Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?3

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka: A ci gaba da hadawa a […]

Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?3
Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?3

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka:

A ci gaba da hadawa a matakin tarayya, sannan a raba -Alhaji Sa’idu
Alhaji Sa’idu Abubakar Musa, babban mai koyarwa a Kwalejin Ilimi ta Birnin Tarayya da ke Zuba: Ina goyon bayan a ci gaba da hada kudin da aka samu daga ma’adinai, wanda Allah Ya albarkaci kasa da shi a matakin tarayya, sannan a raba shi ga jihohi gwargwadon yawan jama’ar da suke da shi. Wannan shi ne tsarin federeshin da muke amfani da shi, kuma da haka aka fara tun lokacin da aka faro hakar rijoyin mai da ake cin gajiyarsu a yanzu, inda aka yi amfani da kudaden albarkatun noma. Sai dai hanyoyin kudin shiga da jihohi da kananan hukumomi suka kirkiro wa kansu, wannan ba sai an kawo shi asusun kasa ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya