Alhaji Ado Bayero: Shekarar ta 1933 zuwa 2014

Inna lilLa wa inna ilaiHi raju`un “Daga Allah muke gare shi kuma za mu koma” Allah Ya yi gaskiya, a ranar Juma`ar da ta gabata ce, wato 06-06-14, mai girma Walin Kano, Alhaji Mahe Bashir Wali, ya bayyana wa mutanen Jihar Kano da ma na kasa da duniya baki daya, cewa Allah SWT, a safiyar […]

Alhaji Ado Bayero: Shekarar ta 1933 zuwa 2014
Alhaji Ado Bayero: Shekarar ta 1933 zuwa 2014

Inna lilLa wa inna ilaiHi raju`un “Daga Allah muke gare shi kuma za mu koma” Allah Ya yi gaskiya, a ranar Juma`ar da ta gabata ce, wato 06-06-14, mai girma Walin Kano, Alhaji Mahe Bashir Wali, ya bayyana wa mutanen Jihar Kano da ma na kasa da duniya baki daya, cewa Allah SWT, a safiyar wannan ranar, Ya karbi ran Mai martaba Sarki Alhaji Ado Bayero, Sarkin Kano na 13, a cikin mulikn Daular Fulani a mulkin Kano, bayan ya share kusan shekaru 51, yana kan karagar mulki. Tarihin Daular Sarakunan Fulani ya tabbatar da cewa margayi Sarki Ado shi ya fi kowane Sarki dadewa akan karagar mulki tun daga lokacin Sarkin Kano Ibrahim Dabo.
Tsawon kwana da Allah SWT Ya yi wa marigayi Sarki Ado Bayero, ya sanya ya zama Sarki da ya ga juyin zamani iri-iri,wanda ya fara da marigayi Firimiyan Lardin Arewa na farko, kuma na karshe, Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, wanda shi ya nada shi bayan mutuwar Sarki Inuwa, wanda ya yi watanni shidda kacal akan karagar mulkin Kano. Alhaji Ado Bayero, kamar yadda na fadi, ya fara da mulkin jamhuriyar farko, ya ga juyin mulkin soja na farko na ranar 15 ga watan Janairun 1966. A takaice dai ya yi zamani da gwamnonin mulkin soja da na farar hula har guda 15, da shugabannin kasa na farar hula da na soja har 13.
Idan mai karatu zai koma a akan tarihin mulkin kasar nan,Sarki Ado ya fara mulki a lokacin da kusan dukkan harkokin gudanar da mulkin jama`a kacokan yake hannun Sarakunan gargajiya, kamar tafiyar da shari`a da gidajen Kurkuku da Baital-mali da sauransu. Shigowar mulkin soja a shekarar 1966, ya sanya sannu a hankali aka yi ta samar da canje-canje da suka rika raba Sarakuna da gudanar da mulkin jama`a kai tsaye, tare da kara kirkiro jihohi da Majalisun kananan Hukumomi, da makamantan sauye-sauye, duk da sunan kusantar da gwamnati ga jama`a.
Bisa ga al`ada, dan Adam bai cika karbar canji ba cikin ruwan sanya ba, ballantana abinda ya shafi tafiyar da mulkin gargajiya, don haka Sarakuna da dama sun shiga cikin wani mawuyacin halin yadda za su iya daidaita tsohuwar tafiyarsu da sabuwar da suka samu kansu, musamman a zamanin janhuriya ta biyu,wanda gwamanatin Janar Murtala da Janar Obasanjo ta mika mulki hannun farar hula a shekarar 1979, bayan sojoji sun share shekaru 13, suna gudanar da mulki ba kakkautawa tsakanin shekarun 1966 zuwa 1979.
Irin wannan sabuwar tafiya ta mulkin farar hula da Sarakunan gargajiya (don sojoji ba su rika wasan kura da Sarakunan gargajiya ba, kamar yadda farar hula suka rinka yi), ta sanya a cikin watan Yulin 1981, gwamatin farar hula ta marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ta aika da takardar tuhuma ga Mai martaba Sarki Ado, bisa ga zargin ya je birnin Zariya da ke cikin Jihar Kaduna, ba da izinin gwamna ba, sannan kuma ya dakatar da shi daga shugabantar Majalisar Sarakunan jihar ta wancan lokacin, har tsawon watanni 6. Wannan tuhuma da dakatarwa ta haddasa wata mummunar zanga-zanga, wadda a cikinta aka kashe Dokta Bala Muhammed, mashawarci na musamman akan harkokin siyasa ga Gwamna Rimi, baya ga kone-konen kayayyaki da gine-ginen Gwamnatin Jihar Kano a lokacin.
Wani babban kalubale da marigayi Sarkin Ado ya fuskanta a zamaninsa, shi ne na wata dakatarwa da kwace takardunsa na fita kasashen waje da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari ta yi musu, shi da babban amininsa Oni na Ife,  Oba Okunade Sujuwade a shekarar 1984, bayan sun kai ziyara kasar Isra`ila a daidai lokacin da kasar nan da wasu kasashen Afirka suka yanke huldar jakadanci da kasar ta Isra`ila akan mamaye wani yanki na kasar Masar. Ya kuma fuskanci kalubale irin na zamantakewa da `ya`ya ko muce Iyali, da na wasu daga cikin talakawa da kuma  kungiyoyin addinai, musamman kungiyar Izalatul Bid`ah Wa`ikamatus Sunnah, akan ginawa da bude Masallatai da yin wa`azuzzuka. Wani abin jin dadi a wannan sabani tsakanin marigayi Sarki Ado da kungiyar ta Izalah an samu fahimtar juna da dadewa.
Duk da wadancan kalubalen rayuwa da marigayi Sarki ya fuskata cikin karagar mulkin shekaru sama da 50, Allah Ya yi masa wata baiwa mai yawa, da bai yi wa akasarin masu mukami da daukakar duniya irin tasa ba.
Wadannan dimbin baiwa, sun hada da irin yadda ya kasance shi ba azzalumi ba ne tsakaninsa da talakawansa, tsofaffin `yan jam`iyyar NEPU SAWABA da suka yi zamani da shi yana Wakilin Doka a En`en Kano, suke bada shaidar haka bisa ga irin adalcin da ya rinka yi masu a duk lokacin da aka gurfanar da su gabansa da sunan sun yi wani laifina siyasa. Marigayi San Kano ya yi suna akan shi ba makwadaici ba ne, ta yadda ba ya tambayar kowa abin hannunsa, amma in ka kawo ka ba shi wani abu kome kankantarsa zai amsa ya ce ya gobe. Tsofaffin shugabannin kasar nan biyu Cif Obasanjo da Janar Babangida sun sha tabbatar da haka, kazalika ya yi suna wajen cika lokaci a duk inda aka gayyaceshi, ko ya sa ma lokacin ku hadu.
Marigayi Ado Byero, ya yi kokarin ganin ya kulla zumunta tsakanin wasu daga cikin manya-manyan mutane na kudancin kasar nan, wadanda ba musulmi ba ne. Daga cikin irin wadannan manyan mutane akwai Oni na Ife da tsohon madugun `yan tawayen kasar nan Cif Odumegu Ojukwu, wanda har jana`izarsa Sarkin ya halarta a Jihar Anambra, a shekarun baya, akwai kuma babban Lauyan nan Cif Micheal Agbamuche, duk da aniyar ganin ana samun hadin kai da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai da kuma manya da kananan kabilun kasar nan. Bayan ga za ka iya alakanta kusan dukkan ci gaba da bunkasar da Kano da mutanenta suka samu a yau, akasari sun samu a zamanin mulkinsa.
Allah Ya karbi ran Sarki Ado yana dan shekaru 84, a duniya, ya mutu ya bar matan aure da `ya`ya 62, 30, maza, 32, mata, daga cikin mazan akwai 8, da suke Hakimai. Allah Ya gafarta wa Sarki Ado Ya sa ya huta, Ya yafe masa duhu da azabar kabari, Ya kuma duba bayansa. Shi kuma Alhaji Sanusi Lamido, tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar nan da ya zama sabon Sarkin Kano na 14, wanda yake jika ga Sarkin Kano na 10, Alhaji Muhammadu Sanusi Allah Ya kama maka, sai mako na gaba zai yi tsokaci akan nadinsa in Allah Ya amince.