Albashin sojan Nijeriya N50,000 ne —Babban Hafsan Tsaro
N1,200 ne kudin abincin Janar din soja da ke filin yaki a rana guda
Acikin wannan tattaunawar, Babban Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yi karin haske a kan hauhawar matsalar tsaro a Nijeriya da kuma yunkurin yadda za a shawo kan lamarin.
Sannan ya yi bayani kan jin dadi da walwalar sojojin Najeriya da sauran muhimman batutuwa.
Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Na san kalubalen tsaron da kasa ke fama da shi musamman lamarin Jihar Filato da ke kwan-gaba-kwan-baya. A jajiberin Kirsimeti lamarin ya auku a Bokkos, sannan wani ya sake biyo baya a Mangu wanda ake fama da shi a halin yanzu. Me ya sa kowane bangare ke zargin sojoji da sa hannu a rikicin?
- Amarya ta yi wa ango yankan rago a Neja
- Aure nake so —Adam Zango ya lashe amansa
- Sakonni 3 da Sarkin Kano ya tura Remi ta isar wa Tinubu
Idan har ya zama kowane bangare na zargin sojoji hakan na nufin suna tsakiya ke nan ba tare da daukar bangare ba. Mafi muni da illar abin shi ne a ce wani bangare guda daya ne kawai ke ganin sojojin na goyon bayansu.
An horar da sojoji ne da su kasance marasa bangare kuma wannan shi muke yi a yayin gudanar da aiki. Wannan ne ya sa ya kamata mu tanatar, su san aikinmu shi ne tabbatar da samuwar zaman lafiya a duk inda muke.
Kuma kai ma ka san matsalar Jos dadaddiya ce. Rikicinsu na siyasa ne ba na soji ba.
Me ya sa ka ce haka?
To yekuwar me suke yi? Rikicin manoma da makiyaya, ina ce magana ce ta ‘yan gari ko da baki? Wadannan matsala ba sojoji ne za su warware ta ba.
Abin da kawai za mu iya yi shi ne dakatar da kashe-kashe. Shi ma matukar mutane ba su shirya dakatar da shi ba, haka zai ta ci gaba saboda ba za mu iya kasancewa a ko’ina ba.
Amma ka taba tattaunawa da shugabannin siyasar don magance matsalar tunda ka ce matsala ce ta siyasa?
Kwarai kuwa. Kuma mafitar ya kamata ta fito ne ta fuskoki da dama kama daga bangaren Gwamnatin Tarayya ka gangaro zuwa ta jiha sannan na kananan hukumomi, a dukkanin matakan. A maganace ta tattaunawa kuma tana da muhimmanci.
Mu zauna mu fada wa junanmu gaskiya da gaskiya. Mece ce matsalar? Me ya sa ba mu maganace ta? Idan har kana da ciwo kuma kana shan maganin da ya kasa warkar da kai sai ka gane cewa ba shi ne hakikanin maganin da ya dace ka sha ba, daga nan kuma sai ka nemo wani maganin.
Amma tattaunawar zaman lafiya da kake magana a kai an dade ana yi.
Zai iya yiwuwa ke nan ba matsalar ake tunkara ba. Dole ne mu zauna mu tambayi wai shin me ke haddasa wannan matsalar kuma wacce hanya za a bi a yi maganinta?
Matsalar manoma da makiyaya alal misali abu ne mai matukar saukin warwarewa. Ni manomi ne kuma na killace dabbobina sunan nan a makiyaya inda aka tanadar don yin kiwo.
Ni ne farkon shugaban gonaki da gandun kiwo na sojojin Nijeriya. Mun giggina musu wuraren kiwo inda za su ci abinci da wurin da za su sha ruwa a killace. Kai, amma fi samun kudi da su idan aka killace su!
Yanzu kana magana ne game da gidan soja wanda za a ce suna da kudin yin hakan. Ta yaya makiyayin da ya mallaki shanu misali kasa da goma sha biyu da bai mallaki ko da taku daya na fili ba zai yi? Ta yaya kuka iya kaiwa ga hakan?
Dalilin da ya sa na ce maka ke nan. Wannan matsala ce da mafitarta ta siyasa ce. Idan gwamnati na son magance matsalar za mu iya magance ta. Me ya sa na ce haka? Za mu iya giggina musu gandun kiwon ai.
Idan za ka iya tunawa mun yi amfani da harajinmu a kan shanu a 1960s, amma yanzu ba ma yi. Gwamnati za ta iya samar da kudaden da za ta gina musu gandun kiwo da makiyaya da tafkin shan ruwa da za su rika kiwo.
Arewa na da arzikin fili mai fadi. Hakazalika, muna da magudanun ruwa masu yawa. Mu leka irin wadannan wurare gwamnati za ta iya sarrafa wadannan wurare.
Ke nan yanzu kana ganin tabbas muna kuskuren daukar cewa wannan matsala ce da ta kamata sojoji su dauka a kan mutane?
A’a. Sojoji nasu shi ne dakatar da duk wani mai dauke da makami. Kuma yana da kyau ka gane rikici wata dabi’a ce a rayuwar dan Adam.
Yanzu mu kalli abin da ya faru a Jihar Filato. Matsala ce kawai da wani a kan babur ya buge wasu dabbobin da ke kiwo. Yanzu wannan ya isa ya zama sanadin kashe-kashe?
Ai rashin shigo da mafita ne ya haifar da hakan. Wannan shi ne hatsarin.
Ke nan akwai iyaka game da abin da sojoji za su iya yi?
Za mu yi duk iya abin da za mu iya yi, amma dai har yanzu mene ne dalilin duka wadannan tashe-tashen hankulan?
Wannan shi ya sa na ce maka yana da muhimmanci sosai a raba dabbobi da manoma.
Amma kuma lura da yawan jama’a da kuma karancin filaye za a iya cewa wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Shin ba ka tunanin hakan?
A’a. Na fada maka cewa, muna da gandun kiwo a 9RP, kuma akwai dabbobi a wajen. Idan ka je za ka ganewa kanka wata saniya kai za ka dauka Giwa ce saboda ta ci ta koshi.
Ta bayyana kamar babu wata cikakkiyar tuntuba da ganawa da kuke yi da al’ummun Fulani makiyaya saboda kun ga wannan abin fa gadarsa suka yi?
Kamar yadda na fada maka ne, an tattauna kuma an bayar da mafita sannan an kakkafa kwamitoci kusan komai an tattauna shi matsalar kawai ita ce yadda za a aiwatar.
Har yanzu kuna tattauna irin wannan idan kun zauna da shugabannin siyasa a sama?
Eh. Namu bayar da shawara ce kawaiamma ba mu da ikon zartarwa. Mun dai fada musu idan ana son a yi abu kaza to ga mataki iri kaza da ya kamata a dauka a siyasance kuma abu ne mai yiwuwa.
To me ya sa sojoji ba su iya tunkarar lamarin gaba daya ba a jihohin Katsina da Zamfara da Nasarawa da Neja da kuma Birnin Tarayya Abuja ba a halin yanzu, don magance ’yan bindiga a tashin farko don kawar da su gaba daya ba?
Ya kamata ka fahimci irin fadin kasar da muke tunkara. Arewa fa ta fi wasu kasashen girma. Mutane nawa kake zaton za a tanada da za su iya kasancewa a ko’ina? Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Ke nan dai ba ku da isassun ma’aikata?
Kwarai da gaske ba mu da wannan adadin na ma’aikata. Sai dai yanzu dole mu yi amfani da fasahar zamani wadda ba ma samar da ita a nan sai dai mu saya kuma yanzu kasar na fama da matsalar kudi.
Ba sojoji ne kawai ke bukatar kudi ba ka ga dole mu yi amfani da iya abin da muka samu.
Mutane da dama na ganin idan an magance matsalar tsaro a kasar nan kusan komai zai daidaita. Idan ko aka kasa aiwatar da haka to ba za a iya magance tattalin arzikin manoma da makiyaya ba domin manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Ko ka yarda da hakan?
Eh, na yarda da kai a kan haka. Amma abin da muke yi shi ne, muna samar da gurbataccen mai a Kudu maso
Kudu, amma kuma adadin abin da ake samarwa ya yi kasa sosai. Rashin samar da adadi mai yawa kuma ya shafi tattalin arzikinmu ba mu da isassun kudade.
Amma dai muna kokarin samar da abin da ya fi hakan kusan za ka ganmu a dukkanin shiyyoyi shida na kasar nan wanda bai kamata ya kasance haka ba.
An ce an karkasa ku kusan dukkanin jihohi 36 na kasar nan ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda nan ma ya dau zafi a ‘yan makonnin baya. Kusan kuna ko’ina ke nan. Ta yaya kuke tafiyar da wannan raba jami’an?
Abin da gaba daya muke yi shi ne magance wannan matsalar. Muna da sojoji na kasa da na ruwa da na sama da sauran hukumomin tsaro.
’Yan sanda sun fi yawan adadi da kuma warwatsuwa a cikin kasa. Hakazalika muna aiki da Jami’an Tsaro na Sibil Difens don kara yawan da za mu rika tunkarar matsalar don magance ta.
Amma fa gaskiya riga-kafi ya fi magani. Don haka dole mu duba wasu hanyoyi don hana ci gaba da faruwar wadannan abubuwa.
’Yan bindiga na haifar da barazana a cikin kasa tare da nuna mana ‘yatsa. Ba wani shiri daga cibiyar tsaro ta kasa da za ta tunkari abin ya wuce a lokaci guda ba? Babu wani kayyadajjen lokaci ne da aka dauka don ganin an murkushe abin kwata-kwata?
Muna kan daukar sababbin ma’aikata. Yawancin wadanda suka yi ritaya sun riga sun gaji don haka ba za mu so mu sake dawo da su cikin wannan aiki ba. Sun hidimta wa kasa don haka a bar su su je su huta.
Matsalar fa gaba dayanta ta ta’allaka ne a kan shugabanci na gari da adalci cikin duk abin da za mu yi. Idna har mun tsayu a kan hakan, ina mai tabbatar maka komai a kasar nan zai dawo daidai.
Yanzu kamar ka samu wani mayunwaci ne ka rika ce masa ya zauna lafiya ban da tashin hankali, amma kuma ka san cewa mayunwaci fa mafadaci ne. Ga shi ba makarantu ba hanyoyi ba wannan ba wancan, da haka al’amura suka fara lalacewa.
Ya kamata mu tsayar da wannan lamarin tun kafin ya girma kada mu yi fargar daji.
Rundunonin soji na iya bakin kokarinsu akan abubuwa da dama. Ba fa duk wani sumame da muka yi ba ne ake yadawa a kafafen yada labarai ba. Duk hukumomin tsaro ina mai tabbatar maka ba sa yin barci.
Su ma da yawan ’yan Nijeriya ba barci suke ba. Suna ganin yadda abubuwa suke dada tabarbarewa, kalli alal misali abin da yake faruwa a Abuja, yanzu mene ne mafita a kai?
Abin ya faro ne da aikin bata-gari ya koma zuwa harkar ‘yan bindiga ya dawo na masu garkuwa da mutane daga baya ya koma na ‘yan ta’adda.
Kuma dama haka abin yake zama matukar akwai rashin aikin yi a cikin al’umma. Muna da labarin ma wanda ya yi garkuwa da kansa. Al’umma ma na da tata matsalar.
Ke nan al’umma ta yi lalacewar da ba za ku iya gyarata ba?
Wannan shi ne abin damuwar. Za ka ga hatta a cikin gida dan uwa na garkuwa da kanensa ko kanwarsa sannan ya fada wa iyayensa su biya kudin fansa. Wannan abin ya kazanta a ce komai ya zama abin neman kudi a kai.
Kowa tunaninsa shi ne idan ya samu kudi shi ke nan ya huta. Wadannan su ne abubuwan da ya kamata mu magance su. Amma harkar ’yan bindiga aiki ne na bata-gari wanda ya bambanta da na ‘yan Boko Haram?
Su masu laifi ai suna aiki da juna tare ne. Don haka dole jama’a su ma su hada hannu da karfe don yakar bata-gari. Kuskuren da muke yi shi ne muna kallon ai sojoji ne kawai ya kamata su yi alhali ba haka abin yake ba.
Su waye ke daukar nauyin wadannan mutanen? Mutane na da alaka da su domin akwai masu ba su rahoton sirri a cikin jama’a. Wannan ita ce sana’arsu kuma suna samun kudi sosai a cikinta.
Wasu da dama na son su ba ku hadin kai amma gudun abin da ka iya biyo baya da rashin tabbas yakan hana su.Ta yaya za ku karfafa wa irin su gwiwa?
Magana ta gaskiya mutane da dama kan iso gare mu ta hanyoyi daban-daban kuma hakan na taimakawa matuka. Amma dai har yanzu akwai masu cin abinci da harkar ‘yan bindigar nan a cikin jama’a.
Akwai likitocin da ke shiga can cikin daji suna kula da lafiyarsu. Muna da wasu matan da ke kai wa ‘yan bindiga mata suna amfani da su don su samu kudi a nan Arewa.
Na ga bidiyoyin wasu ’yan bindiga tare da wasu mawaka suna shiga daji da sauransu, wanda hakan ke nuna cewa akwai wasu da ke rayuwa a wurin. Me kake tunanin ya sa abin har ya kai ga hakan?
Mutum ne zai je ya yi wa wasu kida da waka su ba shi Naira dubu biyar, amma idan ya je ya yi wa wadannan mutanen sai su ba shi Naira dubu dari zuwa dubu dari biyu kuma ya kan manta cewa wannan kudin fa na haram ne.
Ba kawai sojoji nake magana ba a nan, hatta hukumomin da abin ya shafa, mene ne tsarinku na ganawa da su?
Mun riga mun tattauna wannan batun ai. Batun tsarin tattaunawar na da muhimmanci. Ina tunanin Ministan Yada Labarai ta hannun Hukumar Wayar da Kan Jama’a suna tsara yadda za a tunkari lamarin.
Mutane sun damu ne saboda lokacin da irin hakan ya faru a Nasarawa da adadin da bai kai wannan ba kamar babu wani bincike da aka gudanar kuma alal akalla ma mutane ba su ji sakamakon da kuka fitar ba.
Kana nufin wannan zai zama daban da wancan ke nan?
Mun fuskanci yanayin da muka tunkari wani kauye ba mu san cewa suna da makaman da suka tona ramuka suka binne ba sai dai ka ga suna ta hakowa suna kawo farmaki.
Akwai matsala wajen fitar da komai a fili ke nan? Eh, akwai.
Akwai kuma zargin cewa wasu jami’an sojin ma sun koma kasuwanci ne a wuraren don an ce wasu daga cikin busassun kifin da muke gani nasu ne. Su waye a wajen ne?
Gaskiya ban san masu fadin haka ba don babu kowa a saman kogunan da ake aikin tattara kifin.
Ko kun kyautata tsarin daukar sojoji ta hanyar lura da wanne irin mutum kuka dauka aiki?
Eh, ai ba ma gaggawa wajen daukar jami’anmu.
Amma a wasu lokuta a kan samu bata-gari a cikin bangarorin ma’aikatan tsaro. Ta yaya kuka tsara dakatar da samun hakan?
Kamar yadda na fada maka ne, ba mu san me mutum ya kulla a zuciyarsa ba, ka ga ba za mu iya sanin waye ba waye ba.
Zan iya haduwa da wani a tashin farko in dauke shi a mutumin kirki kuma za ka iya yarda da shi, amma daga baya cikin sauki sai ya canza zuwa wani abu daban.
Wa ya taba tunanin Shekau zai rika aikata abubuwan da yake aikatawa? Ya fara ne fa a matsayin dan tireda, amma daga baya ya zama mashayin jini.
Wannan ne ya sa muke son mutane su rika sa ido sosai. Idan ka ga wani yana aikata irin haka to kada a yi shiru.
Wanne sabon abu kuke yi don magance matsalar satar mai?
Muna kokarin samar da tsarin gama-gari da za mu sanya a gaba ne. Muna lura da wuraren da za mu sa ido ta yadda ko ka sace ma babu inda za ka iya kaiwa.
Kuma akwai manyan mutane masu hannu dumudumu a ciki?
Da yawa ma kuwa. Mun sha kama jiragen ruwa (da man sata) amma bayan kwana biyu za ka sake ganin jirgin dai da muka kama yana dawowa.
Amma dai na ji dadin irin matakan da ake dauka yanzu. Hakan ne ya sa za ka ga mu muna bin wasu hanyoyi idan mun kama jirgin ruwa sai mu lalata.
Amma akwai zargezargen sojoji, kama daga na kasa zuwa na ruwa cewa wasu na yin rakiya ga irin wadannan barayin man. Me za ka ce kan wannan zargin?
Ba zan iya ce maka dari bisa dari hakan ba gaskiya ba ne, mu mutane ne kuma mutum tara yake bai cika goma ba, amma dai ba wanda zai shiga hannu bai dandana kudarsa ba.
Ya aka yi game da binciken wani Janar daga Sakkwato da aka same shi da kudade masu dimbin yawa, kananan jami’ai na yi masa sufurinsu su ma suna kokarin karkatar da su. Kafafen yada labarai sum yada labarin.
Wannan tsohuwar magana ce.
Amma ba mu ji yadda aka kaya ba.
An gurfanar da shi kuma an amshe kudaden sannan an sallame shi daga aiki.
Kuma ya tafi a banza ba tare da an tsare shi ko daukar wani mataki ba?
Wannan mataki ne dai na shari’a kuma masu hukuncin suna da irin nasu tsarin. Na san ya bi matakan zuwa kotu ne kuma bai yi nasara ba.
Yaya batun walwala da jin dadin ma’aikatanku sojoji musamman masu zuwa fagen daga? Mun daina ganin bidiyo da audio na wasu sojoji da za ka ji suna korafin kan alawus din da ake biyansu. Ko akwai wani yunkuri na kyautata jin dadin wadanda ke sadaukar da rayuwarsu domin mu?
Yayin da muka fara irin wannan a shekarun baya kudin alawus din da muke kira RCA Naira dari biyu ne.
An kara daga baya zuwa 500 yanzu kuma ya haura 1,200 kuma na tabbatar da ka san me 1,200 za ta iya yi maka wajen siyan abinci a kowace rana.
Yanayin da kasar ke ciki, amma duk da haka dakarunmu sun cancanci yabo. Suna tsayuwa awa 24 don ganin mun yi barci.
Na san akwai kalubale da yawa kuma tattalin arzikin kasar ba ya tafiya daidai, amma duk da haka za mu iya yin abu mai kyau. Sojan da ke tare da ni yana karbar sama da 50,000.
Manyan janarori ne ke nan ke karbar manyan kudade?
Ba wani kudin kirki ba ne.
Kowa ta haka yake bi kuma irin abin da kowa ke fuskanta ke nan. Na fada maka suna ciyar da ni da 1,200 ne a kullum fa.
Wannan idan kana fagen fama ke nan ko? Eh. Ke nan babu wani tazara tsakanin soja da kuma janar?
Babu bambanci a nan ai. Abincinmu na fitowa daga tukunya daya ne.
Kuna tattanawa da ’yan majalisa kuwa tunda su ne masu amincewa don zartar da komai don su fahimci irin halin da ake ciki?
Sosai kuwa. Sanata Ndume da sauran sanatoci da ‘yan majalisar wakilai suna magana a kan kyauta ta jin dadin sojoji.
Ko kuna tunanin kara yawan sojoji?
Muna daukar sojoji ai don na san kowace shekara ana diban sojojin da ba su gaza 12,000 ba.
Amma wannan adadin sun isa?
Ba su isa ba kam don akwai yunkurin kara yawan adadin. Sojojin Ruwa da Sojojin Sama da ‘Yan Sanda kowannensu suna daukar ma’aikata ba maganar gefe daya ba ne kawai. Kuma ka san ba karamin kudi ba ne zai iya rike wannan adadin ba.
Ba ma son gaggawa wajen horar da sojoji domin sojan da bai samu cikakken horo ba hatsari ne shi. Muna son mu tabbatar bayan ka gama samun horon wata shida ka fito za mu sake ba ka wasu wata ukun don mu tabbatar ba da zarar ka fito shi ke nan sai ka je ka fara karkashe farar hula ba.
Ba ku amfani da fasahar kere-kere ne don gano inda ’yan bindiga ke fakewa da za ku dirar musu?
Lokaci ne kawai ina mai tabbatar maka zamu cim musu. Muna kai kwamandojinsu kasa. Suna da matukar wayo ne ba sa kai komarsu a bayyane kamar yadda sauran mutane ke yi, amma muna bibiyar su kuma za mu cim musu.
Idan a ce za a ba ku lokaci zuwa yaushe ne kake ganin komai zai daidaita?
Ni a matsayina na Kwamanda ina ganin tun jiya ya kamata a ce mun gama da muna da duk abin da muke bukata. Mafarki da burina shi ne a wannan shekarar kafin karshenta mu samu zaman lafiya a cikin kasa.
Muna bukatar wasu makamai da kayan aiki. Shugaban kasa kuma ya amince da wasu daga cikin kudaden da za a fitar a kai. Da zarar mun samu za mu fara aiwatarwa.