Alfanun Ilimantar da manoma

Noma sana’a ce wadda ta yi daidai da kowa, wato mai dukiya ko talaka, kowa yana iya daukarta a matsayin sana’a gwargwadon karfin jarin  da mutumzai iya zubawa, matsawar dai an yi da basira tabbas za a iya taimaka wa kai da al’umma wajen habaka tattalin arziki. Sannan,  wannan tsohuwar sana’a na matukar taimakawa wajen […]

Alfanun Ilimantar da manoma

Noma sana’a ce wadda ta yi daidai da kowa, wato mai dukiya ko talaka, kowa yana iya daukarta a matsayin sana’a gwargwadon karfin jarin  da mutumzai iya zubawa, matsawar dai an yi da basira tabbas za a iya taimaka wa kai da al’umma wajen habaka tattalin arziki. Sannan,  wannan tsohuwar sana’a na matukar taimakawa wajen samar da ayyukan yi a kasa. 

Don haka  ya kamata duk wani mai sha’awar sana’ar noma ya yi kokarin samun ilimin sana’ar daidai gwargwado, musamman ta hanyar karatun littattafai da mujallu da suke bayar da shawarwari akan sana’ar ko kuma sauran shirye -shiryen da ake gabatarwa a rediyo da talabijin in ma aka samu hali har ma taron kara wa juna sani; ana iya halarta tarukan hukumomi da kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda gangamin zai yi tasirin wayar ma manoma kai tsaye.

Matsawar manoma za su ci gaba da noma ba tare da illimi ba tabbas za a ci gaba da ganin asara ya kamata kowa ne manomi ya dan san wani abu game da sana’arsa. Misali yana da kyau musan abin da malaman gona suke kira “Side selection,” wato yadda ake zabar wurin shuka, ba wai kowane wuri ne ake shuka duk abin da aka ga dama ba. Kowane wuri a filin kasar noma yana da abin da ya dace da shi a nau’ukan tsirrai da hatsi. Baya ga haka yana da kyau mu gane abinda ake ce ma “ Field measurement,” wato yadda ake auna fadi ko girman kasar gona kafin shuka. Saboda hakan zai taimaka wa manomi fahimtar yawan kudin da zai kashe da kuma hasashen abin da zai samu, sannan abu ne mai matukar amfani manomi ya san “ bariety and seed selection,” wato ya san irin da zai shuka ya kuma zaba, misali yasan cewa, wannan irin mai yi ne da wuri ko kuma mai manyan kwaya ne ko mai bukatar taki ne da yawa dadai sauransu. Sai sanin abin da ake kirada “ Planting datse, time and methods,” wato ma’ana sanin hakikanin rana da wata da kuma lokacin da mutum ya kamata ya yi shuka.

Kuma yana da matukar alfanu sanin abin da ake ce ma “Soil management,” sanin hakikanin yadda ake tattalin kasa don gudun ka da ta rasa wani sinadari, wanda take bukata, da yake taimaka wa amfanin gona wajen habaka da samun yabanya mai yawa. Ga dabarun kariya ga shukar da ta tsiro, wato a Ingilishi, shi ake kira da “Safety use and handling of pesticides,”  wato ma’ana a nan ana bukatar manomi ya san yadda ake amfani da magungunan kashe kwari yasan kuma irin maganin da ya dace ya yi amfani da shi.

Bayan wannan akwai abin da masana ke kira a Ingilishi da “Crop maturity, harbesting and storageg” wato ma’ana a nan ana maganar yadda yabanya ke kai matukar gayar girma, tare da kuma yadda za a girbeta. Sannan asan yadda ake bin matakai wajen adanata. Duka wadannan ayyuka na ilimi ne da ya kamata manomi ya samu don taimaka wakansa wajen samun dimbin alfanu, kan abin da ya shafi bunkasa noma.

Yana da kyau manomi ya rinka neman shawarwari wajen malaman gona don saboda dole wasu abubuwan su rinkka shigewa cikin duhu. Misali malaman gona sun san abin da a Ingilishi ake kira da “ Diagnosing and Managing Crop problems, “ wato ma’ana yadda ake gano matsalolin tsirrai kafin a magancesu. Akwai abin da masana ke kira da “ Nutrional Deficiencies and Tadicities “ wato karancin sinadaran da ke taimaka wa yabanya tarika habaka. Kuma in suka yi yawa sukan iya zama guba. A nan za mu iya fahimtar cewa ko taki in ya yi wa amfanin gona yawa yana iya zama guba maimakon ya habaka shukar. A nan ya kamata manoma su rinka tuntubar malaman gona don fahimtar hakikanin yawan sinadaran da za su yi amfani da su.

A wannan gabar zan jawo hankalin masu ruwa da tsaki a hukumance cewa, ya kamata a kara mayar da hankali sosai don ganin an habaka harkar noma a kasar nan, matukar da gaske ake yi, ana da niyar farfado da tattalin arzikin kasar nan. 

Irin shirye -shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na taimaka wa manoma da rancen kudi ba tare da an sanya ruwa ba, wannan abu ne mai kyau. Da dimbin amfani. Tabbas idan aka kara kaimin ilimantar da manoma, tare da basu dukkan taimakon daya kamata, za a samubunkasar harkokin noma da karuwar tattalin arziki. Sai dai ba nan gizo ke sakar ba, shirin cike yake da magudi da dawara da rudu da kuma bata lokaci.

Saboda haka ya kamata mu fahimci hanyoyin da wasu kasashe suka bi, suka habaka harkar noma, mu kuma fahimci irin bayan da muke ci ta wannan fanni. Domin a kasar nan fa sai kwararren manomi ne ke iya noma buhu 40 a kadada 1, kuma a duk cikin mutum 100 mutum 1 ne kawai a lokacin da a kasar China da  Indiya da Amurka suke noma buhu 150 a kowace kadada 1.

Kamal Abdulrahman Dodo

ya rubutomakalarsa daga Malumfashi, aJihar Katsina. Dodo Kamal <[email protected]>