Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?4

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka: Kowane yanki ya rike albarkatunsa, ba […]

Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?4
Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?4

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka:

Kowane yanki ya rike albarkatunsa, ba zai taimake mu ba -Mista Jabin

Mista Jabin Joshua a Lafia: Ka ga abin da ya kamata a ce ’yan Najeriya, musamman talakawa su nema shi ne shugaba nagari. Saboda idan muka fara tunanin kowanne yanki ya rike albarkatunsa, to, ina tabbatar maka mun fara jawo wa kanmu damuwoyi ke nan. Saboda tsoro ma da muke baiwa duniya a matsayinmu na babbar kasar Afirka za mu bar ba da shi. Saboda haka mu talakawa, idan za mu yi wa kanmu adalci, to mu tsaya mu bincika mu gano wane ne shugaba nagari da zai iya yin amfani da wadannan albarkatun yankunanmu yadda ya kamata don inganta rayuwarmu da ta ’ya’yanmu, maimakon mu tsaya muna magana cewa kowanne yanki ya rike albarkatunsa, wanda hakan ba zai taimake mu ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya