Albarkar Ruhu (1)
kaunaA wannan makon da yardarm Ubangiji za mu yi bincike ne a kan albakar Ruhu Mai tsarki ga mu bayinSa. Mene ne albarkar Ruhu Mai tsarki? Bari mu duba cikin littafin Galatiyawa 5:22,23: “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da […]
kauna
A wannan makon da yardarm Ubangiji za mu yi bincike ne a kan albakar Ruhu Mai tsarki ga mu bayinSa. Mene ne albarkar Ruhu Mai tsarki? Bari mu duba cikin littafin Galatiyawa 5:22,23: “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.” Da farko dai idan muka lura a nan za mu ga cewa Albarkar Ruhu (a zaman abu guda) kamar yadda muka gani a karatunmu: Albarkar Ruhu kuwa ita ce…mai makon a ce albarkokin Ruhu, ita kanta albarka suna ne na (jam’i). Dalili kuwa shi ne albarka guda daya ce amma takan samu bayyanuwa ta hanyoyi daban-daban. A takaice Manzo Bulus ya fara da “kauna,” me ya sa kauna? Domin kauna ke haifar da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kamun kai. A wasikarsa (Manzo Bulus) zuwa ga Ikilisiyoyin kasar Galatiya za mu ga cewa ya gargade su cewa kada su biye wa halin mutuntaka amma su yi rayuwa da zama cikin Ruhu Mai tsarki, shi ya sa ya ambaci kauna da abubuwan da take haifarwa domin jagorantar ikilisiya. Har wa yau wannan koyarwa na da muhimmanci ga Ikilisiyarmu don mu girma cikin rayuwarmu ta ruhaniya.
Idan muka sa hankali za mu ga cewa Manzo Bulus ya ambaci abubuwa guda tara, amma a takaice suna zaman abu guda, wato kauna, domin kauna ke haifar da dukan sauran albarkokin kamar yadda muka fadi da farko. Domin kauna ta fi muhimmanci ga rayuwarmu, shi ya sa Manzo Bulus ya fara da kauna. Bari mu ga yadda ya bayyana kauna a cikin Littafin1 Korantiyawa 13; Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala’iku, amma ya zamana ba ni da kauna, na zama kararrawa mai yawan kara ke nan, ko kuwa kuge mai amo. Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matukar ban-gaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da kauna, to, ni ba komai ba ne. Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a kone, in har ba ni da kauna, to, ban amfana da komai ba. kauna tana sa haƙuri da kirki. kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko. kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. kauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da ban-gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali da juriya a cikin kowane hali. kauna ba ta karewa har abada. Annabci zai shude, harsuna za su bace, ilimi kuma zai shafe… To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, ban-gaskiya da bege da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.” Kana da kauna a cikin zuciyarka, ko a baki kadai kake fadi? kauna fa ita ce babba.Yesu Almasihu da kansa ya ce mu nuna kauna ga kowa har ma ga magabtanmu a cikin Littafin Matiyu 5:43-45: 43; “Kun dai ji an fada, ‘Ka so dan uwanka, ka ki magabcinka.’Amma ni ina gaya muku, ku kaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda Yake cikin sama. Domin Yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, Ya kuma sauko ruwanSa ga masu adalci da marasa adalci.” Ubangiji Allah bai nuna bambanci ba wurin nuna mana kaunarSa kamar yadda muka karanta, Ya ba mu rai da jiki da bukatunmu na yau da kullum, bai bambanta tsakanin fari ko bakin mutum ba, ko kabila da addini ba, Ya dauke mu a zaman bayinSa, halittarSa kuma, Ya ba mu daraja bisa kowace hallitta a duniya, wannan kadai bai isa mu yi koyi ba?
Bari mu dubi abin da Littafin 1 Yahaya 4: 7,8 ke fadi; “Ya ku kaunatattuna! Sai mu kaunaci juna, domin kauna ta Allah ce. Duk mai kauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.Wanda ba ya kauna, bai san Allah ba sam, domin Allah Shi ne kauna. kauna daga Allah take, idan muna da kauna a cikin zukatanmu za mu ga cewa sauran albarkokin Ruhu za su bayyana a cikin rayuwarmu, domin idan ba ka da kauna a cikin rayuwarka babu yadda za a yi ka zama da farin ciki, babu yadda za a yi ka zama da salama ko kuma hakuri, kirki zai zama da nauyi ainun a rayuwarka, nagarta da aminci ko tawali’u za su yi nesa da kai, ba kuwa za ka zama da kamun kai ba, kuma ka nuna cewa ba ka san Allah ba, domin har idan ka san Shi, za ka bi gurbin abin da yake nuna mana ta wurin ikonSa a kulum.
Wani abin lura kuma a nan shi ne za mu ga cewa wani lokaci muka yi niyyar ka sa cikin rayuwarmu na mutumtaka wajen nuna wadannan albarkoki, mukan iya zama da kauna amma sai ka ga muna da karancin nuna hakuri, ko kamun kai da sauransu. To me ya kamata mu yi a irin wannan yanayi? Ya kamata mu girma cikin ruhaniya ta wurin yin nazari a cikin Littafi Mai tsarki, mu bincika mu ga me Ubangiji Allah Yake so mu yi cikin rayuwarmu, mu kuma yi koyi da abubuwan da ke cikin Littafi Maitsarki, mu kuma bi gurbinYesu Almasihu domin shi ne hanya, shi ne gaskiya, shi ne kuma rai. Kowane wayewar gari mu roki Ubangiji Allah Ya ba mu albarkokin ruhunSa mu kuma bude kofar zuciyarmu ga nufinSa, ta wurin yin haka kuwa babu shakka za mu samu nasara kuma ta wurin yin haka ne za mu nuna hasken Almasihu ga dukan duniya a zamanmu na Kirista.
Mako mai zuwa da yardarm Ubangiji za mu ci gaba da karin bayyani a kan Albarkar Ruhu.
Bari kaunar Yesu Kiristi da Zumuntar Ruhu Mai tsarki su kasance tare da mu daga yanzu da har abada, amin.