Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?1
Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya? Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka: Dole a ci gaba da hada […]
Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya? Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka:
Dole a ci gaba da hada arzikin kasa ana rabawa -Yunusa Suleiman
Yunusa Suleiman, shugaban makarantar UMRABS: A’a, ai in an yi haka, an yi kwara, domin ai da arzikin da aka samu a Arewa aka gina duk inda ake takama da shi a halin yanzu. Don haka dole ne a ci gaba da hada arzikin kasa ana rabawa, har sai kowa ya gamsu tukunna kafin a daina hadakar arzikin kasa kowa ya koma ya ci gashin kansa.