Albashi: Za a tantance ma’aikatan kananan hukumomi a Nasarawa

Za a tantance m a’aikatan kananan hukumomin Jihar Nasarawa kafin a biya su albashinsu na wasu watanni da suke bi da tallafin kudi da jihar ta samo daga gwamnatin tarayya.&nbsp Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kwamred Abdullahi Abubakar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke […]

Albashi: Za a tantance ma’aikatan kananan hukumomi a Nasarawa
Albashi: Za a tantance ma’aikatan kananan hukumomi a Nasarawa

Za a tantance m a’aikatan kananan hukumomin Jihar Nasarawa kafin a biya su albashinsu na wasu watanni da suke bi da tallafin kudi da jihar ta samo daga gwamnatin tarayya.&nbsp

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kwamred Abdullahi Abubakar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Keffi. Ya ce kungiyar tare da hadin gwiwar kungiyar shgabannin kananan hukumomin jihar sun dauki matakin tantance ma’aikatan kananan hukumomin jihar kafin a biya su albashinsu da tallafin kudin ne don kauce wa ma’aikatan bogi daga cikin tsarin wadanda za a biya.
Acewarsa gwamnatin jihar ta riga ta bai wa kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar cekin kudin tallafin wanda ya kai Naira biliyan 4 da miliyan 3. Ya ce tuni wasu kananan hukumomin jihar suka fara tantance ma’aikatansu don biyansu wasu basussukan albashinsu ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce tantance ma’aikatan ya zame dole idan aka yi la’akari da yadda ake samun matsalar rashin kudi a kananan hukumomin sakamakon ma’aikatan bogi.
Ya bayar da karin haske da cewa za a biya ma’aikatan albashinsu na watanni biyu da rabi ne watau kashi 50 na watan Yuli sai na cikakken albashi na watan Agusta da kuma na Satumban shekarar da muke ciki. Ya ce daga bisani idan aka samu ragowar kudin kaso na jihar daga gwamnatin tarayya za a biya sauran albashin.
Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ganin kudin da ake kasa a halin yanzu ba zai isa a biya dukkan basussukan albashin a lokaci guda ba.
Daga nan sai ya jinjina wa gwamnatin tarayya da na jihar a kokarin da suka yi na ganin an ceto ma’aikatan kananan hukumomin daga halin da suka tsinci kansu a ciki.
Ya yi kira ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jihar baki daya su tabbatar kwalliya ta biya kudin sabulu wajen gudanar da ayukansu cikin gaskiya da rikon amana.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin da ta wuce ne gwamnatin jihar ta bai wa kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar cekin wannan tallafin kudi na Naira biliyan 4 da miliyan 300 da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar a matsayin kudin tallafin gaggawa don a biya ma’aikata basussukan albashin da suke bi.