Algeria ta yi tayin samar da gwamnatin rikon kwarya ta watanni 6 a Nijar

Kasar Algeria ta kaddamar da shirin sasanta rikicin siyasar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, inda take bukatar samar da gwamnatin rikon kwarya na watanni 6 a karkashin shugaban farar hulan da zai shirya zabe. 

Algeria ta yi tayin samar da gwamnatin rikon kwarya ta watanni 6 a Nijar

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune kenan.
Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune kenan. © reuters

Kasar Algeria ta kaddamar da shirin sasanta rikicin siyasar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, inda take bukatar samar da gwamnatin rikon kwarya na watanni 6 a karkashin shugaban farar hulan da zai shirya zabe. 

Ministan Harkokin Wajen kasar, Ahmed Attaf ya sanar da haka bayan ya ziyarci wasu kasashen da ke yammacin Afirka domin samo maslahar rikicin da kuma kauce wa amfani da karfin sojin da ECOWAS ke shirin yi.

Kasar Algeria ta dade tana adawa da barazanar amfani da karfin soji, inda take nuni da irin matsalar da aka shiga a Libya sakamakon hallaka shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011.

Daga cikin shirin na Algeria har da shirya taron Majalisar Dinkin Duniya a kan lamarin da zummar mayar da doka da oda a Nijar da kuma bayar da kariya ga bangarorin da ke rikici a kasar, tare da wani shiri na cigaban yankin Sahel.

A makon jiya, tashar talabijin ta kasar Algeria ta sanar da cewar shugaba Abdelmajid Tebboune ya ki amincewa da bukatar Faransa na amfani da karfin soji a Nijar, yayin da Faransa ta musanta gabatar da wata bukata mai kama da haka.

A baya, shugaban sojin Nijar Janar Abderahmane Tchiane ya ce, suna bukatar akalla shekaru 3 domin mayar da mulki ga fararen hula, amma kungiyar ECOWAS ta sa kafa ta shure.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya sani ko wannan yunkuri na Algeria zai samu karbuwa a tsakanin sojojin Nijar da kuma kungiyar ECOWAS.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa