Alhaji Adamu Falke ya kwanta dama
Allah ya yi wa Alhaji Adamu Falke, wanda aka fi sani da Alhaji Ada Falke rasuwa yana da shekaru 58 a duniya. Marigayi Alhaji Adamu ya rasu ranar Alhamis da ta gabata a Jihar Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.Alhaji Adamu kani ne ga dillalin jaridar Aminiya a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da […]
Allah ya yi wa Alhaji Adamu Falke, wanda aka fi sani da Alhaji Ada Falke rasuwa yana da shekaru 58 a duniya.
Marigayi Alhaji Adamu ya rasu ranar Alhamis da ta gabata a Jihar Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.
Alhaji Adamu kani ne ga dillalin jaridar Aminiya a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke yankin Ikeja a Jihar Legas, Alhaji dallami Ibrahim.
Ya mutu ya bar matarsa ta aure da ’ya’ya bakwai, wadanda suka hada da Alhasan da Muhammdu da Aminu-Alajeje da Zahara’u da Maryam da Humaira da kuma Bilkisu.
Alhaji Adamu ya bar aikin gwamnati a mukamin darakta a ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano.
kanensa Alhaji danlami, dillalin jaridar Aminiya a Jihar Legas ya bayyana shi a matsayin mutum mai hakuri.
Tuni aka yi jana’izarsa a safiyar ranar Juma’ar da ta gabata.
Manyan malamai da ’yan kasuwa da kuma ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano ne suka halarci jana’arsa.