Alhaji Ibrahim Mamuda ya rasu yana da shekaru 85

Allah ya yi wa Alhaji Ibrahim Mamuda rasuwa yana da shekaru 85 a duniya.Marigayi Alhaji Ibrahim Mamuda ya rasu a ranar Lahadi 26 da watan 10 a shekarar 2014, inda aka yi jana’izarsa a unguwar Agege da ke jihar Legas.Ya rasu bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya kwanaki kadan bayan ya kai ziyara mahaifarsa da […]

Alhaji Ibrahim Mamuda ya rasu yana da shekaru 85
Alhaji Ibrahim Mamuda ya rasu yana da shekaru 85

Allah ya yi wa Alhaji Ibrahim Mamuda rasuwa yana da shekaru 85 a duniya.
Marigayi Alhaji Ibrahim Mamuda ya rasu a ranar Lahadi 26 da watan 10 a shekarar 2014, inda aka yi jana’izarsa a unguwar Agege da ke jihar Legas.
Ya rasu bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya kwanaki kadan bayan ya kai ziyara mahaifarsa da ke Jihar Nasarawa.
Allah ya albarkace shi da ’ya’ya 19 wadanda suka hada da maza 12  da mata 9 da kuma jikoki 43.
Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai babban dansa Auwalu wanda ya bayyana mahaifinsa da mutum mai hakuri da taimakon jama’a.
Marigayin wanda ya yi fiye da shekaru 50 a Agege ya yi fice a wajen kula da addini da taimakon makarantun Islamiyya.
Wani na kusa da shi mai suna Ladan Galadima, ya ce dubban jama’a ne suka halarci jana’izarsa cikinsu har da Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhamadu Musa Dogon Kadai da malamai da ’yan kasuwa.