ne Ya nemi hanyar da zai ceci mutum daga cikin wannan bautar zunubi. Babu wani aiki mai kyau da mutum zai iya yi domin ya gamshi Allah idan ba ta wurin hanyar da Shi Allah da kanSa Ya shirya a cikin Yesu Kiristi ba. Kirisimeti; lokacin murna ne kwarai da gaske domin ’yancin da wanda yarda da wannan shirin Allah zai samu daga karkashin bautar Shaidan da zunubi. Shin; mene ne ya kamata ka yi da Yesu Kiristi? Kirisimeti ba lokacin lalata ba ne da aikata abubuwan da ba za su gamshi Allah ba, kamar yadda wasu ke yi, amma lokaci ne na godiya ga Allah domin jinkanSa da kuma alherinsa zuwa ga dukkan mutane. Yarda da Yesu Kiristi a cikin zuciyarmu; samun rai ne na har abada, kin yarda da Yesu Kiristi cikin zuciyarmu kuma halaka ne na har abada. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.