Albarkar Ruhu (2)

Farin cikiDa yardar Ubangiji a wannan makon za mu ci gaba da bincikenmu na sanin Albarkar Ruhu mai tsarki cikin rayuwarmu. Bari mu sake dubawa cikin Littafin Galatiyawa don samun tushen bincikenmu. Littafi Mai tsarki na cewa; “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da […]

Albarkar Ruhu (2)
Albarkar Ruhu (2)

Farin ciki
Da yardar Ubangiji a wannan makon za mu ci gaba da bincikenmu na sanin Albarkar Ruhu mai tsarki cikin rayuwarmu. Bari mu sake dubawa cikin Littafin Galatiyawa don samun tushen bincikenmu. Littafi Mai tsarki na cewa; “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su” (Galatiyawa:5:22,23).
Da irin halin da muka tarar da kanmu a ciki na tashe-tashen hankula da muke fuskanta dare da rana a zamanin da muke ciki a yau (wato karshe zamani), sai ka ji an sace wannan an kashe wancan, an kone muhali ko masujadai a nan, an kai hare-haren bam a can, ana yaki a nan da can da dai makamantansu, sai ka ga cewa mutane da dama  na cikin matukar bacin rai maimakon farin ciki, yakan zama da zafi, kuma abin bacin rai ne matuka idan muka fada cikin irin wannan hali. To, mene ne ke kawo irin wannan yanayi? Rashin kauna. Duk inda ana zama cikin kaunar Ubangiji, babu shakka nan za ka samu farin ciki, inda kuma babu kauna, sai a tarar da bakin ciki.
Bari mu zo cikin kasarmu Najeriya, idan kana tafiya a kan titi ko ka shiga cikin kasuwa ko motar haya, ko naka abin hawan, za ka ga cewa yawancin mutane na saurin fushi, saurin zagi har ma fada, domin wani abin da bai kai ya kawo ba. Mutane yanzu na da rashin hakuri, ba kaunar juna sai dai son kai, idan kana bin layi a banki ko gidan mai, za ka ga wani ya zo ya shige gabanka yana kokarin biyan nasa bukatar bai damu da kowa ba. Me ke kawo irin wannan halin? Rasin kauna. Irin wannan hali kuwa yakan kawo bacin rai, sai ka ga an wayi gari kowa yana cike da fushi ba bakin ciki a cikin harkokin yau da kullum. Shi ya sa Littafi Mai tsarki ke koya mana cewa mu zama mutane masu kaunar juna, cike da albarkar ruhu mai tsarki, ta wurin yin haka kuwa za mu ci nasara bisa halin mutuntaka- “Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato fasikanci da aikin lalata da fajirci da bautar gumaka da sihiri, da gaba da jayayya da kishi da fushi da son kai da tsaguwa da hamayya da hassada da buguwa da shashanci da kuma sauran irinsu. Ina fadakar da ku kamar yadda na facakar da ku a da, cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su samu gado a Mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5: 19-21).
Abin nazari a nan shi ne kada ka ga cewa ai wani ne ke bata maka rai har ya kai ka ga yin fushi, ya zamanto ba ka da farin ciki a cikin rayuwarka, ba haka Ubangiji Allah Yake so mu zama ba, Yana so mu zamo masu kauna da nuna farin ciki a koyaushe, musamman ga magabtanmu ko masu bata mana rai. Kada mu zama masu saurin yin fushi (muna iya nuna fushinmu ga ayukan jiki ko halin mutuntaka kamar yadda muka karanta a Galatiyawa 5: 19-21, domin irin wadannan ayyukan masu ban kyama ne a gaban Ubangiji Allah), amma sai dai mu zamo masu nuna kauna da farin ciki ga mutane, ta wurin yin haka kuwa za ka ga cewa mai irin wannan mugun halin zai sa hankali ya kuma dauki darasi da irin wannan kyakkyawan hali na kauna har ya kubuta daga irin wannan mugun hali.
Kada mu karaya da yanayin da muka samu kanmu a ciki na rashin zaman lafiya a kowane bangare na kasarmu ko kuwa duniya baki daya, mu kaunaci Ubangiji Allah, mu nuna kaunarSa ga makwabtanmu. “Sai ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka da dukkan ranka da dukkan hankalinka da kuma dukkan karfinka.”  Mabiyinsa shi ne, “Ka kaunaci dan uwanka kamar kanka.” Ba fa sauran wani umarni da ya fi wadannan girma.” (Markus: 12: 30,31). Ta wurin yin haka ne za mu samu cikakken farin ciki a rayuwarmu.
Farin ciki abu ne da kowa ke marmarin samu, idan ka ga iyali ko kungiya da ba ta da farin ciki a cikinta,babu shakka akwai karancin kauna a nan, domin kauna tana sa hakuri da kirki, kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura, kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo, kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya, kauna tana sa daurewa a cikin kowane hali da ban-gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali da juriya a cikin kowane hali. kauna ba ta karewa har abada. (1 Korantiyawa 13: 4-8a).
Ashe rashin kauna shi ne tushen rashin zaman lafiya da farin ciki domin ai son kai da rikon wani a zuci da rashin hakuri da zalunci da daga kai da yin mugunta da makamantansu, ba sa samar da farin ciki sai wahala da za ta kai mutum ga hallaka. Don haka sai mu lura mu yi kokarin bin abin da Ubangiji Allah ke bida a gare mu bayinSa, wato mu zamo mutanen kirki. Karin Magana 10:28;  “Abin da mutanen kirki suke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai.”
Idan ka ga cewa kana bukatar farin ciki a rayuwarka ko iyalinka, sai ka sani fa cewa farin ciki daga wurin Ubangiji ake samunsa, kauna kuwa ita ce tushen irin wannan rayuwa, bin tafarkin Ubangiji da yin addu’a kuma zai ba mu nasara cikin irin rayuwar da muke fuskanta a zamanin da muke ciki. Manzo Bulus ya karfafa mu a cikin wasikarsa zuwa ga masu bi a Roma cewa; “Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu’a.” (Romawa 12:12) babu shakka idan mun roki Ubangiji Allah ta wurin yin addu’a, zai ba mu albarkar ruhunSa a yalwace don mu yi rayuwa cikin farin ciki da kauna.
 “Allah Mai kawo sa zuciya, Ya cika ku da matukar farin ciki da salama saboda ban-gaskiyarku, domin ku yi matukar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki.”(Romawa 15:13).
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar Ubangiji Allah.