Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?2
Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya? Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka: Kowane yanki ya rika sarrafa dukiyar […]
Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya? Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka:
Kowane yanki ya rika sarrafa dukiyar da ya tara -Lawal Muhammad
Lawal Muhammad dan Kasuwa a Abuja: Ina ba da shawaran kowane yanki ya rika sarrafa dukiyar da ya tara, na albakatun kasa da Allah Ya huwace masa, sai a ware wani kaso daga dukiyar a matsayin na gwamnatin tarayya don gudanar da ayyukanta. Saboda a tsarin da ake bi a yanzu na tattaro dukiyar kasa zuwa nan Abuja, sannan a kasafta shi, adadi mai yawa na salwanta, sannan kuma na sanya jihohi na zama haka nan ba tare da kirkiro hanyoyin kudin shiga ba da sunan suna jiran babban asusun kasa.