Albashin N615,000 shi ne abin da ya fi dacewa a Najeriya
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce biyan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi shi ne iya abin da ya fi dacewa na zahiri a ƙasar. Joe Ajaero ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels kan dambarwar ƙarin mafi ƙarancin albashi a Najeriya. “Naira N615,000 shi ne […]
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce biyan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi shi ne iya abin da ya fi dacewa na zahiri a ƙasar.
Joe Ajaero ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels kan dambarwar ƙarin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.
“Naira N615,000 shi ne zahirin abin da ya fi dacewa a matsayin albashi; ba maganar albashi kamar na bayi ba.
“Lissafawa muka yi muka ga abin da zai wadaci ma’aikaci a wannan yanayi na tsadar rayuwa,” in ji shi.
- Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Kai Hari Ofishin ’Yan Sanda a Borno
- An kama barawon wayan da ya caka wa budurwa wuka a Yobe
A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙarin albashi da kashi 25 da kashi 35, ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28 na abin da ake biya a yanzu.
Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta yi watsi da ƙarin da cewa ya yi kaɗan.
Shugaban ƙungiyar ya ce suna samun matsin lamba da ma’aikata a matsayinsu na shugabanni; a daya bangaren kuma gwamnati na zagin su.
Ya ce lissafin da suka yi a kan magadanci mai ’ya’ya hudu a wata guda ya kunshi abubuwa 30, ciki har da wadannan:
- Kudin haya – N40,000
- Wutar lantarki – N20,000
- Ruwa – N10,000
- Gas din girki – N28,000
- Abinci – N240,000
- Asibiti = N50,000
- Makaranta = N50,000
- Kwasan shata = 10,000
- Kudin mota = N90,000