Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?5

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka: Kowane yanki ya rike albarkatunsa bai […]

Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?5
Albarkatun kasa: Kowa ya rike nasa ko a hada a raba a tarayya?5

Ana ta cece-kuce dangane da albarkatun kasa. Filin muhawara ya bukaci jin ra’ayoyi kan shin kowane yanki na kasar nan ya rike albarkatunsa ko kuwa a hada, tunda dukiyar kasa ce, sai a raba ta a tarayya?  Ga dai yadda aka sami ra’ayoyin wasu jama’a, a yau, kamar haka:

Kowane yanki ya rike albarkatunsa bai dace ba  -Injiniya Haruna
Injiniya Haruna Sani Abubakar a Lafiya: A nawa ra’ayi dai batun kowanne yanki ya rike albarkatunsa bai dace ba, don yanzu ka ga akwai albarkatun kasa da mu ’yan Arewa muke amfana da su daga Kudu, akwai kuma wadanda su ’yan Kudu ke amfana da su daga nan Arewa. Saboda haka, idan aka ce kowa ya rike nasa, to da mu da su duk za mu samu matsala. Misali ka ga akwai su kayan lambu da na gonaki da dai sauransu da mu a nan Arewa muna da su da ba irinsu a can Kudu. Mu kuma muna amfana da man fetir dinsu da sauransu. Saboda haka ban goyi bayan kowanne yankin kasar nan ya rike albarkatunsa ba. A cigaba da abin da aka saba, don Najeriya daya ce, sai dai idan ana so a raba kasar nan.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya