Alhaji Idi Mai nama ya rasu

Allah Ya yi wa fitaccen mahaucin nan da ke Legas, Alhaji Uba Idi Mai nama rasuwa yana da shekara 76 a duniya.Alhaji Uba wanda ake kira Oga Idi ko kuma Idi Mai nama ya rasu ne a ranar  Litinin 17 ga Fabrairun da muke ciki bayan gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke Layin Ifeledun […]

Alhaji Idi Mai nama ya rasu

Allah Ya yi wa fitaccen mahaucin nan da ke Legas, Alhaji Uba Idi Mai nama rasuwa yana da shekara 76 a duniya.
Alhaji Uba wanda ake kira Oga Idi ko kuma Idi Mai nama ya rasu ne a ranar  Litinin 17 ga Fabrairun da muke ciki bayan gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke Layin Ifeledun a Unguwar Agege.
Marigayi Oga Idi dan asalin garin Yaba a karamar Hukumar  Malumfashi da ke Jihar Katsina, kuma ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya 11.
Daga cikin ’ya’yansa  akwai Umaru da Shu’aibu da Inuwa da Ibrahim da kuma Habu da ake masa lakabi da Habu Fada.
daya daga cikin jikokinsa ya ce kakansu ya bar jikoki 25 da kuma tattaba kunne hudu.
An yi jana’izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada inda aka binne shi a makabartar da ke layin Markaz a Unguwar Agege.
Alhaji Idi ya shafe kimanin shekara 40 yana sana’ar fawa a Legas tare da taimaka wa jama’a.
Sarakuna da shugabannin kasuwanni da na kungiyoyin mahauta da malamai ne suka halarci jana’izarsa, inda jam’a da dama suka bayyana Oga Idi da attajiri mai taimakon jama’a da koya musu sana’ar fawa, kuma mutum mai son zaman lafiya da duniya ba ta dame shi ba.