Aleiro ya kayar da Gwamnan Kebbi a kujerar Sanata
Zaben na daya daga cikin mafiya zafi a Najeriya
Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Adamu Aleiro, na jam’iyyar PDP, ya kayar da Gwamnan Jihar mai ci, Atiku Bagudu na APC a kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya.
Jami’in Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) mai kula da sakamakon zaben, Farfesa Abass Yusuf Sa’id ne ya bayyana hakan da safiyar Talata.
- Atiku ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Shin ’Yan Najeriya Sun Gamsu Da Yadda Sakamakon Zabe Ke Fitowa?
Ya ce Aleiro ya sami kuri’a 126,588 inda shi kuma Bagudu ya samu kuri’a 92,389.
An gudanar da zaben ne a Kananan Hukumomi takwas na Gwandu, Bunza, Aliero, Maiyama, Koko-Besse, Jega, Kalgo da kuma Birnin Kebbi.
Dana ana ganin zaben a daya daga cikin wanda ya fi zafi a Najeriya.